KASAR WAJE. 2

2.2K 91 9
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 3/4

Koda Aliy ya iso kasuwa suka had'u da Yusuf yace masa "abokina ka sayar da gidanku mana"!

Zaro idanu Yusuf yayi yace "ay bazai yiwu ba inkai mamana da k'annina ina"?

Aliy yace ka kama musu haya kana zuwa waje shekara zaka tara kud'in da zaka saya musu gida a sharada ma ko rijiyar zaki

Shiru Yusuf yayi yace to kasan wani wanda zaimin hanya?

Eh aliy yace akwai abokin abbamu aikinsa kenan nima abbamu bayaso ne wai sai bayan degree kuma nayi aure tukuna zan fita

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace shikenan ka bari zanyi tunani sai na fad'a maka

Suka yi sallama!..

Yau kwana goma da maganar Yusuf da maganar yake kwana yake tashi inda a k'arshe ya yanke hukuncin bayar da gidansu jingina ya samu kud'in fita k'asar waje

Kuma bazai fad'awa innarsu wannan gangancin ba gara yayi komai a sirri har buk'atarsa ta biya

Da haka ya nemi aliy saidai bai gaya masa ainihin hukuncinsa saida sukaje gurin alhaji shamsu yusuf ya masa bayani inda aliy yasa baki yayita rok'on alhaji ya karb'a jinginar takardun

Alhaji shamsu ya amince aka kira dillalai suka duba information d'in gida darajarsa million 4 inda alhaji ya tanbayi Yusuf k'asar da yake son zuwa

Yusuf yace Toronto Canada yana yawan ganin k'asar a labarai sabida yawan da musulmai suka yi a k'asar

Kallonsa alhaji yayi yace Toronto zaka kashe kusan millions5 komai da komai da visa 2yrs da masauki da d'an kud'in da dole mutum ke shiga k'asar waje dashi

Shiru Yusuf yayi alhaji ya kalleshi yace in haka ne babu damuwa zan maka komai kaidai ka nutsu ka biyani kud'ina in kaje bana fata mu rabu babu dad'i

Yusuf yace IA bazan baka kunya ba

Alhaji yace Allah yasa.

Amin suka ce shi da Aliy

Yusuf ya k'ara godiya nan alhaji yace kaje gobe zamu je mu fara shiri

Toh yace yayi godiya sosai suka yiwa alhaji sallama aliy nata taya Yusuf murna da mamakin irin kwarjinin da Yusuf yayiwa alhaji har ya amince taimakonsa babu sharad'i ko ribau

Koda Yusuf ya isa gida yayiwa innarsa bayani da cewa aiki ya samu daga ogansa zai turashi

Tayi murna sosai tasa masa albarka

Aka gama komai cikin 2wks cikin kud'in Yusuf ya rok'i alhaji 100k yayiwa innarsa cefane buhun shinkafa wake carton taliya couscous macaroni semovita manja man gyada maggi sannan ya bata saura kusan 35k a hannunta

K'anninsa da innarsa sunsha kuka domin tun bayan rasuwar babnsu haka suke ganin yusuf kamar babansu haka Yusuf ya wuce sai Canada!

A Canada Yusuf da k'yar ya samu aiki a wani swimming-pool  da nisa shima duk rashin maganarsa haka ya daure ya rok'i wani mok'ocinsa bak'in fata ya samo masa aikin da visarsa kasancewar alhaji yayi masa komai a matsayin driver wani kanti da alhaji ya sansu a Toronto don shiga k'asar yayi masa sauk'i.

sai train da yake biya da cefane da biyan gaz da electric da ruwa bills dai biyar yake biya banda gida.  
Ana biyansa babu laifi saidai k'alu bale na farko da ya fara ganewa shine kud'in yadda kake samunsu a gurin yawanci haka suke wucewa a gurin sai mutum ya jure sosai kafin ya tara

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now