9-10

1.4K 124 9
                                    


_That exactly what TAWAKKUL means,it means that don't see the solution,i don't know what is gonna happen tomorrow. BUT! I do know one thing for sure and that is_ ان معي رب_ سيهدين (Inna ma'iya rabbi sayad deen) _ndeed my Lord is with me and he will guide me through._
_And when we have that kind of attitude Allah_ _promises US something, that he will split seas for us, And situation that look impossible ALLAH will make a way out...._


*****Shuru Moon tayi tana sauke ajjiyar zcy kamar wacce tayi tsere,can kuma ta kallesa tace "Dad Mummyna" yana jinta yay mata shuru,cikin Muryar kuka ta ƙara cewa "Dad ƙafa na hannu na ciwo duk suke min" still shiru ya ƙara yi mata,a hankali ta ɗura ƙafarta a shoulder ɗinsa idanunta na zubar da hawaye sosai leg ɗinta ke mata zafi da kuma raɗa ɗi,ganin yadda take jiyaway fararan manyan idanunta ka san ce she look so sick,20 minutes left ta fara kuka tana ɗaga ƙafafuwan ta sama gaba ɗaya ta turmushe sa,cikin wani a zababen baccin da yake fizgarsa ya ware idanunsa tare da sauke sa a kan fuskarta wacce ta jiƙe da hawaye,da mmki yake kallonta musamman yadda take juyi a kan bed tamkar macen da take naƙuda ganin da gaske ciwon ne bawai iskanci ba yasa murya can ƙasa yace "keeee" jin muryarsa yasa ta ƙara sanya wani sabon kukan tace "Dad ƙafa ta ciwo" tashi yayi zaune tare dasa hannu a bed side ya kunna hasken ɗakin, ɗan waro idanu yayi waje ganin yadda ta haɗa uwar zufa ga yadda tayi face-face da hawaye a fuskarta duk ta fice a hankalinta,shuru yayi yana tunanin abinda zai mata can maganar Alhaji ta faɗo masa lokacin da yake waya yace "yarinyar ma sickle gareta" tuna wannan maganar yasa ya ɗan saurin juyawa zuwa gare ta yana nazarin abinda ya dace yay mata.

Zameta yayi daga jikinsa ya nufi cikin bathroom wanda yake cikin ƙaramin ɗakin da yake, tsayawa yayi yana kallon bathroom gaba ɗaya kansa ya ɗaure bai san mene zai mata ba wanda zai sanya taji sauƙin ciwon da take ji a yanzu,bai saba ba haka nan bai san ta ina zai fara ba.
Tunanin haɗa ruwan zafi ne yazo masa kai,a zafafe kamar yadda yake tafiya a ko yaushe ya ƙarasa gaban jakuzzie ya faɗa mata warm water,cikin sauri ya juya ya nufi cikin bedroom ba tare da wani abu ba,yana zuwa yasa hannu ya ɗauke cak ya nufi cikin bathroom ɗin da Ita,sam bai damu daya zafin ruwan yake ba,burinsa bai huce yaji ta daina masa ihu a ka ba,yana daka tsayen ya cilla ta cikin ruwan, ƙara ta saki mai ƙarfi gaske ga yanayin buguwar da kanta yayi ga kuma zafin ruwan daya ratsa ta wanda ta keji tamkar naman jikinta zai kwakkwaɓo sabida zafin ruwan.
Da sauri ta yun ƙura zata miƙe ya sanya tafin ƙafarsa ya dannata cikin ruwan,a'a dole ta koma taci gaba da kukan a zama,ganin ta zauna ya juya da sauri yabar cikin bathroom ɗin.
Yana fita ya faɗa saman bed da rufda ciki.

Ajjiyar zcya Moon ta shiga saukewa,a hankali kuma zafin ruwan ya fara ratsa mata cikin jikinta Zuwa ƙashin ta ta naman ɓargwanta,wajan 20minutes jinin jikinta daya daskare sanadiyar zaman parlour'n da tayi sanyi ya gama ratsa ta fara sinkewa.
SICKLE
ciwo ne mai haɗarin gaske,wasu da susan ciwo wasu kuma basu san shi ba,ciwo ne da yake a cikin jinin mutum,ciwon na tashi a sanadiyar wata ƴar ƙaramar ƙwaya daza tazo tsakiyar jijiya ta tsaya,hakan zai sanya jinin mutum ya daskare yaki tafiya ya cure waje guda,jinin nayin hakan ciwo zai tashi,wasu lokacin kuma jinin ke lanƙwashewa yay kamar lauje,idan kace Zaka ɗaga wannan laujen zai iya karewa idan kuma kace Zaka bassa a wajan zai iya sanyawa naman wajan tsatsa har takai ga wajan ya kumbura ya fara ruwa.
To aduk sanda ciwon ya mutsa sai dai a dinga ruwan zafi ana shafa man zafi tare da shan magani irinsu ibuprofen diclofenac sodium da sauransu, wasu lokotan kuma ana injection ne a yayinda maganin yaƙi aiki a jiki.
Ciwon sickle babu inda baya kamawa ƙafa, hannu,baya,ciki,ƙirji,kai, haƙori da sauran,wani lokacin ƙafa ko hannun mutum na iya karyewa haka kurum ba tare da wani ciwo ko rauni ba.
Da yawan lokota ba'a gane ciwon sickle a jikin ƙana nan yara,wasu lokacin sai anyi gwajin jini na genotype a nan za'a fahimci wanne kalan jini gareka AA,AS,O, SS, SS shine cikakken sickle,AS kuma kamar aƙwai amma bamai ƙarfi ba,da blood group a nan kuma shine B+ da sauransu.

MOONWhere stories live. Discover now