13-14

1.4K 150 15
                                    

Deen ya kalli security tare da duƙule hannunsa tamkar wanda zai kai naushi yace "Are you mad? Arrest for what reason?" Ya ƙare maganar yana fesar da wani huci, lokaci kaɗan kaminsa suka sauya,jikinsa ya shiga rawa kana ganinsa zaka san he is not on his mood,musamman yadda farar fuskarsa ta koma jaaa sabida zafin rai, security ne yace "akan wanne dalili na'urar dake kuka a jikinka?hakan ne ya tabbatar min baka da gaskiya" Deen ya ware yatsun hannunsa guda biyu tare da haɗe su waje guda suka bada wani soud mai karfi, Ovasi ne ya kalli security yace "You can check him, if not trust him,ko a garin ku haka ake kama mutum?" Security yace " an sorry,i know i made a mistake,but it's my work komai akan ƙa'ida nake" ya faɗi hakan ya duba jikin Deen wanda yake tsaye tamkar gunki ko mutsawa ba yayi sabida yadda yake jin zcyarsa na ta farfasa,babu abinda ya samu a jikin Deen hakan yasa ya tsaya yana kallonsa cike da mamaki domin tunda ya fara aiki bai taɓa ganin hakan ba koda wasa,babu yadda ya iya dole ya basu hanya suka shige,kai tsaye cikin taxsi suka shiga Deen na bayan mota yana shiga ciki ya hankaɗe Moon daga jikinsa,ovasi da Nana kuma suna cikin wata taxsi ɗin,kai tsaye masu taxsi ɗin suka fice daga cikin harabar airport ɗin,sanyin daya ratsa jikin tane ya sanya ta buɗe kumburarrun idanunta ta shiga murzasu da sauri sabida nauyin da sukai mata,ware idanunta tayi ta kalli Deen daya kifa kansa a tsakanin cinyoyinsa a hankali ta matsa kusa dashi ta miƙa hannu wajan tattoo ɗin dake damtsen hannunsa,saurin janyewa tayi sabida ganin kamar tattoo ɗin yana mutsin,cikin Muryar shagwaɓa tace "Dad yunwa na keji kuma sanyi" ta ƙare maganar tana tura bakinta haɗe da rarraba jajayen idanunta wanda basu gaba dawowa dai-dai ba,a zahiri idan kaga yadda Deen yay zaka ɗauka yana jin maganarta yay mata baza,amma gaskiyar lamari ko taɓa shin da tayi baiji ba,ya lula duniyar tunani sabida next step kawai yake hangowa wacce ƙasar zashi kuma wanda suke da ƙarancin ilimi da kuma kuɗi, ma'ana dai ƙasar da talakawa suka fi yawa, ihun da tayi ne yasa Baturen mai taxsi ɗin yay saurin reverse da motar tare da yin parking gaba ɗaya a tsorace take,duk wannan ihun Deen bai jisa sai Muryar Baturen da yaji yana faɗin "Yallaɓai yarinyarka na kuka,ta kusa sawa na kifar da mota na" Moon ganin Deen ya buɗe idanunsa yasa tayi sauri matsawa kusa dashi tace "Dad kai ni gida, ina son ganin Mummy da Daddy na" banza yayi mata ganin har yanzu mai taxsi ɗin yana tsaye ya sanya ya buɗe murfin taxsi ɗin ya fita da sauri,ba tare daya kula mai taxsi ɗin ya finciki hannun Moon dake cikin motar tayo waje, Baturen mai taxsi ɗin ya leƙo da kansa cikin harshen turanci yace "yallaɓai shiga mota fi" cikin zafin nama da kuma ɓacin rai Deen ya zaro kuɗi irin na ƴan ƙasar ya watsawa mai taxsi ɗin cikin wata murya mai nuni da gargaɗi da kuma zallar ɓacin rai dake ransa yace "Ubanka zan maka a mota? Da daka tsaya nina saka,get lost you mumu" da sauri mai taxsi ya ɗauki kuɗin yabar wajan sabida yanayin Deen ba ƙaramin tsoro ya basa ba, Moon da duk jikinta ke rawa sabida tsoran daya bata daɗin da ɗawa ga yadda ya matse mata hannunta ƙashinta har ƙara yake gata daman mai ƙashin a gwagwa babu ƙwari ya sanya ta fashe da kuka,duk abinda take yana jinta amma ko a jikinsa a haka ya tsaida wata taxsi ɗin..

RENAISSANCE DHAKA GULSHAN HOTEL(The hotel is only 20 minutes away from Hazrat Shahjalal International Airport, with a distinctive local character that dictates the atmosphere)

so ta zararsa da airport ɗin babu wani nisa sosai har cikin mai taxsi ya shigar da Deen wanda har yanzu yake riƙe da hannun Moon wacce lokacin kukanta bai fita sosai sai ajjiyar zcya take saukewa kamar wacce ta shekara tana kuka, kuɗin sa ya bashi tare da fitowa daga cikin taxsi ɗin,ganin securities da yawa a wajan ya sanya ya durƙosa dai-dai tsayinta yace "meye?" Jikinsa ta faɗa da saki kuka,wani abu ya haɗiye a cikin maƙoshinsa yama rasa me zai mata banda haushinta babu abinda ya keji a rasa,sabida ita ɗaya yaje wata ƙasa ya zauna har kusan watanni baƙwai zuwa takwas,tsaki yaja kafin ya sanya hannu ya rungome ta a jikinsa ya shiga shafa kanta yayin hakanne sabida securities ɗin da yaga suna kallonsa,wani daga cikin securities ɗin ne ya ƙarasu wajansa,cikin harshen turanci yace "meke faruwa?"
ba tare da Deen ya kalli security ba yace "she is sick" security yace "meye haɗin ka da ita?"  Wani kallo Deen ya watsawa security domin har zcyarsa ta harziƙo a ransa yace " fuck You! you mumu" a fili kuma ya fesar da wani numfashi ta cikin hancinsa mai zafi kafin ya gyarawa Moon gashin kanta yana kallon cikin idanunta da duk suka sauya kala yace "jini nace ita,i mean she is my daughter" da sauri Moon ta buɗe baki zatai magana yay sauri rufe mata bakin ta hanyar bata wani light kiss kafin ya ɗaga ta cak ya nufi cikin reception da ita.

MOONWhere stories live. Discover now