63-64

1.1K 87 19
                                    

Jan gemunsa Farouk yay yana sakin Murmushi wanda kana ganinsa kasan na mugunta ta ne kana yace "Lokacin hutawarsa ne yanzu, kaje ka huta King Aliyou Eneye Ahuoyza Deen"Wanda ke kusa dashi yace "Oga yanzu yana ina? Babu da sauran time kafin ace ya dawo gareta yana da kyau musameta ko?" Baya Farouk yay idanunsa akan wata budurwa dake rausayawa yace "A.j kasan dole zan san inda Aliyou yake,banyi niyyar kashe fa shiyasa har na bari aka taimakesa,a lokacin da bom ɗin ya tashi ni masa Ovasi ya ɗauke sa sbd duguwar sumar da yay,abinda basu sani ba duk wannan faɗan da ake nima ina cikin ƙasar, bayan Ovasi ya ɗauke sa ne ya kaisa can bakin ruwa inda manyan masu kuɗi suke hutawa,amma inda ba za'a a ganshi ba, bayan ya kaisa ya dawo yake faɗa min ya kaisa to a nan Ovasi ya kamamu nida budurwa sa ganin babu yadda zanyi kawai ɗauke masa numfashi da bindigar dake jikin, to kafin na ƙarasa wajan Deen wasu Mutane sun ɗauke sa a mota,nabi diddigi kuma na gane inda suke" murmushi A.j yay yace "gsky Oga kana da brain ba duk kai ba serious" murmushi Farouk yay yana jin daɗin ƙudirinsa na shekara da shekaru na gaf da cikawa, gyara zama yay yace "bari na baka labarin waye Farouk Bashir Yahya gidan iko..

#flash back.
Sunana Farouk Bashir Yahya gidan iko, nine frist Born wajan iyaye na sai ƙanwata Yasmin,daga nan iyayenmu basu ƙara samun wani ɗa/ƴar ba,ina da Shekara goma a duniya a primary school muna zaune bayan an fita breakfast, wani abokina mai suna Khamis ya bani sweet, girgiza masa kai nayi nace "No thank you!" Ɓata fuska Khamis yay yace "why" nace "haka nan" kamar zai kuka yace "please kasha ko sau ɗaya ne" ganin yadda ya sauya fuska yasa na amsa na sha,tofa wannan wannan sweet ita ce silar jefani halin da nake ciki a yanzu,ashe mahaifin yaron ɗan mafiya ne shike bashi alawa yana rabawa friends ɗinsa,kwana nayi kai na nayi mani ciwo cikin dare zanji shawo na yawo saman bedroom ɗina yana kiran sunana, na shiga tashin hankali sosai sbd ban saba dajin hakan ba, kwanci tashi naje makaranta Lokacin ina ss3 bayan an tashi wata mota tai parking gaba na, banyi wani musu ba na shiga motar daga nan kuma ban ƙara fahimtar komai ba sai farkawa nayi na ganni a cikin wani babban ɗaki tare da tarin maza da mata sanye da jajayen kayan  ga wasu manyan ƙoƙona a hanunsa ɗauke da jini.
Wani babbansu wanda yake saman kujera yay dry tare da faɗin "wlcm Farouk Bashir Yahya gidan iko" nidai tsaye nai ina kallonsu kafin na kalli aboki na Khamis da sauri ya janye idanunsa,a nan dai suka faɗa min abinda suke so kasa yi masu nai a take a wajan kuma nace na bada cikin dake jikin mahaifiyata.
Tun daga nan komai ya lalace kusan rabin familyn mu na bada jikinsu mugwayen kuɗi nake samu bana wasa ba, kuma kai na ya ƙare wayewa,bayan kamar shekara huɗu haka aka ƙara kiranmu meeting, nan dodo ya bada izinin a samo masa wata yarinya kuma babu wanda aka bawa aikin sai ni, photon yarinyar aka ban tare sunanta a jikin photon aka rubuta MOON da jan jini, aikin da hatsari da kuma sharaɗi dole ni zan kawota idan har ban kawota ba za'a fanshi jinina bisa nata da aka rasa, idan na sameta san zama shugaba gaba ɗaya a nan jahar Kano, a lokacin kusan 100.m aka bani..," murmushi Farouk yay yace "Tayaya kake ganin zanbar wannan dabar da barni,abun mmkin yadda mahaifina bai taɓa tambaya ta komai ba,hakan yasa wata rana da aka kira meeting na gayawa dodo damuwata,dry yay sosai tare da yin wani ihu,cikin ƙaramin lokaci ya buga wani abu sai ga vedio'n Abbana ya bai yana a tsakiyar wasu mata suna ta shafasa,mmki ya cika ni,ban bar wajan ba sai da aka gayamin dukkan abinda Abbana yake,sai naji farin ciki shima yana aikata hakan bare ni,san da su Moon suka tare a gidan dake farcing namu farin ciki ya kamani sai ban nuna sosai ba sbd nasan mahaifina nada buri a kanta, infact bai san nasan na ganta ba,haka akai lokacin da Deen yazo kallo guda nai masa nadan cewa ba asalin aikinsa kenan ba,akwai manufar data kawosa gidanmu,yin duniya Abbana yaƙi korar Deen, Aliyou Eneye Ahuoyza yana da kaifin basira fiye da tunanin mai tunani, duk yadda kakai da gane mutum da wahala ka fahimci inda Deen ya dusa gane asalinsa da abinda yake shirin yi shine Abu mai wahalar gaske tabbas, wannan dalilin yasa na ƙara sanya idanuwa na a kansa, nasan soon or later I know everything about him tabbas,dalinsa na ƙarar da dukkan familyn namu domin duk sanda aka buƙaci Moon nace a ƙara min lokaci to dole sai na bada jinin wani matsayin toshiyar baki".
Jinjina kai A.j yay yace "tabbas abun babba ne basan san lamarin ya kai haka ba wlh"  ka faɗa Farouk ya ɗaga irin whatever ɗin nan... Yakumbo ce ta kalli Sarki Aliyu Al'amin tace "nikam gani nake yarinyar nan kamar bata son haɗin da kakeso kayi na shekara da shekaru" gyara zama Sarki Aliyu Al'amin yay tare da sakin lallausan murmushi kana yaja numfashi yace "Na lura da wannan amma yaya kikeso naiwa Faizak kina sane da irin son da yake mata ai?" Yakumbo tace "Allah ya ƙarawa Sarki lfy, amma ya kamata aji ta bakinta domin ba za'ai mata auren dole ba, ko Fulani?" Girgiza kai Fulani tayi tace "A'a Yakumbo duk abinda kuke dai-dai ne" Murmushin jin daɗi Sarki Aliyu Al'amin yay domin ya yarda da karamcin matar tasa, miƙewa Fulani tayi tace "Na barku lfy" daga nan ta bar turakar Sarki,ganin babu kowa yasa ta nufi ɗakin Moon zaune ta sameta a gefen gado tana taje sumar kanta, Murmushi tai mata tace "wanka kikai?" Kanta a ƙasa tace "Eh" shiru Fulani tayi can kuma tace "kin gama prioud ne?" Kasa bata amsa tayi hakan yasa fulani yin Murmushi tace "look! Am your mother babu buƙatar ki ɓoye min wani abu, idan ban san abinda ke ranki ko yake damunki ba wane ya dace ya sani? So sharing your feelings with me kin gane, kin gama al'ada? Ma'ana farin ruwa ya biyo bayan jinin?" Kai Moon ta ɗaga kamar zatai kuka duk ta marai-raice fuska tace "eh" "ok kwana nawa kikai? Kin iya wankan ai?" Kwaɓe fuska tayi tace "Ammi" haɗe fuska Fulani tayi tace "bana son shashanci Maimunatou" da sauri Moon ta runtsa idanunta sbd sunan Maimunatou da Fulani ta ambata, duk sanda akace Maimunatou sai ta tuna gwarzon jaruminta wanda ya salwarta da rayuwarsa a kan tata, hawaye ne suka fara taruwa a cikin idanunta, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta fara zafi da raɗaɗi haɗi da ƙona, shiru Fulani tayi domin tasan abinda yake damun yarinyar ta ta, numfashi ta sauke tana gyara zaman Alƙyabbar ta tace "Yayinda kike jini ki kiga kumfa wata farin Ruwa ya fito Wannan alama ce take nuna jinin ya tafi saura wankan tsarki, idan kin iya wankan to idan ba kiyi ba yanzu dai zan maki bayani;

MOONWhere stories live. Discover now