45-46

1.2K 109 14
                                    

Jini kawai ke fita ta cikin bakin Yasmin da hancinta,banda ihu babu abinda take yadda yake ihu haka Moon ke ihu,gaba ɗaya sun cika coner ɗin da ihu,Sumy na fita tayi wajan teachers section a hanya ta haɗu da Faizak sai je office ɗin principal sbd kiran da yake mata,tun daga nesa yaga gudun da take hakan yasa ya ja tsaya yana kallonta,kai tsaye itama Sumy wajansa ta nufa tana haki,tana zuwa wajansa ta shiga nuna masa hostel ɗin su Moon, kallonta kawai yake yana kallon derection ɗin da take nuna masa,tsaki yaja kaɗan yace "Keee! Lfy? Mene haka kike nuna min?". Gaba ɗaya a tsorace take da ƙyar ta shiga faɗin "Sir Moon ce,zata kashe Yasmin wlh,har ta fasa mata". Da mamaki yake kallonta yace "Kamar ya ya kenan?". Gaba ɗaya ta fice daga cikin hayyacinta cikin haki ta shiga faɗin "Moon ta danne Yasmin sai duka take gaba ɗaya ta fasa mata jiki". Waro idanunsa waje yay yana mamaki tayaya ƴar Jss zata daki ƴar ss? wacce take final year ɗinta da sun gana exam zasu bar magana,kai ina hakan ba zai taɓa yiyowa ba, kallonta yay yace "muje". Da sauri tayi gaba yabi bayanta cike da nutsuwa yake taka ƙafafuwan sa a ƙasa,tun a bikin coner yake jiyo ihunsu ga ɗalibai duk sun cika wajan, gyaran murya yay hakan yasa suka fara matsawa suna basa waje,a haka harya isa gareta tana jin alamun yasa ta miƙe da sauri haɗe da gudu, Amira ce tayi saurin cewa "Sir bata hayyacinta fa,mutananta suka tashi kada tai wani wajan". Bai tsaya bi takan maganar Amira ko ya tsaya taimakon Yasmin ya marawa Moon da sauri harda gudu ya haɗa,yana fita ya hango ta  su principal sun riƙeta shi da wasu teachers guda biyu sai kokawa suke da ita,yana zuwa ya kalleta sai kuma ya daka mata wata gigitacciyyar tsawa da sauri ta saki su principal ta faɗi a wajan bakinta na fitar da kumfa,gaba ɗaya tsayawa sukai suna kallonta da ƙyar principal yace "what's going on Coupe Faizak?". Sauke numfashi Faizak yay kafin yace "What am going to say? Kawai ance ta daki wata harda fasa mata baki". jinjina kai Principal ɗin yay yace "i understand" can kuma ga numfasa yace "ka ɗauke ta" Waro idanuna Faizak yay dan babu abinda yake tsoro irin yaga mutum ya data ALJANU, girgiza kai yay yace "bana iya wa". Principal yace "a Kira Amira" babu jimawa aka kira Amira kafin ta ƙarasa wajan Moon,Moon ta miƙe tsaye tana goge bakinta idanunta yay jajir jikinta duk ya saki, sai zare idanu take, kallonta Principal yay yace "Maimunatou mene ya haɗaki da senior ɗinki?".  Shiru tayi masa sai turo baki gaba take tana kumbura fuska da alama dai gama hucewa ba,kallon Amira yay yace "kuje da ita". Moon na jin hakan tai gama abinta ga tare da ta tsaya Amira ba,da idanu Faizak ya bita shi dai ta tsaya masa a rai komanta irin na Mai martaba, idanunsa yaji ya kawo ruwa da sauri ya ɗauke kansa tare da nufar office ɗinsa,sam koda wasa baya son tuna abinda ya huce,yana jin zafi da kuma raɗaɗi a ransa,yana zuwa ya kwanta saman sofa tare rufe idanunsa yana shafa gemunsa,wayarsa ce ta fara ruri wani kiɗan algaita ya fara tashi ga wata sarewa da musamman a cikin giɗan, answering call ɗin yay cikin ƙasa da murya yace "ALLAH! Ya tai maki Mai martaba" Murmushin jin daɗi Mai martaba yay yana ƙara kwanciya a jikin wasu manyan cosion masu kyau,kana ganinsa kaga na gartaccen mutum,zallar kyau da haiba komansa a nutse yake,cikin muryarsa irin ta masu sauran yace "how're you son?". Faizak yace "ALLAHAMDULILLAH!" Jinjina kai yay kamar bazai magana ba sai kuma yace "fatan ka cire damuwar?". Kamar Faizak zai kuka yace "Eh" Mai martaba ya sauke numfashi yace "Bravo! Ka kula sosai" cikin ƙasa da murya Faizak yace "still babu wani impormation ko Mai martaba?". Lumshe idanu Mai martaba yay a hankali kuma yace "just pray,komai zaiyi dai-dai" wasu hawaye ne masu zafi suka sakkowa Faizak yace "In sha Allah". Sai kuma sukai shiru gaba ɗayan su na wani lokaci kafin Faizak yay Murmushi yace "You know what Mai martaba?". Girgiza kai Mai martaba yay tare da lanƙwasa ƙafafuwansa fuskarsa cike da fara'a yace "uhm" Faizak cikin farin ciki yace "Mai martaba yau ALLAH! ya nuna min mai kama dakai,kamar kayi kaki ka tofar,in da kasan kai ka haifeta" Murmushi kawai Mai martaba yay yace "zaka soma ko?baka tunani zai na abubuwan da suka shuɗe to sai an jima,and ka dawo kafin ranar Fulanin duniya (Fulanin worlds day)yazo" yana faɗin haka ya kashe kiran. Deen kwance a makeken royal bed ɗin sa,yana sanya da farar shirt sai faffaɗan ƙirjinsa dake waje wanda ya cika da yalwataccen gashi,yau kwanansa uku kenan da dawowa,amma gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa burinsa bai huce yaga Lollynsa ba,haka kuma baya son takura Besty sbd yay masa halarci,yay masa abinda ya dace a ce duk Uba na gari yaywa ɗan sa, Amma ya ya zai yi da rashinta?? Lumshe idanunsa yay yana fidda numfashi,a hankali kuma yaji ciwon da cikinsa yake masa yana ƙara yawa, mirginawa gefe guda yay tare kifa cikinsa ya rungome pillow, hannunsa yasa ya mararsa dake masa ciwo a hankali kuma ya saki wani sauti mai ɗan ƙara "Auchhhhhi!!! uhmmmm" Yayinda dake bakin ƙofar bedroom ɗinsa ta saki salati tana tafe hannaye tare faɗin "Mahammadur Rasulullah,ashe da gaske ake nima ni Faɗimatu, a'a Wlh babu ruwana ba zaka zame bana masifa a cikin gida ba,azo ana yi damu duk inda muka huce a dinga cuna mana baki ana,gasu can wanda ɗan su ya mutum sbd masifar dake damunsa,Ohh Oohhh! Ai ban yarda zan can Kunyaga Ramla ba sai yau ɗin nan,ai ba gulma gsky zan faɗa maka da kaje ana shunaka gwamma na faɗa maka gsky,uhm rufin asiri dai nada daɗi amma tunda jikana na faɗawa ai na rufa mata asiri, tunda dai har al'ƙawari na ɗauka ai zan tuba ne,Astaga firr firr namijin tuba" da sauri Deen ya juya ya kalleta fuskarsa cike da mmki,yasan cewa ko Besty idan zai shiga flat ɗinsa sai Amintacciyar kuyangarsa tayi masa magana amma gashi da shigo masa,kasa ce mata komai yay sai kansa daya mayar saman pillow tare da lumshe idanunsa kamar mai bacci,Yayinda ta ƙara leko kanta sai kuma ta zauna gefen bed ɗin tare da rafka ta gumi tace "To dai ance idan abu na damunka a rai baka fiddashi ba tsaf za'a wayi gari babu kai, Allah na tuba nikam da ƙuruciya ta da komai ai bazan so na mutum yanzu ba,amma ko ai al'ƙawari na ɗauka gwamma dai nai shiru"shi dai Deen na jinta yay manta banza yaci gaba da pretending kamar bacci yake,da sauri ta girgiza kanta tace "Ina sam sam ba zan iya ba,idan ba faɗa ai sai Allah ya kamani haka nan wutar nan ta duniya me shegen zafi ina ga ta lahira,kana ji na ko? Nidai gsky zan faɗa maka shawara kuma ba basira,ashe da gaske ne duk balagaggen namiji ana jinsa yana ihu shi ɗaya,kamar dai yadda naji kayi yanzu,to nida ba gantalalliya bace nace babu ruwa na da shiga hurumin da banawa ba,nasan ai ba zakai ta ihu kai ɗaya kamar wani zaki ba,to a kan me ma? Su gantallun iyayen naka da suka sallamaka tun kana yaro nike komai naka, nikam tayaya zan bari ka dinga ihu kai ɗaya fisabilillahi?" Miƙewa yay zaune tare ɗura mata rikitattun idanunsa da sauri ta Miƙe tace "kul kul wlh kurwa ta kur,meye wannan kuma?akan wanne dalili zaka kwalalo min ido haka?kai dai jeka can ta masofarka kai ta ihu kai ɗaya kamar doki,Ni kaga tafiya,kuma zan zami uban naka gwamma ka ɗauko ita sallamammiyar yarinya ka zauna da ita,Ni dai da raina da lafiyata ba za'a hanani shiga danki ba,eh to hanawa mana,idan kaja mana abin faɗa ai mun shiga uku gaba ɗaya Masarautar nan sai an sata a bakin Duniya, shiyasa tun wuri na nema mana maganin tsari da kuma ɗan tambura,Ni sai Danoo shawara nake baka wlh wannan ihun bana lfy bane,masifa ce kawai take damunka a rai" shirun da taji yay mata yasa ta juya shi kuma ya gwalo mata jajayen idanunsa waje da sauri tayi waje tana sakin alƙyabbar ta tare da faɗin "A'a wlh kaci kanka nidai nafi ƙarfin ka" bayanta yabi da kallo har ta fici daga cikin bedroom ɗin, miƙewa yay da sauri ya nufi cikin ƙawataccen Bathrobe ɗinsa kai tsaye wajan shower ya nufa tare da sutale shirt ɗin ya saukarwa kansa ruwa, lumshe idanunsa yay ya shiga fesar da ta cikin bakinsa rinannun idanunsa ya ɗago ya sauke cikin makeken mirror'n dake bathroom ɗin, cikin wata dakakkiyar murya yace "Now it's right time to show them my real face am coming to you Oga Taju" yana faɗin hakan yasa hannunsa ya birkita gashin kansa wanda suka cikurkuɗen kamar wanda aka masa saloon tare da Dada, cikin zafin nama kuma yaja bathrobe ya saka a jikinsa,yana zuwa bedroom ya fara shafawa fresh skin ɗinsa wani versiline mai ƙamshi da laushi,after ya gama ga ɗauki body spray ya fesawa murɗaɗɗan jikinsa,wata riga armless mai shegen kyau ya saka kana ya ɗauki wani half ɗin blue jeans ya saka,ya ɗauki p.cap ɗinsa ya saka sosai kyau kamar Balarabe,ida kaga Deen ba zaka taɓa cewa yasan Muslunci ba bare kai tunanin ya iya wani abu daga cikin karatun Alkur'ani,key car ya ɗauka,da gudu kuma ya fice daga flat ɗin yana jin yadda kuyangi suka biyosa yay masu banza domin tuni yay masu nisa,Ba tare daya kalli flat ɗin iyayensa ba ya nufi can harabar Masarauta yana zuwa fadawa suka nufi wajansa wata gigitacciyyar tsawa yay masu da sauri kowa yaja da baya,kai tsaye ya shige motarsa ya nufi wajan saloon da gyaran ƙumba. Deen ke sauraran abinda Besty ke faɗa masa,da sauri ya ɗago kansa bakinsa har wata kumfa yake yace "Mene? Sarauta fa? Ni na taɓa cewa ina so ne?what the fuck??" Tunda ya fara magana Besty ke kallonsa yana Murmushi gaba ɗaya ya rasa kalar Deen ya iya ruwan masifa akan abu kaɗan,mmkinsa yadda baya iya control kansa kwata kwata,har addu'a yake Allah ya kawo wanda zai iya sarrafa Deen,kuma thank God domin da alama zai iya komai akan his wife, gyara zama Besty yay kana ya kalli Nene ya kalli Yayinda ya kalli Chiroma da kuma Tiraki,kana ya kalli Waziri, numfashi ya sauke kafin yay gyaran murya kaɗan da sauri Chiroma yace "Aliyou kayi hattara,zama Sarki a wannan masarautar wajibi ne gareka,domin tun tuni Sarki yay murabus daman kai ake jira". wani kallo Deen ya watsawa Chiroma ba tare da yace komai ba ya miƙe zai bar wajan,kasa daurewa Ohinoyi yay hakan yasa yay gyaran murya yace "You can go every where you like to go,but kasan cewa idan har baka yarda zaka zama Sarkin Nufaz to tabbas Auranka da that girl ɗinsa babu shi" cak Deen ya tsaya ba tare daya juya ba yace "what the you mean by that?". Miƙewa Ohinoyi yay har zuwa inda Deen yake tsaye yay, shoulder ɗinsa ya kama yace "i mean my words Besty,that hausa Fulani girl ɗin can" kallonsa kawai Deen yake with much surprise shi bai taɓa ganin inda aka maƙala wa mutum mulki ba,baya so bashi da interest akai dole ne,fuskar Ohinoyi a haɗe yace "Aliyou Eneye Ahuoyza,bana magana nai karyata billahi indai baka amshi sarautar na ba sai ka saki yarinyar can,na aza zaka min biyayya ko dan farin ciki dana saka na baka abinda yake shirin kai ka lahira,wai ke wacce kalan zuciya gareka heeee??" Ƙasa Deen yay da kansa jikinsa ya ɗauki rawa gashin jikinsa dana kansa duk suka mimmiƙe tsaye, ƙara matsawa kusa dashi Ohinoyi yay can ƙasa yace "BESTY"shiru Deen yay sai fesar da iska da yake,hannu yasa ya rungome sa a jikinsa,kamar zai kuka haka Deen ya kwaɓe fuska yace "i don't like it Besty,ban so" shafa kansa kawai Besty yake yana faɗin "Sorry!! Nasan isn't necessary for you,but haka zaka daure,kai fini lfy ƙarfi zuciya jajirr cewa,so kawai yafi can canta daka zama Sarkin Nufaz"shiru kawai Deen da hannu Ohinoyi yaywa su Chiroma alama da suje kawai,gaba ɗaya suka fice daga haɗaɗɗan parlour'n, ɗago kai Deen yay yace "i need a favour" Ohinoyi yay yace "Uhm" Deen yay shiru kamar bazai magana ba sai kuma yace "ina son zuwa wajanta" murmushi Ohinoyi yay yace "who??" Manyan idanunsa ya juya hankali kwance yace "my wife" Murmushi Nene tayi tana jin daɗin yadda ɗan nata yay accepted zama sarki, ko yaya zai gudanar da Mulkin nasa a wannan baƙar zuciyar tasa ohhhhu!? Besty yace "why not? Idan ma tawowa zakai da ita nan ai fine haka nkeso" bayan ya shirya cikin kayan bacci yana kwance yaji wayarsa tana ringing ƙin ɗagawa yay har sai da akai kiran wajan huɗu ana Uku yay answering call ɗin, ajjiyar zuciya Moon ta sauke yana kallon Principal ɗin cikin ƙasa da murya tace "he picked the call" jinjina mata kai yay,shiru tayi tana sauraran yadda yake fidda numfashi kamar,jin shirun yay yawa yasa yace "uhm" sai kuma ya fara ƙoƙarin kashe kiran, Da sauri Moon tace "Daddy!!!" Ware idanunsa yay yana jin muryarta kamar tana gabansa,a ɗan zafafe yace "MAIMOON ALIYOU" kasa magana tayi sai hawayen da yake fita daga cikin idanunsa, miƙewa zaune yay yace "Lolly talk to me" nan ma tai masa shiru cikin tsawa yace "What wrong with you Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza Deen.!!!!".

Vote
Comment
Follow please

MOONWhere stories live. Discover now