69-70

1.4K 109 20
                                    

Da sauri yake taka ƙafafuwansa a ƙasa yana tafe yana fesar da iska daga cikin bakinsa, idanunsa ya kaɗa yay jaa sbd tension ɗin da yake ciki, cikin isa da gadara da kuma zallar izzar daya samu kansa da ita a lokaci yake tafiya a cikin Maison Santé Rémusat zuwa ward ɗin da aka kwantar da ita, yana tafe Ammar da Faizak na biye dashi gaba ɗaya cikin babu wanda zaka iya tantance abinda zuciyarsa take faɗa masa akan sabon al'amarin daya samesu, har suka isa ward ɗin babu wanda yaywa ɗan uwansa mgna, a  bakin special female surgical room ɗin da aka kwantar da ita suka samu Nene da Besty sai kuma Yakumbo, Waje yaja ya tsaya yana lumshe idanunsa tare da fesar da numfashi cikin ƙasa da Murya yace "BESTY!"  Ware ido Eneye Ahuoyza yay yana ƙara kallon ɗan nasa wanda yar yanzu mmkin bai yanarsa bai sakesa ba, miƙewa yay tare da ware masa hannayensa, cikin nutsuwar data fara samunsa ba kamar da ba ya fara jan ƙafafuwansa wanda ya kejin sun masa nauyin gske ya nufi wajan mahaifin nasa, jikinsa ya shige yana ƙara maƙale sa, bayansa Besty ya shafa tare da bubbuga bayansa yace "Don't cry my King" cikin sabuwar shagwaɓar data samesa ya sauke numfashi tare dayin ƙasa da Murya very slow yace "Besty! Queen Maimunatou" kansa ya shafa cikin kwantar masa da hankali yace "just pray for her, in sha Allah! Ubangiji na tare da ita matarka zata samu lafiya anyi theatre an cire all bullet ɗin daya taɓa mata jiki, na bayanta ne kawai matsala,na hannunta kuma bai sameta sosai ba" shiru yay kawai yana fidda numfashi kafin ya zare jikinsa cikin nutsuwa ya nufi cikin room ɗin da take, gaba ɗaya suka bi DEEN da kallo kowa yana jinjina ƙarfin soyayyyar da Aliyou ya kewa Maimunatou. Slowly ya sanya hannunsa a saman handle ɗin ƙofar tun a bakin ƙofar ya fara jiyo fitar numfashinta dake fita da sauri², ga kuma ƙarar computer da akai using dashi wajan maƙala mata oxygen ɗin dake taimakawa numfashinta wajan samun damar fita yadda ake so, hannunsa duka biyun ya zuba a jikin aljihu yana ƙarewa innocent face ɗinta kallo wacce ta faɗa lokaci guda, gently ya fara takawa zuwa wajan gadon gadon tare da ɗaukan chair  ya zauna kusa da kanta, lumshe idanunsa kana ya buɗe ya fara bin blood dake maƙale a hannunta yana shiga cikin jikinta, a karo na biyu kenan jininsa na shiga jikinta, ɗaya hannun kuma drip ne ki shiga a hankali, hannunta ya kama ya riƙe a hannunsa ya fara murzawa a hankali yadda bazai dameta, Ring ɗin hannunta ya gani wanda ta mai da shi ƙaramin yatsarta sbd kaɗan din yay mata, a hankali kuma ya sumbaci hanunu yana faɗin "Wake up My Queen Maimunatou, nothing will happen to you again, nothing   my Shona my Moonlight, no more separate My Lolly am with you forever and ever always Darling Habibaties, kin daina kukan rashin mijinki I'll make you happy zaki alfahari da samuna zan mai daki Shalelen King Aliyou Eneye Ahuoyza Deen" ya ƙare maganar wasu hot tears na bin fuskarsa, soyayyarta shine weakness nasa ya gama tabbatar da hakan, babu wanda zaice yaga kukansa sai ita,to yaya zai yi ta riga ta zama jinin jikinsa ta zama bugun zcyarsa, kanta ya shafa yana ƙara gyara mata kwanciyar da akai mata ta rufda ciki sbd harbin da akai mata a baya. Wayarsa ce ta shiga ƙara screen ɗin wayar yabi da kallo ganin number na yawo yasa yaja tsaki domin yasan m.k ce tuni ya bata waccan wayar ya amshi asalin tasa a wajan Ammar daman tana nan babu abinda akai da ita. Miƙewa tare sumbatar forehead ɗinta kana yay waje yana tamkar ya dawo da ciwon kansa, Ammar kawai ya gani a wajan a tsaye sai kuma m.k da zuwanta kenan, kallo ɗaya yay mata ya ɗauke Ammar ne yay ƙasa da Murya yace "Sarki Aliyu Al'amin ne ya ƙara su shine suka tafi airport daga nan kuma zasu huce hotel ɗin da suka sauka, shiru yay ko tari bai ba sai da wani Dr ya ƙarasu wajan yace "Wannan patient naku he's in critical condition" tsaki Deen yaja yay gaba abinsa yana tafe yana duba Rolex ɗinsa dake maƙala ne a hannun Patek philippe, da idanu m.k ta bisa da kallo tana jin zuciyarta babu daɗi, fatanta ɗaya kada ya rabu da ita domin soyayyarsa ta gama ratsa zuciyarta. Ammar ne yabi bayan Dr Salamon har zuwa cikin wani room ɗin tun daga baƙin ƙofa yana jiyo surutansa  da yadda yake bige² shi ɗaya, ƙarasa shiga yay ciki a hankali ya bisa da kallo musamman ƙafar data fita da kuma hannunsa daya cire sakamakon accident ɗin daya faro lokacin daya kaiwa Deen hari, yana tsaka da harbin kuma wata motar ƴan kwana kwana tai gaba da motarsa zuwa cikin wani rami, nan take motar ta kifa ta ƙara kifawa sai data kifa sau uku sannan ta tsaya, tashin farko gaba ɗaya yaransa sun mutum shi kuma a take a lokacin ƙafarsa da hannunsa suka fita, yanzu ma tsananin azabar dake cinsa yasa yake ta ihu shi ɗaya anyi masa injection domin ya samu bacci ya ɗauke sa amma ina ko gyan gyaɗi bai ba sbd karfin da jininsa yake dashi. Washe gari aka ƙara yi mata treatment ɗin wajan, har yanzu bata farka ba amma kuma tana cikin hayyacinta kawai allurar hutu ake mata.

MOONWhere stories live. Discover now