11-12

1.6K 118 12
                                    

Belet ɗin dake maƙale da jikin kujerar ta,ya zameta yay a jikinsa kana ya ɗaura mata belet ɗin,kallonsa kawai take tana ɗan lumshe idanunta wanda sukai  kumbura sbd kukan da tayi jiya,lafewa Deen yay jikin kujerarsa tare dajan idanunsa ya lumshe,a hankali baturiyar cikin jirgin ta fara faɗa kowa ya shirya jirgi zai tashi,Nana dake kusa ta Ovasi ta kalli Deen wanda ko inda take bai kalla ba, kuma tana da tabbacin shine ya bata offer ta aikin,a haka jirgin ya fara shawagi a ƙasa kafin a hankali ya fara yin sama-sama har cikin gajimare Moon dake zaune tana rarraba idanu tayi saurin ƙanƙame jikinta sbd karkarwar ba jirgin yay a hankali jirgin ya ɓace cikin gajimare.

ABBA ya fito daga cikin part ɗinsa da sauri da sauri yana yi yana gyara zaman babbar rigar sa,a main parlour yaci karo da Farouk wanda ya fito daga cikin part ɗinsa yana gyara zaman agogon hannunsa, kallo Abban nasa yayi ya ɗauke kai,a tare suka fita compound na gidan kai tsaye cikin motarsa ya shiga inda yabar Farouk tsaye ya harɗe hannayen sa a ƙirjinsa, horn yay yana jiran mai gadi ya buɗe masa amma yaji shuru,sama da 3minutes ya leƙo kai yace "Farouk jeka kira min mai gadi" ba tare da Farouk yay magana ya ƙarasa ɗakin mai gadin, knowking door yay  shima yaji shuru ɗan tura kansa yay ciki,wani lafiyayyan murmushi yyi kafin ya juya zuwa inda Abba yake yace
"i think baya nan,kamar dai ya tafi"
fitowa Abba yay daga cikin motar yace
"ban gane bai nan ba?" Yana faɗin hakan yana nufar ɗakin,baki ya saki ganin babu kowa hatta akwatin sa babu ita,hannu yasa ya share zufar da ta yanko masa,kana ganinsa za kaga zallar damuwar dake ƙwance  a saman fuskarsa,kallon Farouk yay yace
"meke nan Farouk?" Farouk ya cije baki kafin yace
"ya gudu Abba,daman ai kai ka bashi yarda tun farko"
da mamaki Abba ya ƙara faɗin
"meye amfanin tafiyar tasa? Ko ya aikata wani laifi ne? amma abin ya ɗaure min kai wlh"
juyawa Farouk yayi ya nufi fita daga cikin gidan, sai da yaje wajan gate Sannan ya ɗan kalli Abban nasa ta gefen ido yace
"sai ka saka ayar tambaya a kansa,amma ni na daɗe sa sanyawa,kuma ina tabbacin yana dasa hannu a kan rasuwar iyayen Maimoon"
jinjina kai Abba yay a kuma dai-dai lokacin wayarsa dake cikin aljihunsa ta fara ƙara alamar kira ya shigo,da ɗan sauri yay picking call ɗin yana manna wayar a kunnansa yace
"C.P Aƙwai matsala,OHHH too Allahamdulillah tunda kama ƙara su,ok bari na fito"
rejecting call ɗin yay tare da fita daga cikin motar,yana fita yaga motoci da yawa kusan  uku wani magidanci ne ya fito daga cikin motar tsakiya ya nufi inda Abba yake tsaye,yana zuwa ya miƙa masa hannu sukai musabaha,mutumin ya kalli Abba yace
"Nasan zakai mamaki ko?to a zahiri C.P baya gari,bai nunar a faɗa maka bane sabida baza kaji daɗi ba,yace na famshesa kafin ya dawo dukkan abinda kake buƙata ka gaya min,fatan babu Matsala?"
kai Abba jinjina cike da gamsuwa da maganar A.C.P yace
"Wannan ba abin damuwa bane ai,daman burina ace manyan masu  ƙare haƙƙin ɗan adam da kuma rayukansu su shiga cikin wannan rikitaccen lamari" murmushi A.C.P shima yayi kana yace
"Muje ciki muga,sabida idan muka bincika zamu iya samun wani Evidence ɗin"
Gaba ɗaya suka nufi gidansu Moon,suna zuwa Abba yasa key ya buɗe ƙaramar ƙofar gidan wanda tun jiya yasa aka siyo masa ƙwaɗon ya rufe gidan da shi,ta bakin ƙofar suka fara ƙaro da bushassen jini,kai tsaye suka nufi cikin gidan duk binciken da sukai babu wata shaida da suka samu sai kuɗaɗen Dadyn Moon da akai filla-filla dasu,duk abinda suka ci karo da shi a cikin gidan sai sun ɗauki photonsa,duk girman gidan babu inda ba'a duba har suka kammala kana suka fito waje, Abba yace
"Yawwa A.C.P wani abun ya ban mamaki yanzu haka,yaron da yake min gadi munwayi gari babu shi babu labarinsa"
A.C.P ya zare glass ɗin idanunsa ya ƙurawa  Farouk dake shiga cikin gida Idanu,kafin ya bayar da glass ɗin yace
"Muje inda yake ƙwana" gaba ɗaya kayan Deen na sayawa suna ɗakin,hatta ƙwanukan da aka bashi lunch suna ɗakin,Abba ya sauke ajjiyar zcy cikin Muryar sarewa yace
"Babu abinda ya bari sai kayansa,duk na rikici nama rasa meye amfanin hakan da yay,ko aikin ne bai so ai zai iya sanar min a bashi haƙƙinsa kaga sai ya tafi abinsa"
Shuru A.C.P yay sabida wata farar paper daya gani a ƙasan pillow,warwarewa yay ya fara karantawa a fili kamar haka

_BA ABIN MAMAKI BANE DAN KA NEMI DEEN KA RASA,NI WALƘIYA NE A DUK LOKACIN DA NASU BAI YANA NA KAN BAI YANA NE BA TARE DA WANI HAUFI BA,KA MAIDA ƘULAFUCINKA ALHAJI BASHIR YAHYA GIDAN KUƊI,HHHHH!! ALBISHIR GUDA NAKE SON GAYA MAKA, TABBAS ZAN DAWO GAREKA  A RANAR DA ZAN BAKA MAMAKI,NI ƊIN BA YADDA KAKE TUNANI BANE,NI AZZALUMI NE,NI MUGU NE,NI MACUCI NE,DUKKAN ABINDA KAKE TUNA NI NA HUCE HAKA, I'M DEEN THE CRIMINAL MAN_

Abba ya zauna a ƙasan carpet ɗin ɗakin tare da zame hular kansa,gaba ɗaya kansa ya ɗaure yama rasa wanne kallo zaiwa wannan al'amari,waye Deen? Me yake nufi da maganganun da yay? Mene yasa yazo masa a matsayin ƙasan ƙantacce wanda baya da kowa baya da komai? Me yake nema a wajan sa?
Wata iska mai zafi Abba ya fesar ta cikin bakinsa kafin ya miƙe da sauri yace
"A.C.P ya kamata kayi wani abu akan wannan yaron,ina tsoron abinda zai je ya dawo, Tabbas lamarinsa ya sani cikin tashin hankali wlh"
A.c.p ya jinjina kai tare da naɗe takardar ya sanya a cikin aljihunsa, daga haka yaywa Abba sallama tare da masa alƙawarin duk abinda ake ciki zai faɗa masa,kuma daga yanzu zai fara bibbiyar rayuwar Deen.
Gdy Abba yay masa kana ya juya zuwa cikin gidansa a parlour ya samu Ummi da autarsa Yasmin,zama yai shima yana sauke numfashi,Kallonsa Ummi tayi sabida tasan ba haka mijin nata ya fita ba,gyara zama tayi tare da faɗin
"Abba lafiya dai (dake itama haka take faɗa masa) numfashi ya sauke yace
"KHADIJAH aƙwai matsala,yaron nan ya ha'ince mu,ya yaudare mu,ya sanya mun so shi kuma mun yarda dashi,gashi yanzu yana ƙoƙarin tuzarta mu"
Cikin rashin fahimta Ummi tace
"Abba ban gane ba,wa kake magana a kansa ne?"
Abba yace
"Wannan mai gadin mana,ya gudu ni ba guduwarsa ce matsala ta ba,dalilin guduwar tasa nake son ji"
Ummi tace
"Ikon Allah, Allah ya ƙyauta to" Yasmin dake zaune kusa da Ummi tana shan tea tace
"Abba to basai ka rabu dashi ba, ƙilan wani aikin ya samu"
kallonta kawai yay ba tare da tace komai ba,ya miƙe tare da nufar part ɗinsa, Farouk dake tsaye tun ɗazo yay murmushi shima ya fice daga cikin gidan gaba ɗaya.

*BANGLADESH*
Pakistan, Thailand, China, India, and Bangladesh are in the top 10 for countries with the largest number of trafficking victims around the world. India is at the top of the list with 14 million victims, China comes in second with 3.2 million victims, and Pakistan comes in at third with 2.1 million victims.

Dhaka Hazrat Shahjalal International Airport (Hazrat Shahjalal International Airport
Hazrat Shahjalal International Airport, Dhaka
This is the largest and the principal international airport of the country. It is situated at the capital city Dhaka.

A hankali train ɗin yay saukar ungulo a Hazrat Shahjalal International Airport,da sauri baturiyar cikin jirgin ta fara sanarwar kowa ya shirya jirgi ya sauka,gama faɗarta keda wahala jirgin ya gama parking a harabar airport ɗin,a hankali kuma passengers ɗin suka fara ɗaukan travelling bag ɗinsu tare da fita.
Ovasi ya miƙe tsaye tare da ɗaukan jakar Deen ya kalli Nana wacce take zaune yace mata
"muje ko"
jin hakan yasa ta miƙe ta ɗauki jakarta tana mai satar kallon Deen wanda yake zaune ya lumshe idanunsa yana sauke numfashi da sauri da sauri,kallo guda zakai ma Deen kasan irin masifaffun mazan nanne kuma mai girman kai wanda bai damu da kowa ba sai kansa,bayan Ovasi tabi har suka sauka daga cikin jirgin
Sama da 20 minutes  wata ma'aikaciyar jirgin ta ƙarasu inda Deen ke zaune, kallonsa tayi kana ta juya ta kalli Moon wacce ta kewa kallon ƴarsa, tace
"Yallaɓai kai ake jira a rufe jirgin"
ta faɗa cikin harshen turanci,ware manyan idanunsa yay wanda sukai jaa tare da janye wa kaɗan,ba tare daya kalleta ba ya zare belet ɗin jikinsa,da sauri kuma ya miƙe ya nufi fita daga cikin jirgin da sauri ta kallesa tace
"Ka manta babbynka?" tsayawa yay cak yana son ya fahimci maganar ta,kafin yay wani abun ma'aikaciyar ta ƙara faɗin
"Your daughter"
Hannunsa ya dunƙule cikin zafin nama kuma ya dawo da baya,da sauri taja baya ganin yadda yake huci shi kaɗai,kamar zai tashi sama haka ya ƙarasa wajan Moon dake bacci ya zare belet ɗin jikin ta,hannu ɗaya yasa ya ɗauke ta zuwa kafaɗar sa,gudu-gudu sauri-sauri haka yake tafiya har ya isa harabar airport ɗin,can ya hangi Ovasi wanda aka gama bincika jakar kayansa, security ɗin ne ya kalli Deen yace
"Za'a bincika jikinka"
Ba tare dako gizau ba Deen ya tsaya tare da ƙara gyarawa Moon zama a ƙafaɗarsa,da manyan idanunsa ya kalli security ɗin kana ya ɗauke kai,jinjina girman kan Deen yay shima ba tare da yace komai ya nufi inda Deen yake tsaye,na'urar binciken ya karawa Deen kamar wasa na'urar ta fara ƙara da  mamaki Deen ya juya manyan idanunsa a zcyarsa yana faɗin "what the fuck!" Security yay murmushi yace "you're under arest..



COMMENTS, COMMENTS
SHARE SHARE sabida Allah👏🏻

Wattpad dan Allah ku dinga comments da vote Please follow me😍
08119237616

SARAUTA👑

MOONWhere stories live. Discover now