61-62

1.2K 102 15
                                    

Saurin zare jikinta tayi ta nasa ta shiga haɗe fuska, Murmushi Faizak yay mata yana jin ransa babu daɗi cikin ƙasa da Murya yace "Am sorry,i can't control myself idan muna tare" banza tai masa sai hawayen da suke shiga zuba daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta,da sauri kuma ta fara tafiya tabar masa lambun gaba ɗaya, iska ya fesar kafin yace "what should I do?" Ya faɗa yana dafe kansa dake juya masa,da sauri shima yabar cikin lambun kai tsaye ɓangaren dawakai ya nufa ya samu sarkin dawakai suka fara mgna kafin a ɗauko masa wani farin doki ingarma mai girman gaske,da sauri ya kama silken dokin ya hau cikin sauri kuma ya saki linzamin dokin yay waje da gudu.. washegari ta kama Friday tun asuba ta tashi da wani irin ciwon ciki mai a zabar gaske ga wani kumburi da mararta tayi mata, ciwon kai zazzaɓi duk suka taro waje guda sukai mata yawa, da ƙyar ta lallaɓa tai sallar asuba ta koma ta kwanta a hankali bacci yay gaba da ita sbd baccin da bata samu tayi ba, cikin baccinta taji amai na tasu mata da gudu tai bathroom ta shiga kwarara amai a cikin sink kamar zata amayar da abinda yake cikinta, Fulani dake bakin ƙofar bedroom ɗin ta tura ƙofar a hankali ta shigo, kamar zata shiga bathroom ɗin kawai saita zauna bakin bathroom ɗin ta shiga bin ɗakin da kallo, tana rawar sanyi ta fito daga cikin bathroom ɗin da sauri Fulani ta riƙeta tana faɗin "dabe careful" kwantar da ita tayi ta rufeta da duvet kafin tace "how long baki da lfy?" Bakinta yana rawa tace "jiya ne" miƙewa tai tace "Am coming" tana faɗin hakan ta fice daga cikin bedroom ɗin. Fulani na fita ta nemi mai Babban ɗaki tai mata iso a wajan sarki, babu daɗewa mai Babban ɗaki tace ta shiga, yana zaune a saman wata ladduma  mai taushi da kuma laushi, sanye da shigar ta Alfarma ga takubin Sarauta a gefensa yay kyau sosai kamarsa da Moon ta ƙara bai yana fiye da kullum, zama tayi cikin ƙasa da murya tace "Salam my king" murmushi yay mata yace "Salam Queen Maryam" kallonsa tayi tana sakin Murmushi shima kallonta yay domin kaf cikin matansa babu wanda yake so sama da Queen Maryan yace "what's the matter?" Kanta a ƙasa tace "My king Autar ka ce babu lfy,shiyasa na nemi iso domin nazu na gaya maka" da sauri ya mike tare da ɗaukan takubinsa yace "what exactly wrong with you Queen Maryam? Shine tun safe baki faɗan ba sai yanzu, let's go" ya faɗi hakan yana kama hannunta cike da izza da taƙama yake tafiya zuwa flat ɗin ƴar tasa,tun a hanya ya kira Dr Masarautar ya faɗa masa yana nemensa yanzu, babu jimawa Dr ya ƙarasu har cikin ɗakin Princess Moon or Queen Maimunatou, bayan ta dubata sosai ya tabbatar da abinda yake damunta drip yasa mata bacci ya ɗauke ta, Faizak dake tsaye yace "meke damunta?" Dr yace "time ɗin prioud ɗin ta ne ya fara" da mmki Yakumbo tace "kana nufin bata fara Al'ada ba sai yanzu?" Jinjina kai Dr yay yace "that's what I mean" tace "da matsala idan haka ne" Dr yace "matsalar me? Bari kiji cikakken bayani akan Al'ada:

Menene Jinin Al'ada? Jinin al'ada jinine da yake fita da karan kansa daga gaban macan da a al'dance zata iya daukar ciki ba tare da ya wuce kwanaki goma sha- biyarba. Wannan shi ake nufi da jinin al'ada, da akace 'jinine da yake fita da kansa' kenan idan ya zamana ba da kansa ya fitaba kamar ace cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jinni ya balle mata to wannan bai zama jinin al'adaba. Da akace 'Ta gaba' kenan idan ya fita ta dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin al'adaba. Da akace 'Wacce a al'adance zata iya daukar ciki' kenan idan ya fita daga wacce a al'adance ba zata iya daukar cikiba sabo da yarinta ko girma to wannan shima bai zama jinin al'adaba. Amma da aka ce 'Ba tare da ya wuce kwanaki goma sha-biyarba' kenan idan ya wuce kwanaki sha-biyar to bai zama kuma jinin al'adaba. Wadannan nau'uka da akace basu zama jinin al'ada ba kenan hukuncin jinin al'ada bai hau kansu ba za su yi sallah domin jinin ciwone sai a nemi magani, Allah ya sawwake.

Mafi Karancin sa: Malamai sun karawa juna sani kan mafi karancin jinin al'ada, mafi karancinsa shine 'dugo guda' kenan idan ya duga sannan ya dauke, shikenan ta yi al'ada kuma ta dauke.

Mafi Yawan sa: Mafi yawan kwanakin jinin al'ada shine kwanaki goma sha-biyar kenan idan ya wuce haka to bai zama jinin al'adaba muddin ba ciki take da shiba.

MOONWhere stories live. Discover now