17-18

1.3K 128 13
                                    

Harta kai glass cup ɗin bakinta sai kuma ta tsaya tana ƙarewa cup ɗin kallo kamar mai nazartar wani abu,a hankali kuma ta ɗura cup ɗin anakin ta cikin nutsuwa ta fara shanye haɗaɗɗan tea ɗin wanda yasha suger,milk, bonvita,duk zafin shayin bai hanata shanye wa tass ta ajjiye cup ɗin tana kallon Damus a ɗan tsorace ba,dry yay kana ya amshi cup ɗin yace
"Good beauty, kinyi aiki mai ƙyau"
Da ido kawai take kallonsa harya fice daga cikin ɗakin,yana fita Deen ya fito tare da neman kujera 3seater ya zauna akai, Moon tsayawa tayi tana kallon sa sbd yadda lokacin ɗaya ya sauya daga yadda ake ɗazo zuwa yanzu, idanunsa sunyi jajir sun janye kamar mai jin bacci, jijiyoyin kansa suyi raɗa raɗa a saman goshinsa,jikinsa banda ɓari babu abinda yake,sai fesar da wata zazzafar iska ta cikin bakinsa yake,ganin yasa Moon ta fashe da kuka still idanunta na kan Deen, runtsa idanunsa yayi sbd har tsakiyar kansa ya kejin kukan nata, ganin bata da alamar yin shuru shi kuma bai wani abu lallashi ba,yasa yaja tsaki tare da miƙa mata hannunsa alamar tazo garesa,abinda take jira kenan tana ganin hakan ta nufi wajansa ta gudu tana zuwa ta haye saman kujerar tare da shigewa jikinsa ta rirriƙesa, yatsansa ya ɗura saman lips ɗinta a hankali cikin iriyar murya yace
"Shiiiiiit...!"
Shuru tayi ta fara sakin ajjiyar zcya akai-akai kamar wacce ta shekara tana kuka,shuru shima yayi yana sauraran bugun zcyarsa da kuma yadda take sauke ajjiyar zcya mai ƙarfi,mutsi gudu yay sai ta ƙara ƙanƙamesa,Damus na fita ya nufi wani special side kai tsaye ya danna telephone line dake sama,wata maid ce ta ɗaga tana ɗagawa yace "haɗa ni da Eki"
Jikinta na rawa tace "okey sir"
Da sauri ta kiran line ɗin side ɗin su Eki babu jimawa aka ɗaga kiran tayi Sa'a kuma Eki ce tayi picking call ɗin, haɗe kiran tayi waje guda kana ta shaidawa oga Damus Eki tana kan line, Eki tace
"Good morning Sir"
Daga can ɓangaren yace mata
"Mrng,ina yarinyar nan kaya sun kammalu aiki yana wajanki"
Fari tayi da idanunta kafin tace "Sir daman umarnin ka ake jira,yanzu za'ai komai a gama"
Damus yace "okey good,kizo ki amsa yanzu,alrdy na gama da yarinyar"
Eki tayi dariya tace
"Baka da ƙyau sir"
Tana faɗin hakan ta ajjiye kan wayar ta shige bedroom ɗin data fito,zaune ta samu Nana tana gyara gashin kanta,tana sanye cikin wata duguwar riga,mai ƙirar buba amma duk da faɗin rigar hakan bai sanya jikinta ya ɓoye ba, bayan ta gama ƙare mata kallo tace
"My dear bari a kawo maki breakfast,naga acan baki sakewa tare damu"sosai hakan yaywa Nana daɗi domin a cikinsu jinta take a takure bata iya sakewa taci abincin yadda ya kamata, murmushi saman leɓe tai mata tace "ok! Thank you"
Juyawa Eki tayi a hanya suka ci karo da Salmerh haɗe rai tayi kafin taka waje ta tsaya tace "da wasa naga kin shiga part ɗina wajan NANCY saina haɗaki da oga,kin san punishment ɗinki dai wallahi yanzu za'a haɗaki da ƙarti biyar" ita dai Salmerh bata tanka ta ba tayi shigewarta aiken da granny tayi mata.

Yana zaune Moon na jikinsa baice mata ci kanki ba har bacci ya ɗauke ta,ganin hakan yasa ya miƙa tare da ajjiye ta a kan sofar ya nufi cikin wani bedroom,duk yadda yakai daya samu nutsuwa a wannan lokacin kasawa yay sbd zuciyarsa da yaji tana zalzalashi zuwa ga abinda bai yi niyyar sa ba a yanzu,gaba ɗaya tunaninsa ya goshe wani duhu yake gani a cikin idanunsa,dole zaibi abinda zuciyarsa take kwaɗaita masa,da gudun daya gama zama jinin jikinsa ya ƙarasa shiga cikin bathroom ɗin dake cikin bedroom ɗin part ɗinsa,wanda aka ware masa daban a cikin gidan,yana shiga ya zare kayan jikinsa ya sakarwa kansa shower,a zafafe yake wanka da ruwa mai sanyi duk da irin sanyin da ake busawa a ƙasar,yana kammalawa ya juna handrayer ya budar da kwantaccen gashin kansa,kafin yay brush ya fito,kansa ya tsorawa idanu da jikin makeken madubin dake maƙale a dressing mirror,gaba ɗaya Deen yabi ya birkita kansa kamar kumurcin zaki,bai wani damu da shafa mai a jikinsa ba,ya ɗauki body spray ya fesa a saman fresh skin ɗinsa,wajan wardrobe ya nufa ya ɗauki wani blue black ɗin crazy jeans ya saka tare da riga armless,bayan ya gama ya ɗauki facecap ya sanya saman sumar kansa,kai tsaye ya ƙarasa wajan trolly ɗin sa ya ɗauki ticket daya yanka tare da wayoyinsa Wada wasu muhimman bayanai,yana gamawa ya fice daga cikin bedroom, tsayawa yay yana kallon harya ɗaga ƙafa zai ƙarasu inda take sai kuma ya juya da gudu yabar part ɗin,bai tsaya ko ina ba sai harabar gidan,wata ash ɗin mota ya shiga drever yaja da sauri ya nufi airport dashi.

MOONWhere stories live. Discover now