*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).®️Hajja ce👈
Wattpad... Hajjac.
YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g*SAWUN GIWA....*🐫🐘
Page 1
Da sauri take sakkowa daga matakalar jirgin, idanuwanta sanya cikin farin glasses wanda ya kuma ƙayatar da kyakkyawar fuskarta. Tana gaba securities suna biye da ita dan kare mata lafiyarta, sai da tazo dai-dai motar da zata shiga, sannan ta juyo da sauri tana kallon ɗaya daga cikin su, ta kafe shi da ido kamar wanda ya yi mata laifi kafin tace.
“Kun ce baku sanar da excellence ba ko?”
“Yes ma! bamu gaya masa ba.”
“Good! kuzo muje.”
Daga haka aka buɗe mata murfin ƙofar ta shiga ta zauna tana ta faman share gumi saboda shiga cikin tashin hankali. Suna zuwa ko gama parking driver beyi ba ta ɓalle murfin motar ta fito, cikin tsantsar tashin hankali ta shiga reception tana waige-waige. Bodyguard ɗin ta da ta kasance mace ita ce ta mata magana kan cewar ta bari su tambayo ma'aikatan asibitin. Bata ce komai ba guard ɗin ta wuce inda ta hango nurses na gudanar da aiyukan su. Cikin ƴan mintuna sai gata ta dawo hannun ta riƙe da ƙaramar takarda, tana zuwa miƙa mata tayi tana cewa.
“Room number ɗin ne.”
Ta karɓa ta duba tare da yin gaba suna take mata baya har suka je gurin kofar da aka basu lambar ɗakin. Gabanta ne ya dinga bugawa ta rintsa ido tare da kai hannu kan handle ɗin ƙofar, cikin azama guard tayi saurin saka nata ta buɗe tare da komawa gefe guda dan ba ta damar shiga. Tana saka ƙafa suma suka sanya tasu, ta ɗago ido da kyar ta ɗora akan gadon inda ta hange shi kwance duk ya sha bandeji tamkar ba shi ba.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Ahsan me zan gani haka?”
Ta faɗa tana jan ƙafa zuwa gurin da yake kwance, kura masa ido tayi dan ta kasa gasgata cewa shi ɗin ne a kwance saɓa masa kamanni kawai aka yi. Ta shiga girgiza kai tana yin baya cike da da tashin hankali take cewa.
"Wannan ba Ahsan ɗina bane, kuje ku dubo min nawa." Duk suka yi shiru kansu a ƙasa sannan suka ƙi motsawa.
"Baku ji abin da nace muku bane?"
Ta faɗa cikin tsawa, jikin guard ɗin ta na rawa tai salute tare da ƙamewa tace.
"Sorry excellency, but wannan shine Ahsan ɗin ki."
Tana gama jin haka hawaye suka ziraro daga cikin kyakkyawar fuskarta, ta ƙarasa kusa da gadon tare da durkusawa a gurin tana kuma ƙare masa kallo cike da tausayawa. Allah sarki Ahsan yaro mai nutsuwa da kamala uwa uba kauna ta gangariya da yake yiwa iyayensa. Duk wata rawar kai irin ta yaran masu kuɗi da masu mulki ba ya yin su, Allah ya raya musu shi cikin nagartacciyar rayuwa da duk wani uba ko uwa zasu so ganin sun samu irin shi.
Shigowar Doctors ne ya dakatar mata da hawayen da take yi, tai azamar miƙewa tsaye da zummar yiwa likitocin tambayoyi amman sukai saurin dakatar da ita ta hanyar cewa kowa ya fita zasu duba shi. Cikin tashin hankali ta kuma buɗe baki zata yi magana suka nufi gurin da yake kwance, ita kuma guard ɗin ta cikin lallashi ta samu suka fito da ita.
“Kiyi haƙuri yarinki ya daɗe, Insha Allahu zai samu lafiya.”
Gaba ɗaya ta manta a gaban waɗanda take zubar da hawayenta, saboda rufewar da idanunta suka yi na ganin ɗanta kwance rai a hannun ubangiji madaukakin sarki, wanda yake saukar da ciwo a duk lokacin da ya ga dama ya kuma warkar da wanda yaga dama a lokacin da yaso yin ikon sa. Ƙarar wayar ta yasa ta ɗan dawo cikin nutsuwarta, ta ciro daga cikin tsaleliyar jakarta, tana dubawa taga mai kiran gabanta ya yanke ya buga da ƙarfi. Me zata gaya masa yanzu? Gashi tasha kuka shin da wace irin murya zata amsa kiran da yake yi mata? Kiran ya yanke ba tare da ta gama tsaida shawarar abinda zata gaya masa ba.
![](https://img.wattpad.com/cover/281054016-288-k11576.jpg)
YOU ARE READING
SAWUN GIWA... 🐘🐫
RomansLabarin wata matashiyar yarinya yar sarki da ta kasance shalele, sai dai kaddara ta gilma mata wacce ta sanya ta cikin.....