SAWUN GIWA Page 5🐪🐘

172 24 4
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV* https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)*

*SAWUN GIWA....*🐫🐘

Page 5
(Na bati ne)💃

"Wanka yabi jiki uhm! Baku san ana talauci gayu..."

"Karima wai baki tashi kinyi wancan tankaɗan ba? Me kike jira ne?"

Karimatu taji mahaifiyar ta na tunatar da ita yin tanƙaɗe, ta turo baki tana tuna gidan attajirai da suke da masu aiki, yaran gida suna ɗaki kan lumtsumemiyar katifa suna bacci ko Chatting. Ita kam ta rasa me yasa tazo a irin wannan gidaje na yaku bayi, ta manta ba kowa yake yin halitta da kuma tsarawa kowa rayuwa face ubangijin da ya barta da numfashi cikin ƙoshin lafiya ba tare da wata nakasa ba. Ta kasa godewa da ya yo ta gidan rufin asiri da suke iya ci da sha kullum fiye da uku a rana, ga ilimi sun samu dan malam khamis jajirtacce ne, yana ƙoƙari sosai wajan kula da iyalansa.

Da kyar ta mike tana ƙunƙani ta ɗako rariya da farantin da zata yi tankaɗan a ciki, ta kuma janyo kujera ƴar tsugunno ta zauna tana yi tana tunanin yadda in ta samu damar auran attajiri zata dena ta'ammali da cin tuwo, ta ɗauki aniyar tun suna taɗi zata gaya wa saurayinna ta cewa ita tuwo ciwon zuciya yake saka mata, ta yadda ma ba zai yi mata maganarsa ba bare yace tayi musu wata rana. Ta kalli can gefe inda ƙanwarta ke dakan daddawa da kayan ƙamshi na miyar kuka da zasu kaɗa, ta girgiza kai haushi kamar ta fashi da kuka.

Karimatu na kammala tankaɗan ta kai kitchen bata ƙara sanya hannu a komai ba ta shige ɗaki, bata fito ba sai da aka kira sallar magariba tayi alwala ta koma ɗaki, bayan ta idar ta ɗakko carbi tana ta jan ya wadudu tare da kiran sunan guy ɗin da ta gani a IG tana faɗin.

"Ya Allah irin wannan da na gani ka bani shi a matsayin miji, ko ɗan gidan waye ni dai ya yi min har cikin zuciya ta. Allah ka tsole idan duk wanda baya son na mallaki saurayin nan."

"Karimatu wannan wace irin addu'a ce kamar ta marasa sanin ya kamata? Waye wannan kika gano har kike fatan samun sa ke da baki san halinsa ba?"

Ummansu da ke jiyo ta tayi saurin yi mata magana dan taji abin kamar harda rashin sanin ya kamata, banda hauka haka ake addu'ar samun abu kace ko ɗan waye, bayan baka da masaniyar ta ya suka samu abinda suke dashi. Me ya sa wani lokacin ake samun gushewar hankali da tunani idan za a roƙi Allah dacewa? Daman dole idan buri ya yi yawa a dinga samun irin wannan abubuwan na rashin hankali, idan ɗan fashi ne kenan tana son sa saboda yana da kuɗi? Ko kuwa idan ɗan cult ne shima tana so? Ko kuma idan hanyar samun nasa bata da kyau fa, kawai ta ganshi cikin daula da ni'ima ta duniya shine za ta yiwa kanta wannan addu'ar.

"Umma ai yanzu kuɗinka sune halinka, kuɗi fa babu abinda baza su siya ba Umma. Kinga in kana da kuɗi zaka yi rashin mutunci in kaga dama kasa a kamo maka wanda yake neman takura maka. Sannan idan kana dasu zaka yi mutunci da duk wanda kake son yi. Haka zaka je duk ƙasar da kake so, kaci abinda kayi niya, ka kwanta inda ka ga dama. Idan baka dasu fa? Kanaji kana gani abu yafi karfin ka, kamar yadda rashin kuɗi ya hana Hanne tafiya makarantar da take buri."

Karimatu tai maganar cikin tausasa harshe tana kallon mahaifiyar ta, saboda  ita fa ta riga ta gano cewa kuɗi rahama ne ga duk wani ɗan adam mai zuƙar numfashi. Umman tasu ta zauna a bakin gado tana cire hijab ɗin da ta idar da sallah, ta karo hasken fitilar dake gefenta tana magana.

"Toh waye yace miki su masu kuɗin basu da wata damuwa? Ko ce miki akai indai kana da kuɗi shikenan an yaye maka matsalolin duniya Karimatu?"

"Amman Umma a ƙalla an yaye maka cassa'in a cikin ɗari."

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now