SAWUN GIWA Page 18🐪🐘

120 25 6
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).
2021

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV.* https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)*

*STYLISH BCH SPECIAL CARE!*

*Matar aure,💪 uwa sannan kuma ƴar kasuwa. Duk wadannan abubuwan basu hanani kula da yarana, mijina, gidana da kuma jikina. Bani da ƴar aiki ni kadai nake kula da ko wane sashe kuma idan ka kalla sai ka yaba saboda babu kazanta. Ƴar uwa...! Me yake hanaki kula da jikinki? Rashin nutsuwa? Ko rashin kuɗi? Ko kuwa dan mijinki baya yabawa idan kinyi?*

*Toh ƴar uwa ki share hawayenki, domin STYLISH BCH special care Sun tanadar muku da kayan gyaran jiki dana gidajen ku. Ki gyara jikin ki ƴar uwa kodan ke kanki ba sai dan miji ba. Ki gyara sama da ƙasa yadda zaki san kedin macece domin mace sai da gyara take cika asalin mace. Ƴar uwa karki ta zubin adashin da babu riba, ki fito da kuɗi ki gyara jikinki kamar yadda isassun mata suke yi. Muna sai da supplements kala-kala kamar na:-*

Gyaran Nono su ciko su tsaya suyi kyau.
Gyaran HQ zai matse ki jiki cif-cif.
Maganin warin HQ. Ya sa gurin yin kamshi.
Maganin karin ni'ima, ki dena jinki a kafe.
Maganin taushi, laushi da santsin HQ.
Maganin infections kala-kala.
Maganin saka ƙiba, ji ciko kiyi bul-bul.
Maganin Basir.
Arabs Parfums.

*Kina son ganinki kamar tarwaɗa? Yes ina nufin kiji jikinki lukum saboda tsabar taushin fata? Maza garzayo STYLISH BCH special care. Anan za a huce miki takaici, a dawo miki da mutunci da martabarki kamar yadda sauran mata suke da ita. Ƴar uwa matso ki gyara jikinki, ki tara taro da sisi ki yi gyaran jiki. Mace ƴar kwalliya ce! Ƴar kwaskwas! Ƴar kyal-kyal ba wai ballagaza ba.*

*Karku manta da inda zaku samu kayan gyaran jikin ku, idan kun manta bari na tuna muku. STYLISH BCH special care. garin Kano muna aika kayan mu a duk inda ake bukata. A tuntuɓe mu akan lambar wayar nan 08164457511 mun gode.*

*SAWUN GIWA....*🐫🐘
(Badda na raƙumi)

Page 18
(Na bati ne) 💃

Alhamdulillahi su Jasmine sunje Adamawa sunyi biki lafiya lau an tashi lafiya. Sai dai ba ta sani ba sai da Ahsan ya turo security da suka kula masa da ita tun daga garin Abuja, Allah yaso ba tayi wani abun da zai janyo masa kishi ba bare aje a sanar dashi. Duk Wani abu da yake yi baya mantawa da ita, duk seconds tana harbawa cikin zuciyarshi saboda soyayyar da yake yi mata. Har kagara ya yi ta koma US saboda sunfi haɗuwa a can ba kamar suna Nijeriya ba da yake shan tsaro tamkar shine shugaban ƙasar.

Kamar yadda suka saba yau ma kamar kullum ya kirata ta ɗauka tare da karawa a kunne, kusan a rare suka yi sallama suka kuma amsawa juna kafin su saki murmushi, Ahsan dake zaune a wani gurin shaƙatawa dake cikin villa akan wata haɗaɗɗiyar kujera ta hutawa mai matuƙar kyau. Sanye yake cikin riga da wando na shan iska wanda suka amshi jikinsa sukai masa kyau, abinka da kyakkyawa daga indallah.

"Kika ce Ummi ba zata yadda ki zauna opposite gidan da nake ba?"

Jasmine ta lumshe ido tamkar tana gabansa. Kwance take akan luntsumeman gadonta, jikinta sanye cikin doguwar rigar bacci ja mai gajeren hannu. Cikin zazzaƙar muryarta mai sanyin daɗi tace masa.

"Ko da Ummi ba ta yi magana ba, ni bazan iya zama ba."

"Me kike tsoro?" Ya tambaya dan zuciyar shi ta fara wasiwasi.

"Babu komai." Ta bashi amsa.

"Uhmmm my love kenan, kunyar ki tana sake jan hankali a gareki. Allah dai ya nuna min ranar da zan kawo karshen ta." Da sauri Jasmine tace dashi cikin shagwaɓa.

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now