SAWUN GIWA Page 16 🐪🐘

117 20 1
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).
2021

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV.* https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE dan nuna soyayya a gare mu)*

_________
Assalamu alaikum
Hi sister's!

Shin yar'uwa kina fama da matsalan fatane?😯 Shin  kingwada products dayawa but gbdy basa aiki🥺toh hajiyata kisa ranki a inuwa domin *mg's skincare* suntanadar mk Kaya masu matukar anfani da gyarajiki fiye da tunaninki batare da sunyima fatar jiki illa ba domin dukanin kayansu organic ne Wanda akayisu da ingantattun natural abubuwa Wanda zaigyaramuku jiki yayi clearing dukkanin prblms na skin kamar Pimples, Black spot, Black head, sunburn,glass, wrinkles, knuckles,acne, eczema, stretch mark,dama dukkan wani matsala na jiki Yana maganin tattarewan fata hatta wadanda suka shafa cream  yabata musu jiki toh *mg's skincare* gat you covered🤭 wani abunma shine akwai hadadden soap Wanda Koda bakida komai Zaki iya using zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural beauty dinki living the skin fresh, smooth nd glow like never before😬munada soap wnd inmutum naso yadanyi haske akwai Kuma Wanda zaiyi maintaining skin😍Kuma munada complete set gbdy nagyaranjiki😘 inafadimuku karku Bari ayi babuku bama cika Baki wnd yagwada shizai karas🤗 just gv it a try nd ur skin will definitely/forever thank you❤️
Soap price:3k
Set:11k
Munatura Kaya kowani gari buh delivery is not free

Chat:08062991549
Call:08064532391

Hurry nd grb urs
Team glow🧖‍♀️

*SAWUN GIWA....*🐫🐘
(Badda na raƙumi)

Page 16
(Na bati ne).

"Girmanta ne ai, Yaya yi tafiyarka haushi take ji baka yi da ita."

"Lahhhh ni me zanyi dashi tsoho, ga miji na can me sabon jini." Cewar abokiyar wasan tasu tana tabe baki.

"Hahaha tsoho dai, magana kikai a baibai kika cewa mijin ki tsoho Yaya Ahsan kuma sabo mai sabon jiji."

Shi kam tunda ya samu Afreen ta karɓe maganar sai ya ƙarasa wajan Mamie yana yi mata sallama, tayi masa fatan alkairi tare da sanar dashi cewa zasu je Dubai ne hado kayan auran Anas ɗan gidan uncle ɗin su. Duk suka taho aka rako shi har inda zasu shiga jirgi, dama shida su Christopher ne da wasu yaran ƙusoshin ƙasar su shida suka tafi.

Tun a cikin jirgi yake jin wani iri a ransa, zuciyar shi gabaki ɗaya ta kagu ta ganta tare da Jasmine, ya gama sanin cewa rayuwarsa sai da ita take yiwuwa cikin jin daɗi, ko ya ya idan basu tare da ita sai ya dinga jinsa tamkar wani rabin mutum.

*KANO STATE.*
MASARAUTAR ZUNNURAIN.....

Tun da aka sanar cewar ɗan shugaban ƙasa zai zo aka fara shirin tarbarsa ta hanyar gyare-gyaren masarautar. Mai martaba yasa ana ta shiri kai kace president ɗin aka ce zai zo saboda yadda ake shiri babu kama hannun yaro. Hankalin Haj. Alawiyya uwargidan sarki Uthman duk ta bi ta ruɗe ganin yadda ake shirin saukar surukin su. Sai yanzu take nadamar rashin haihuwar ƴa mace, duk a zaton ta tunda tafi kowa yara maza kuma nata sune manya tayi tunanin zatafi kowa ɗaukaka a cikin masarautar. Sai gashi Haj. Amina mai guda ɗaya kuma ma mace tana neman finsu komai a duniya, tunda gashi har an fara buga sunayanta a jaridu da kafafan yaɗa labarai.

Suna dira gwamna already ya tura a dakko su, Ahsan sai tsaro yake sha ana ta kare shi saboda kulawa daga ƴan adawa. Wani katafaran parlor aka sauke su shida su abokansa, an tsara gurin yadda ya kamata ga kayan cima kalakala na zamani dana gargajiya. Akan royal chairs ɗin dake parlorn Ahsan ya zabi ɗaya mai kallon kofar shigowa ya zauna, saboda jira kawai yake yaga gimbiyar tashi. Bayan sun huta ne muƙarraban cikin masarautar suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya suna gaishe sa, abin duk ya damesa ganin sunyi jika dashi amman ko wanne sai yaje har ƙasa yake gaidashi.

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now