SAWUN GIWA Page 8🐪🐘

112 21 3
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV.*https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)*

*SAWUN GIWA....*🐫🐘

Page 8
(Na bati ne) 💃

*STANFORD UNIVERSITY* 🎓

Itace ta fara faɗo masa cikin zuciyar sa, kenan can ya kamata ya fara zuwa ko Allah zai sa tana nan. Kasancewar basu da wata wahalar mota tuni an tanadar musu wadanda zasu yi amfani dasu tun kafin su ƙaraso ƙasar, ya fito ya shiga suka ja zuwa gurin Jasmine. Suna zuwa ya dinga waige-waigen inda zai hangeta ya rasa, gashi ba hotunanta gareshi ba bare ya nunawa ss ɗin su taya shi nemanta. Hankalinsa yayi kololuwar tashi duk ya duba inda yake tunanin zai ganta amman babu ko mai irin shigar ta.

Jiki babu kwari ya juya yana tafiya kamar ance ya waiga sai ya hangota sun ɓullo ita da su Fauza, nan da nan ya sauke wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya, ya fara tattaro nutsuwarsa ta yadda ba zasu gane ruɗanin da ya fita daga ciki ba a yanzu. Sam basu ganshi ba har sai da suka zo daf dashi sannan Jasmine ta kai idanunta gurin, karaf kuwa suka yi ido huɗu ko wanne ya fara motsi da baki alamar son yin magana.

"Lahhhh Ahsan! Daman kana ƙasar nan har yanzu?"

Ikram ta faɗa cike da murnar ganinsa, ya ɗan yi shiru yana son ta tuna sunan ta amma ya kasa, sai kawai yace.

"A'a na dawo ne."

"Ohhhh! Shi yasa, ai muna ta cigiyarka cikin school ɗin nan ko ba'a ban kake karatun ba?"

"Yeah." Kawai yace da ita yaci gaba da kallon Jasmine.

Fauza ce taja sauran suka bar Jasmine dan taga kamar akwai sanayya a tsakanin Ahsan ɗin da ƙawar tasu. Kamar dama jira yake su bar gurin ya dan gyara tsayuwarsa yana matsawa kusa da ita, sai da yaje dap kamar zai haɗe su guri ɗaya har ta zaro ido sai kuna taga ya tsaya.

"Kinsan gurinki na zo, amman me yasa idan kika ganni bakya nuna cewa na zo dan mu gana dake ne?"

Ta kawar da fuskarta gefe tana turo baki, duk da cewar baya ganin duka fuskar har bakin yasan ta canza daga lokacin da ya ganta dasu Ikram.

"Ni ai baka taɓa ce min dan ni kake shigowa school ɗin nan ba."

"Yanzu fa?"

"Har yanzu baka sanar dani ba kawai labari kake bani."

"Toh naji, daga yanzu idan kin ganni a duk gurin da kike, na zo ne dan na ganki muyi hira."

"Idan kuma ina aiki fa?"

"Sai ki barshi kizo kiji dani."

Ta ɗago da sauri tana kallonsa, yadda taga ya kuma yin kyau shine yasa tayi saurin yin ƙasa da kai tace.

"Saboda mene?"

"Yanzu dai ki samo mana gurin zama muyi maganar, ko kina sauri ne?"

Ta dan yi shiru tana tunani, babu wani sauri da take yi dan gurin shaƙatawa ma zasu je sai kuma ta ganshi, kuma wannan shine damar da zata samu taji irin alaƙar da yake son su ƙulla, idan ba ta bashi dama ba zai iya kufce mata kamar yadda tai ta wahala gurin nemansa bayan ta dawo daga gida. Tafiya ta fara yi ba ta ce masa komai ba, shima ya bita suka jera gwanin ban sha'awa dan sun matuƙar dacewa da juna. Gurin wata rumfa ta kai su mai ɗauke da kujeru a ciki suka zauna Ahsan sai faman kallonta yake yi har sai da ta gaji tace.

"Wai baka gajiya da kallon mutane?" Ya shafa haɓarsa tare da cewa.

"Bana iya kallon mutane kamar yadda nake samun kai na da yawan son kallanki, shin ko zaki iya gaya min dalili?"

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now