SAWUN GIWA Page 9🐪🐘

106 19 4
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV. *https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)*

*SAWUN GIWA....*🐫🐘

Page 9
(Na bati ne)

Karimatu ce ta fito daga cikin ɗakin su tana gyara ɗaurin ɗankwalin kanta, Baban su dake zaune a bakin kofa riƙe da wata takarda sai faman juyata yake yi ta gaida shi ta wuce banɗaki, zuwan Ɗahiru gurinsa ne ya shiga yi masa bayanin Form ɗin yana cewa.

"Gashi nan da kyar na samu guda ɗayan nan wallahi, kaga idan ka samu ka shiga aikin ss ɗin nan ai ka rage min wani aikin da wannan zaman da kake yi na rashin abin yi."

Ɗahiru ya shiga sosa ƙeya shifa ga baki ɗaya baya san aikin takura, aiki ko wane iri ne ko nawa zai samu indai ba za a barshi ya wataya ba baya san shi. Jin shirun da yayi ne da kuma kin karɓar form ɗin yasa Baban su kuma yi masa magana.

"Karɓi kaje ka ciccike idan ka gama sai ka kawo min naje na kai musu, sai kaci gaba da addu'a Allah yasa a dace."

"Baba ss fa." Ɗahiru ya faɗa yana kumbura fuska.

"Au baka son ss ɗin?"

"Gaskiya Baba tsaurin su yayi yawa, kuma aje a kai ni inda zan kasa fitowa, da dai an canza min wani aiki."

Baki buɗe Baban su ya kalli Ɗahiru, can gefe Inna ta jiyo maganar, ai kuwa da sauri ta ɗago ta fara faɗa jin yaron yana neman janyo musu asara.

"Ashe baka da hankali Ɗahiru? Kasan da ya aka samu wannan form ɗin da zaka ce kai ba zakai irin aikin ba, wato kafi son kayi ta garari a cikin gari daga wannan inuwar ku koma wata ko? Toh baka isa ba sai kayi shi tunda kai ba nemarwa kanka wani aikin kake yi ba, sakarai shasha kawai."

"Idan ba zai yi ba Baba abani wallahi zanyi, ni aiki ko wane iri ne inda zai kawo kuɗi masu tsoka wallahi banga abinda zai sani cewa a'a ba."

Karimatu da ta fito daga banɗaki tana wanke hannu ta yi maganar cikin gaskiyarta, Umma ta na jiyowa ta fito da sauri dan tasan a yadda Karima ke neman kuɗi zata iya bada kanta ma ba neman aiki ba.

"Ana maganar maza kina mace kina cewa zaki yi, dallah wuce ki gyara min ɗaki sakarai kawai."

"Umma mata na yi fa." Karimatu ta kuma faɗa tana buɗe ido.

"Toh ba zaki yi ba, nace ba zaki yi ss ɗin ba."

"Allah ya baki hakuri."

Ta faɗa tare da shigewa cikin ɗaki, yau taga samu ta ga rashi bata san me yasa Umma take wannan abun ba, ga samuwa tazo amman wai ba zata bari ba.

Haushi da takaici suka cika ran Malam khamis ganin yadda Ɗahiru yaki karɓar aikin sa aka samo masa, ya ce ya tashi ya bashi guri, ya mike kamar munafuki yabar gidan yana ƙanƙani cewar indai aikin ss ne kawai yanzu a nigeria to ba zai yi ba gwara ya mutu a haka, shi babu wanda zai je yana wani tsarewa ya sanya kansa cikin hatsari su suna cikin a.c suna hutawa. Jiran Kamalu ya yi yana zuwa kuwa yace zai yi ya bashi form ɗin a gabansa ma ya cike inda be gane ba ya nuna masa har suka gama ya karbi form ɗin yasa cikin file ɗin da zai fita gobe. Karimatu kuwa ranar da kunci ta yini duk da cewa taji daɗi da Kamalu ya ce zai yi ko babu komai ɗan uwanta ya samu abin yi.

Ana cikin haka ne malam Khamis ya kuma zuwa da albishir gidan nasa, ya tara matansa ta sanar dasu cewa mata ake son ɗauka aiki a cikin jirgin sama, irin masu bada abinci da kula da passenger an bashi slot biyu wa suke ganin zai bawa su dan ana samun kuɗi sosai. Cikin sauri Umma tace sai dai ya kaiwa wasu ƙabilun dan sune aikin ya dace ba yaran su na musulmi ba, ya kalleta da murmushi tare da cewa.

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now