SAWUN GIWA Page 14 🐪🐘

100 21 0
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).
2021

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV.* https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)*

_____________

*Treat/repair your skin with mg's skincare today,are you battling with pimples, Black spot cream reaction eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg's skincare is the plug for you,mg's skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg's skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet's/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don't HV anything mg's skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰*
Soap price:3k
Chat 08062991549 to plc ur orders
Call:08064532391
*We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏 we can't wait to be a part of your beauty story🤭*

*SAWUN GIWA....*🐫🐘
(Badda na raƙumi)

Page 14
(Na bati ne) 💃

Gudun da ya ringa yi ne ya tayarwa da masu kula da shi hankali saboda be saba yin irin wannan tuƙin ba, duk iya ƙoƙarin su na son tsaida shi ta hanyar shiga gabansa abin yaci tura har sai da suka ƙarasa gida. Wani irin wrong parking yayi ya shige sashen sa da sauri, ɗaya daga cikin masu tsaron sa ne yaje ya gyara parking ɗin dan ko mukulli be cire ba haka ya bar motar. Yana shiga ciki komai tsab dashi ya rasa abinda zai yi karo dashi kawai yasa ƙafarsa ya dinga harbin kujerar dake gabansa, cike da ɓacin rai Safwan ya furzar da iska daga cikin bakinsa.

Wannan yarinyar dama yasan dole tayi rashin kunya dan ya saba ganin irin su, saboda tana taƙamar babanta wani ne a ƙasar shine har zata zo gabansa tana nema yin ramuwar kalaman da ya gaya mata? kai bama ramuwa ba ne gargaɗi take masa tamkar wata uwarsa. Sai ya yi maganinta ta yadda gobe ba zata kuma yiwa wani ba bare kuma shi kankin kansa. Yaushe ne lokacin da zai koya mata wannan ladabin? Tunda Kano zasu koma shi kuma zamansa yafi kamawa a garin Abuja ko Lagos be fiye zuwa kano ba saboda baya son yawan abinda uncle ɗin sa ke yi masa.

Gobe! shine abinda yazo masa cikin rai, amman kuma ta ya ya zasu haɗu goben? Shi dai ba zai je gidan su ba domin duk wulakancin da tayi masa shine ya janyowa kansa, amman da zai samu damar ganinta a waje sai ya fi kowa jin daɗin hakan yadda zai nuna mata yadda ake ladabi da biyayya tare da girmama na gaba. Sallamar da yaji daga bayansa besa shi juyawa ba dan ya dauki murya, ya nufi hanyar shiga bedroom yaji tana cewa.

"Yaya Safwan Gwaggo ce take kiranka."

Ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba, cikin zuciyarsa yana tunanin dalilin da yasa Gwaggo ke nemansa a wannan lokacin da yake cikin ɓacin rai. Kai tsaya ya nufi hanyar fita be yiwa Aneesah magana ba, tabi bayansa yadda yake tafiya kadai ya isa ya tafi da imanin duk wata mace mai isashiyar lafiya wace tasan kanta. Har cikin ɗakin Gwaggo ya shiga fuskarsa babu yabo babu fallasa, itama kallo ɗaya tayi masa tasan akwai ɓacin rai a tattare da shi.

"Zoka zauna kayi min banin abinda akai maka shalele." Safwan yaje ya zauna kusa da ita yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri.

"Wata yarinya ce." Ya faɗa cikin wata irin murya irin ta shagwaɓabbun yaran nan idan sun kawo kara.

"Kai....! Amman dai banji daɗin labarin ban ba, kai yanzu har ka tsaya mace ta ɓata maka rai? Tsaya ma ni ban san wace kala bace nake ta wannan zubar, shin budurwarka ce da zamu sha shagalin bikin ku.?"

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now