*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV. *https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)**SAWUN GIWA....*🐫🐘
Page 7
(Na bati ne)💃"Umma dan Allah kiyi haƙuri ni wallahi ba da wata manufa nai maganar ba."
"Karki raina min hankali Karimatu ni na haifeki ba kice kika haife ni ba bare ki ce zaki mai dani sha-sha-sha, kina can kina sakin baki har kina cewa Khalifa ba ajinki bane, uban waye ajin naki na cikin waya da baki san ɗan gidan uban waye shi ba ko kuwa waye ajin naki sakarai kawai."
"Inna ce fa ta fara yin zance shine n...."
"Rufe min baki ko na gaura miki mari yanzun nan, kin ɗauka bana jiyo ku tun farkon hirar taku? Ki gama ci kizo ki leƙa ko zaki samu yaro ya taro mana ruwan, a irin wannan gidan Allah yaga damar haifoki idan bakya so zaki iya canza mu gaki ga hanya nan."
Karimatu dai baki ya mutu dan taga alamar Umma ta ɗauki zafi, har ta kammala cin abincin ta fito da samirar Umma ba ta dena mita ba. Karimatu ta saka doguwar rigarta da ta dawo daga makaranta, tasa mayafin ta fita ƙofar gida ko Allah zai sa ta samu yaron da zai taro musu mai ruwa. Ta jima kafin ta samu almajiri yaje ya taro musu ta bashi naira ashirin lada, daga nan ta diba tayi wanka da sauran buƙatun ta, dare nayi ta tafi makarantar dare.
Bayan an taso a hanyarsu ta dawowa gida suka haɗu da Khalifa, tana hangensa ta saki murmushi cikin zuciyar ta tace 'Kamar gaske' a fili kuwa murmushin ne ya kawata fuskarta Khalifa na ta jin daɗi ya ɗauka har a ranta taji daɗin ganinsa. Yana karasowa kawayenta suka gaida shi suka yi gaba su kuma suka jera tare abin nasu very perfect sun dace matuƙa amman Karimatu tana son kwafsawa.
"Barka da dare my love, ya karatu?"
'Haka dai za ai ta tafi da kalaman baki dan akwai iya tsara zance gurin Khalifa na soyayya dana kwantar da hankali'
"Yauwa ya aikin.?"
"Lafiya lau my love, wucewa zanyi nace bari na tsaya mu gaisa."
"Ka kyauta kuwa kamar kasan daman nayi kewarka."
"Da gaske?" Ya tambaya cike da zunuɗi.
Rufe fuska tayi cike alamar jin kunyar abinda ta faɗa, ya kalli kawayenta da suka yi musu nisa gashi shi kuma wucewa zai yi ba zai iya karasawa har ƙofar gidan su ba. Ledar hannunsa ya mike mata taki karɓa duk kuwa da cewa tana so, tsoro take karta je ko yallo da ɗata ne dan gwani ne wajan kawo mata yace suna da amfani a jikin mutum.
"Dan Allah ki karɓa my love, naso na kai miki gida to kinga Kamal can yana jira na zamu je asibiti."
Hakanan ta karɓa tana sunne kai suka yi sallama ta tafi shima ya ƙarasa gurin Kamal suka wuce. Tana zuwa gida ta ajiye ledar tana tsaki saboda ta hango biredi, bata tsaya dubawa ba ta fito ta shiga bandaki bayan ta gayawa Umma cewa Kamal ne ya bata ledar. Hannatu ta janyo tare da zaro kayan ciki, taga biredi, l&Z sai ledar gasasshiyar kaza mai romo-romo da kabeji sai kamshi take yi.
"Umma kinga abinda ya kawo."
Umma dake kwance ta waigo ganin abubuwan yasa ta tashi zaune tana duddubawa, lallai Khalifa yana ƙoƙari gaskiya irin wannan hidima haka, gashi shine yake kula da gidan su tunda mahaifinsa ya rasu. Karimatu ta shigo ganin yadda aka baje ledar kaza yasa ta saurin zama a gurin tana cewa.
"Hanne Baba ya dawo ne?"
"A'a me kika gani?"
"Naga kaza, ko Yaya Habu ne ya dawo?"
YOU ARE READING
SAWUN GIWA... 🐘🐫
RomanceLabarin wata matashiyar yarinya yar sarki da ta kasance shalele, sai dai kaddara ta gilma mata wacce ta sanya ta cikin.....