*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV. *https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)**SAWUN GIWA....*🐫🐘
Page 6
(Na bati ne) 💃*ABUJA NIJERIYA*
Aso rock presidential villa.Ƙawataccen guri ne da aka keɓance a cikin fadar shugaban ƙasar Nijeriya, guri ne daya amsa sunansa guri inda ko wane babba mai ji da kansa a faɗin Nijeriya yake son shiga ciki, idan aka ce masu ji da kai ana nufin waɗanda suka kama ƙasa a hannunsu suka yi mata matsar wanki. Guri ne da talaka ba lallai ko an masa bayanin yadda yake ya gane ba, saboda ko a cikin unguwar su bai zama lallai ya taɓa shiga gidan chairman ba balle yaga wasu abubuwan na more rayuwa. Aso rock presidential villa a nan ne office ɗin shugaban ƙasa yake wato ƙarshen mulki, ofishi mafi ƙololuwa a faɗin Nijeriya.
Alhaji Bilal Bello Bakorindo zaune a cikin katafaran office ɗinsa wanda baki ko alƙalami ba zai iya rubutawa irin tsaruwarsa ba, amman kai mai karatu ka ƙawata abinka yadda yazo maka a cikin ranka. Saƙon saukar bakin da zai yi ne ya isa gareshi, ya ajiye biron hannunsa tare da tasowa ya baro gurin tebur ɗin sa, fuskarsa cike da murmushi yake kallon ƙofar shigowa.
Suna shigowa president Bilal ya nufi gurin Alhaji Bukar Sani Sa'eed (BSS) suka runguma juna cike da farin cikin haɗuwarsu, babban ɗan kasuwa ne, lamba ɗaya a nahiyar Africa da yake da kamfanoni daban-daban cikin ƙasar sa da wajan ta. Suka ƙarasa gurin tebur ɗin baƙi suka zauna wanda aka jera kayan kwalam da makulashe, akwai amana da soyayya mai ƙarfi a tsakanin su, president Bilal ya so bawa Alhaji Bukar ministan mai amman yaki karɓa saboda baya son haɗa harkokinsa da siyasa azo ana zaginsa koda baya cin kuɗin gwamnati, mutane ba zasu yadda ba zasu ce ai kuɗin sune idan suka ga yana wadaƙa da kuɗaɗe.
Tattaunawa suka yi akan yadda za'a dinga sarrafa shinkafa da yadda za'a siyarwa wasu guraran akan farashin da ba zai takurawa mutane ba. Alhaji Bukar ya yi alƙawarin sassauci ga duk wani dila na shinkafa da sukari harma da macaroni da taliyar da suke sarrafawa ta BSS. Cikin farin ciki suka yi sallama Alhaji Bukar ya tafi shi kuma president Bilal ya koma kan kujerar mulki ya zauna yana ta faman tunanin wata hanyar da zai sake bullo da ita yadda talaka zai ci gajiyar mulkinsa.
Sanar dashi aka kuma yi cewar su first lady sun sauka, ya tashi da sauri ya fito ss suka raka shi ɓangaren da su Hajiya Halimatu Bakorindo suke. Yana shiga ya tarar ana ta murnar dawowar su musamman ma Ahsan da kowa shi yake runguma ganin ya warke yayi ras dashi tamkar wani sabon haihuwa, Alhaji Bilal shima yaje suka rungume juna tsawon lokaci
"Alhamdulillahi! Yaro na ya dawo gare ni." Ya faɗa yana shafar bayansa tare da jansa suka shiga ciki.
Kafin kace menene tuni zance ya cika lungu da saƙo a ƙasar Nijeriya cewar Ahsan ya dawo cikin koshin lafiya, nan da nan talakawa da ƴan adawa suka hau surutu cewa. Dama dole ya warke tunda an kai shi lafiyayyan asibiti, su kuwa suna nan sai fama suke da cutar maleria, asibiti ba magani ko kaje ai tayi maka rashin mutunci ana neman zaginka sai kace kai ka ɗorawa kanka ciwo da talaucin. Su kam basu san ana yi ba ana can sai murna ake yi harda yanka cake. Shi dai Ahsan ba abinda yake yi sai murmushi hankalinsa gabaki ɗaya yana US, yasan Jasmine tana can gashi ya baro ta ba tare da ya karbi lambar wayarta ba, saukin sa ɗaya yana da ta Layla zai dinga jin bayananta daga gurinta.
Ɗakinsa ya shiga wanda iya tsaruwa ya tsaru babu algus, ya wuce bathroom ya tari ruwa cikin wani haɗadɗan kwami, fitowa ya yi tare da cire kayan jikinsa ya daura towel tare da komawa cikin banɗakin, ruwan ya shiga tare da kwanciya a ciki ya lumshe ido.
YOU ARE READING
SAWUN GIWA... 🐘🐫
RomanceLabarin wata matashiyar yarinya yar sarki da ta kasance shalele, sai dai kaddara ta gilma mata wacce ta sanya ta cikin.....