SAWUN GIWA Page 4🐫🐘

230 28 10
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: STYLISH TV https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a danna mana SUBSCRIBE)*

*SAWUN GIWA....*🐫🐘

Page 4
(Na bati ne)

"Ya Allah." Bashi da wani ƙwarin gwiwa banda na ambaton Allah, shine kawai zai iya warware masa kullin da yake jin anyi masa a cikin zuciyar shi.

Har aka maida shi ɗaki bai buɗe idanunsa ba sakamakon hoton ta da ya ɗauka a cikin kewayar idanuwansa, baya son kuma ya goge saboda baya gajiya da ganin tsarin halittar da Allah ya zana mata na sura. Shin wacece wannan yarinyar? Ƴar gidan waye? Menene matsayin babanta a ƙasar su ta Nijeriya? Yana son ya sani kodan yaga ta ina zai fara mu'amala da ita.

"Assalamu alaikum Ahsan." Dr Layla tayi masa sallama bayan ta shigo ɗakin.

Ya buɗe ido a hankali, tun sanda ya dawo cikin hayyacinsa Mami ta gaya masa wacece Layla da irin taimakon da ta basu akan rashin lafiyarsa, uwa uba reletionship ɗin ta da Jasmine. Ta sakar masa murmushi tana zuƙo ruwan allura a cikin sirinji tace dashi.

"Ya kake jin jikin?" Kamar wanda aka matsewa baki, a hankali yace.

"Da sauki Doctor."

"Good bari na yi maka allurarka sai ka kwanta kayi bacci."

Kallonta kawai yake yi yana son yi mata tambaya akan Jasmine amman ya yi shiru, saboda mutum ne shi da bai fiye shisshigi ba cikin ko wane al'amari. Har ta gama yi masa ta gyara gurin tare da taimaka masa ya kwanta be yi magana ba, sai da yaga ta juya zata tafi ya kuma san a gurinta ne kawai zai ji labarin Jasmine, ya daure yace mata.

"Wai ina sister ɗinki da aka ce ta taimaka min? Har yanzu ban ganta ba kuma ina son yi mata godiya."

Layla ta dafe goshi lokacin da ta gano cewa Jasmine yake nufi, kuma suna can office ɗinta amman bata jin zata yarda tazo gurinsa dan tace ta gama abinda zata yi na taimakawa. Kallonsa tayi a ɗan zaman da suka yi taga bashi da wata matsala kuma bashi da alfahari na cewa shi ɗan shugaban ƙasa ne bare ya dinga wulakanci ko rashin mutunci irin na wasu ƴaƴan masu farcen susan.

"Bana jin Jasmine zata zo gurin nan gaskiya." Ahsan ya kalli Layla da sauri cike da mamaki.

Ta kuwa san ko shi waye da za a ce tazo amman taki? Ita ɗin kasan ko ƴar gidan waye da zaka ce haka? Zuciyar sa ta dinga masa wannan tambayar wacce babu mai amsa masa ita face ya tambaya.

"Wacece ita?" Yayi tambayar ba tare da yasan a fili ya yi ba.

Layla ta kuma kallonsa ita kanta tana da tambayoyi akan sa, tana son sanin menene ainahin alaƙarsa da ƴar uwar ta da har sai da aka nemo ta sannan ya samu waraka daga kwanciyar da ya yi.

"Jasmine ƴa ce ga sarkin Kano his royal highness Uthman bin Ibrahim (Sarki Zunnuran) ta kasance ƴa mace ƙwarya ɗaya daya haifa sauran duk maza ne, ina jin idan na bar shi haka zaka fahimta."

Kirjinsa ne yai wani irin bugawa wanda ya yi sanadin da yasa shi rintsa ido, shikenan domin yasan ko zai haɗiyi wuta da wahala ya samu kusanci a gurin ta sakamakon izzar da yasan suna da ita. Akwai wata zazzafar izza da yasan zuriyar sarki Zunnuran na da ita, wacce kowa ya sani dan a bayyane take. Shi kuwa mai ya haɗa zuciyarsa da ƴar gidan saraita? Shin wace irin alaƙa zuciyar shi take son su kulla tsakanin ta da yarinyar da bata ma san halin da zuciyar tashi take ciki ba?

"A huta lafiya."

Muryar Dr Layla ta katse masa tunanin da ya shiga.

Buɗe idanunsa yai yana bin ta da kallo harta fita daga cikin ɗakin, yasa hannunsa biyu yana bugun goshinsa dai dai lokacin Mami ta shigo s.s ɗin ta na biye da ita ɗauke da wani kyakkyawan kwando, ɗayan kuma yana riƙe da wasu ledoji manya. Ganin yadda yake bugun kansa yasa tayi saurin yarda jaka ta nufe shi tare da riƙo hannuwan.

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now