SAWUN GIWA Page 20🐪🐘

167 20 5
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).
2021

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV.* https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)*

*TALLA..! TALLA...!! TALLA..!!!*
*ASSALAMU ALAIKUM....*
*Mace sai da gyara ƴar uwa.*
SHIN KO KUN SAN..... 👇

*JEEDATY Beauty spa ya kawo muku kayan gyaran jiki masu kyau da INGANCI?. Ina Amarya da uwar gida? Toh ga kayan JEEDATY beauty spa sun kawo muku, _shower gel_ domin gyaran fata kiyi wanka fatarki tayi kyau da shek'i, akwai _lotion_ na shafawa domin kowacce fata tana glowing skin ga _oil,face cream, scrub_ duk domin gyaran fuska suna gyara ta su ɗauke dark spots pimples, sunburn da dai wasu kaikayin fuska. Sanyi yazo! Duk da haka bata barku haka ba sai da tayi muku mai na kitson na Jeddaty hair cream, domin gyaran gashi. Ba anan ta tsaya ba, A JEEDATY harda mayafai tsala-tsala, laces, khumra masu daɗi da sanya nutsuwa. JEEDATY ta tanadar muku da abubuwan ƙawata jiki, dan haka domin karin bayani zaku nemata a*

*IG @jeedaty Beauty spa*
WhatsApp and call @ 08147491137
sai naji ku mata ƴan kwalisa. Karku manta da cewa sai an gwada akan san na kwarai....

*SAWUN GIWA....*🐫🐘
(Badda na raƙumi)

Page 20
(Na bati ne)

Tunda ya bar asibitin be dawo ba sai washe gari, ya shigo cikin kasaita da jan aji ga masu tsaronsa a baya cikin suit bakake. Shi kuma sanye yake cikin wata orange ɗin shadda, dinkin da akai masa ya dace da jikin nashi dan ba karamin kyau tayi masa. Kai tsaye Safwan ya wuce ɗakin da aka kwantar da Saif, amman abin daure kai shi ne babu kowa a ciki. Sai ya fito tare da ƙarasawa reception ya tambaye su, nan suka sanar da shi cewa an sauya masa asibiti.

Mamaki ya kama Safwan sosai. Ya akai har aka sauya masa asibiti amman babu wanda ya gaya masa? Waye ya yi masa wannan abun? Dan san sanin amsar tambayarsa yasa shi kuma juyawa ya tambayi ma'aikatan wajan su bashi list ɗin su zai duba. Babu ɓata lokaci suka bashi ya shiga dubawa cikin raba idanuwa. 'President of Nigeria' Sing ɗin da ya gani kenan. Ya kuma duba gaban sunan inda yaga bama asibiti kadai aka canza ba, harda ƙasar, ma'ana sun ɗauke shi kacokam an maida shi India.

Iskar cikin bakinsa da ta taru ita ya furzar tare da shafar kwantaccen gashin daya zagaye bakinsa. Ya fito daga cikin asibitin zuciyar shi a cinkushe yama rasa wace irin mafita zai samarwa kansa. Kodai ya yi tafiyarsa gida Nijeriya tunda an fara nuna masa iyakarsa akan aminin nashi? Amman fa idan ya tafi ma hankalinsa ba kwanciya zai yi ba na rashin sanin ainahin halin da Saif yake ciki.

"Ya Allah." Ya furta cike da jin wani irin zugi a kansa.

"Ayi mana booking ɗin jirgi zuwa India." Safwan ya bawa ɗaya daga cikin masu kula dashi umarni.

"An gama ranka ya daɗe." Cewar mutum yana juyawa ya tari mai taxi.

Shi kuma Safwan ya shiga mota suka koma hotel ɗin da suka sauka. Kayansa ya ɗauka suka tafi Airport ɗin yana ta sake saken yadda zai yi idan yaje Indian, dan sai ya nuna musu ɓacin ransa akan wannan wulakancin da sukai masa.

*INDIA...🇮🇳.*

New Delhi Jasmine ce suka fito daga wani rantsattsan gurin cin abinci, bayan su kuma masu kula dasu ne riƙe da manyan ledoji suna kokarin tsallaka titi. Suna zuwa tsakiya wata mota da tazo gab dasu kamar zata buge su yayi saurin damƙo mata hannu. Ita kanta bata yi tsammanin ta tsira da rayuwarta ba, sai da suka gama tsallakewa taji ana gyara mata gefen vail daya rufe mata fuska.

Ta ɗan buɗe ido kaɗan da nufin ganin a ina take, duniya ko lahira? Sai ta ganta jikin Ahsan yana shirin zare hannunsa daga rikon da tayi masa mai cike da karfi.

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now