*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g*ASSALAMU ALAIKUM....*
*Mace sai da gyara ƴar uwa.*
SHIN KO KUN SAN..... 👇*JEEDATY Beauty spa ya kawo muku kayan gyaran jiki masu kyau da inganci. Ina Amarya da uwar gida? Toh ga kayan jeedaty beauty spa sun kawo muku, _shower gel_ domin gyaran fata kiyi wanka fatarki tayi kyau da shek'i, akwai _lotion_ na shafawa domin kowacce fata tana glowing skin ga _oil,face cream, scrub_ duk domin gyaran fuska suna gyara ta su ɗauke dark spots pimples, sunburn da dai wasu kaikayin fuska. Sanyi yazo! Duk da haka bata barku haka ba sai da tayi muku mai na kitson na Jeddaty hair cream, domin gyaran gashi. Ba anan ta tsaya ba, A JEEDATY harda mayafai tsala-tsala, laces, khumra masu daɗi da sanya nutsuwa. JEEDATY ta tanadar muku da abubuwan ƙawata jiki, dan haka domin karin bayani zaku nemata a*
*IG @jeedaty Beauty spa*
WhatsApp and call @ 08147491137
sai naji ku mata ƴan kwalisa. Karku manta da cewa sai an gwada akan san na kwarai....*SAWUN GIWA....*🐫🐘
Page 19
Besan ma tana yin kukan ba kasan cewar ba wani sauti gareshi ba, ya samu kansa da waigowa ne kawai dan ganin meke faruwa sai ya hangota cikin Ummi wacce ke faman bubbuga bayanta. Karaf suka haɗa ido dashi ya yi saurin kawar da kai tare da yin ɗan jim daga bisani kuma ya fara takawa a hankali har ya isa inda suke a tsaye. Cike da ladabi da biyayya ya gaishe da Ummi, ita kuma ta kasa kin amsawa saboda tasan saboda Saif yake gurin nan, ta saki fuska sosai suka gaisa tare da yi masa godiyar zirga-zirgar da yake akan lalurar Saif.
"Babu komai ni dashi duk ɗaya ne."
Safwan ya faɗa yana kallon bayan Jasmine dan har lokacin bata dago kanta ba kuka kawai take yi.
"Me akai mata ne?" Ya tambaya kamar be san komai ba.
"Rigima ce irin ta Jasmine, ni kai na bazan ce ka abinda ya sata wannan kukan ba." Cewar Ummi tana sake shafa bayanta.
"Kanwata zo ki sanar dani matsalarki, ki dena kuka dan idan Saif ya farka yaga na barki kina zubar da hawaye zai ji babu daɗi."
Mamaki ne ya kama Jasmine jin yadda yake magana da Ummi cikin nutsuwa kuma tamkar besan abinda ya sata kuka ba. Ji tayi Ummi na cewa da ita.
"Jasmine Yayanki yana magana, ki sanar dashi abinda ya saki kuka."
Ta dago kanta ba ta kallesa ba ta juya zata bar gurin taji ya sha gabanta wanda hakan yasa ta tsayawa cak haushi kamar ta haɗiye zuciyarta. Me zai ce mata bayan shi ɗin ɗan rainin hankali ne? Koda yake ba ita ya rainawa hankalin ba sai kanshi tunda bashi da aikin yi sai shisshigi da shiga abinda ba damuwarsa ba. Wayar ta ce ta shiga ruri cikin wani sauti mai kwantar da zuciya. Ta duba sunan taga Ahsan ne hakan yasa ta ɗan ji zuciyarta ta fara sakkowa daga cikin bakin cikin Safwan dake tsaye a gurin.
Murya a sanyaye bayan ta ɗan matsa daga gurin shi ta fara yiwa Ahsan magana cike da kulawa.
"OH! Sorry ɗazu ne bani cikin nutsuwa.... A'a wallahi ba wulakanci nayi maka ba, Ummi ce ta sanar min an sassari brother Saif na shirya mu tafi, shi yasa duk na gigice... Amman dai karkai fushi."
Safwan naji ya ɗan kalli inda Ummi take yaga ta tafi, hakan ya bashi damar yiwa securities ɗin gurin alama da subar gurin. Gabaki ɗaya suka ɓace kamar walkiya, shi kuma ya ƙarasa har inda Jasmine ɗin take tsaye, babu zato taji ya zare wayar daga hannunta ya kara a kunnansa. Za tayi magana yai saurin juya mata baya yana ɗan tafiya a hankali tare da cewa.
YOU ARE READING
SAWUN GIWA... 🐘🐫
RomanceLabarin wata matashiyar yarinya yar sarki da ta kasance shalele, sai dai kaddara ta gilma mata wacce ta sanya ta cikin.....