*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).
2021®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV.* https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)**SAWUN GIWA....*🐫🐘
(Badda na raƙumi)Page 22
(Na bati ne)Hasheem na shiga da Karimatu ya fito ya barta a ciki ya tafi office ɗinsa, ta tsaya daga inda take ganin gogan ko ɗagowa beyi ba hakan yasa jikinta yin sanyi da kuma fargabar yadda zai karɓeta. Ya ɗan ɗago da idanunsa daga kan system ɗin da yake dannawa ya zubawa Karimatu idanu alamar yana son ya tuna inda ya san fuskar. Kasa ganowa yayi dan baya tsammanin ma ya taɓa ganinta a rayuwarsa saboda shi ba wani hudɗa ce ke haɗa shi da mace ba.
"Bismillah." Yai magana yana nuna mata kujera.
Karimatu ta ƙarasa a yangance ta zauna tare da ɗora handbag ɗin ta saman table ɗin shi. Itama sai da ta ja aji kafin ta kalleshi ta gaida shi.
"Ina yini?" Safwan ya tuge farin glasses ɗin idanunsa ya daga kai kawai.
"Kika ce nace kizo?" Karimatu ta saki murmushi tare da karya wuya tana kallansa tace.
"Kwarai ma kuwa, nasan daman za'ai haka cewar zaka manta ni tunda kuna harka da mutane da yawa. Mun hadu a jirgi har kayi mana hotuna wanda naga kayi posting ɗin su a Instagram page ɗinka, kuma ka bani kati gashi kace zamu hadu a nan idan ina da bukatar haka. Na daɗe a garin nan saboda kai, ance baka nan shine Alhaji Hasheem ya taimaka min har zuwa yau da Allah yayi zamu hadu da kai."
Tunda ta fara magana be dena danna-dannensa ba, yana dai jin harta gama magana sannan yace.
"Allah sarki, yanzu to me kike da bukata a guri na.?"
Karimatu tayi shiru ta rasa abinda zata ce masa, wata shegiyar kunya ce ta rufe taji ba zata iya cewa ya so ta ba, gani take kamar ta zubar da daraja da mutuncinta na ƴar musulmin bahaushe. Shi kuma ganin taki yin magana sai faman toshe baki take yi yasa shi juya kujera yaci gaba da aikinsa. Sai da Karimatu taga ba kuma yi mata magana zai yi ba sannan ta gyara zama tace masa cikin sanyin murya.
"Kamar yadda nake da buri, kuma nake mafarkin son ganin nayi aiki tare da kamfanin ku. Ina son ka cika min wannan burin nawa, ko babu komai zanyi alfahari da kasancewa ta cikin ku. Karka duba cewar ni macace, ko kayi min kallon mutuniyar banza. Ɗabi'unka da karamcinka sune suka ƙwaɗaita min son kasancewa ƙarƙashin ikon ka. Ina fatan zan samu karbuwa a cikin wannan kamfanin koda kuwa na aikin shara ko goge-goge."
Magana take yi da zuciya kai tsaye zuwa gurin wanda ake bukatar ya saurara.
Cikin ranta banda addu'o'in samun nasara babu abinda take yi. Tasan idan har ta rasa wannan damar toh fa babu inda zata kuma haduwa da Safwan, gashi ta ajiye aikinta da mahaifinta ya samar musu duk saboda tazo ta kasan ce tare dashi. Ya daɗe be ɗago ba bare ya bata amsa, har sai da ya gama danne-dannensa tukunna ya ɗago yana kare mata kallo. Yadda taga yana yi mata wani kaskantaccen kallo shine ya kuma karyar mata da guiwa, ta samu kanta da rintsa ido bugun zuciyarta na sake tsananta.
"Gaskiya bana jin muna da buƙatar kuma ɗaukar ma'aikaci a wannan kamfani, amman reshan mu dake kano muna saka ran ɗaukar sabbin ma'aikata, sai ki kasa kunne duk lokacin da kikaji ana sanarwa kiyi hanzarin nema kafin shima a rufe ɗauka."
Gabaki ɗaya hankalin Karimatu ya tashi, ita da take son kasan cewa kusa dashi ta ya zata yarda da zuwa wata ma'aikatar wacce baya zama cikin ta? Bafa aikin take so ba, shi take muradin gani taya zai yi mata haka ta hanyar nesanta ta dashi? Ta kuma kallan sa, a lokacin shima ya dago suka yi ido huɗu. Kallanta yake irin na ba yabo babu fallasa, shi sam beji tayi masa a tsarin da zai ɗauketa wani aiki ba. Ya juya kujerarsa wajan wata yar loka dake gefensa, ya zaro bandir ɗin kuɗi ƴan ɗari biyar-biyar ya kuma murza kujerar ta dawo dashi inda yake. Direwa Karimatu kuɗin yayi ba tare da ya kalleta ba yace.
YOU ARE READING
SAWUN GIWA... 🐘🐫
RomansaLabarin wata matashiyar yarinya yar sarki da ta kasance shalele, sai dai kaddara ta gilma mata wacce ta sanya ta cikin.....