SAWUN GIWA Page 12🐪🐘

130 17 4
                                    

*©️HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
(Home of expert and perfect writers).
2021

®️Hajja ce👈
Wattpad... @Hajjac.
YouTube: *STYLISH TV.* https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g
*(Ƴan uwa a shiga a yi mana SUBSCRIBE)*

________________

Assalamu alaikum
Hi sister's...
*Shin yar'uwa kina fama da matsalan fatane?😯Shin kingwada products dayawa but gbdy basa aiki🥺toh Hajiyata kisa ranki a inuwa domin MG'S skincare sun tanadar mk Kaya masu matukar anfani da gyara jiki fiye da tunaninki batare da sunyima fatar jiki illa ba, domin dukanin kayansu organic ne Wanda akayisu da ingantattun natural abubuwa Wanda zaigyaramuku jiki yayi clearing dukkanin prblms na skin kamar Pimples, Black spot, Black head, sunburn,glass, wrinkles, knuckles,acne, eczema, stretch mark,dama dukkan wani matsala na jiki Yana maganin tattarewan fata hatta wadanda suka shafa cream  yabata musu jiki toh MG'S skincare gat you covered🤭 wani abunma shine akwai hadadden soap Wanda Koda bakida komai Zaki iya using zai gyara miki jikine ya fiddo miki da ainihin natural beauty dinki living the skin fresh, smooth nd glow like never before😬munada soap wnd inmutum naso yadanyi haske akwai Kuma Wanda zaiyi maintaining skin😍Kuma munada complete set gbdy nagyaranjiki😘 Ina faɗa muku karku Bari ayi babu ku bama cika Baki wnd yagwada shizai karas🤗 just gv it a try nd ur skin will definitely/forever thank you❤️*

Soap price:3k
Set:11k
Munatura Kaya kowani gari buh delivery is not free

Chat:08062991549
Call:08064532391

Hurry nd grb urs
Team glow🧖‍♀️
_______________

*SAWUN GIWA....*🐫🐘
(Badda na raƙumi)

Page 12
(Na bati ne) 💃

Kafin ya yi wani abu kira ya shigo wayar, yana dubawa yaga mai kiran sai ya mik'awa Saif dan da ba dan wanda ya kira mai muhimmanci bane da katsewa zai yi ya ci gaba da abinda yake yi. Saif ya kara wayar a kunne yana gaishe shi, suna gama gaisawa da yake Saif yana ɗaya daga cikin yaran mai martaba da baya iya ɓoye musu komai saboda yadda suke son duk wani abinda yake so, kuma Saif mutumin Jasmine ne yana son ta fiye da kowane ɗa dake cikin masarautar.

"Kana ina ne?"

"Ina gida Abba."

"Gamu nan zuwa Abuja nida Ummy, ina son mu hadu da kai a can villa."

"Villa Abba? Shiga ta ciki zai bani wahala me za a yi?"

"Jasmine na can gurin su tun jiya, kasan tare suka taho da yaron da zata aura."

"Subahanallahi Jasmine tana cikin villa?"

"Kayi ƙoƙari mu hadu a can."

"Toh Abba Insha Allahu bari na shirya Allah ya kawoku lafiya."

"Amin Saifullahi."

Daga haka suka sauke wayar, mamaki tsantsa yana yawo a fuskar Saif kafin yaja tsaki ya mike tsaya yana kallon abokin nasa yace.

"Mai martaba yace naje zamu haɗu dashi a can villa."

Nan da nan Safwan ya sake tsuke fuska, daman tun lokacin da yaji Saif yana waya yana ambato Villa ya fara haɗe rai. Cikin yi masa kallon banza Safwan ya ce dashi.

"Me zaka yi a wannan gurin?"

"Jasmine na can bata da lafiya, abin tambayar a guri na shine me yasa tabi saurayi?"

Safwan ya yi shiru be yi magana ba har Saif ya shiga ciki, yana zaune yana ta mamaki tare da sake-sake har Saif ya fito cikin shirinsa suka fito fito a tare.

"Shikenan ma haɗu gobe." Saif ya faɗa yana miƙawa Safwan hannu alamun sallama.

"Muje can ɗin tare."

SAWUN GIWA... 🐘🐫Where stories live. Discover now