BABI NA BIYUIdan har Goggo ta ce tana jin daɗin halayen Safiyya to ta yi ƙarya, Allah Ya sani, kuma Shi ne shaida a kan tsayuwarta wurin inganta tarbiyyar yaranta guda biyu, ita kaɗai ba tare da taimakon kowa ba. Sai dai duk yadda kake naka ƙoƙarin idan Allah Ya ƙaddara bauɗewar wani to dole sai ya bauɗe ɗin. Tunda Safiyya ta tashi a haka Goggo ta tsinci komai nata a bauɗe, ba ta tsoron fushi da zuciya, sai ƙoƙarin ganin an mata kallon babbar yarinya, saboda Allah Ya yi ajiyar basira a cikin ƙwaƙwalwarta. Da shekaru biyu Goggo ta fara koya mata karatu, na boko da na addini, shi ya sa ta tashi da wata irin ƙwaƙwalwa ta ban mamaki, babu wanda ba zai rantse cewa ba makarantar kuɗi ta yi ba.
Ƙoƙarin da take da shi a makaranta ya sa ta zama wata zakaran-gwajin-dafi, ba a cikin ajinsu kaɗai ba, ba ma a iya makarantarsu kaɗai ba, a duk makarantun da ke faɗin eriyar Hayin Rigasa da kewayenta ɗaɗaiku ne waɗanda ba su san Safiyya Usman Baba ba, saboda duk wani abu da ya shafi fita waje daga makarantarsu zuwa wata makaranta da niyyar wata gasa ko muhawara, dole ne sai ka tsinci Safiyya a ciki. Malamai na alhafari da ita ƙwarai, tun daga sadda take aji uku har zuwa shigar ta aji shida da aka ba ta shugabar ɗalibai wato headgirl. Burinta shi ne ta buɗa a ce ita wata ce, ba ta dariya sai dole, magana ma sai da wanda ta ga damar yi, ta raina kowa a ajinsu saboda tsoron ta da suke yi ba mazan ba ba matan ba. Safiyya yarinya ce ɗaya tamkar da dubu a cikin makarantarsu.
Da farko Goggo na ƙoƙarin haɗa musu abinci idan za su tafi makaranta, saboda ba da wuri suke tashi ba, kuma akwai 'yar tazara balle su dinga dawowa tara. Sai dai a lokacin da Safiyya ta koma Sofi, lokacin da ta fara bambance fari da baƙi, ta san wane ne talaka wane ne mai kuɗi, a lokacin ne ta fara ƙyamar a san asalinta, ta fara ƙin a san kalar abincin gidansu. Ƙiri-ƙiri ta ƙwammaci zama da yunwa...zama da yunwa ya fiye mata tafiya da ɗumamen tuwo ko faten dankalin Hausa.
Safiyya ta ƙwammaci ta kwana da yunwa duk kuwa da rashin haƙurin riƙon yunwarta a kan ta tafi makaranta da datti, a kan ta maimaita uniform babu wanki ko da kuwa ba su yi dattin ba.
Goggo bebiya ce, duk da ba sosai take bebentakar ba, sai dai abun ya munana ne kasantuwar haɗe mata da ya yi da in'ina, wanda tana iya maimaita magana sau uku ma ba a gane me ta ce ba, sai dai su yaranta, idan sau ɗaya ta yi suna gane abin da ta faɗa.
Goggo mutum ce mai sanyin hali, mai ƙoƙarin neman na kanta domin ta rufa wa yaranta biyu asiri.
'Hassu Bebiya' shi ne sunan da ake kiran ta da shi a duk faɗin Rigasa, daga farko tana ƙin sunan, sai dai daga lokacin da Safiyya ta fara nuna ƙyamar larurin nata, sai ta daina jin haushin...haushin me za ta ji bayan ga gudan jininta ma tana ƙyamar larurarta?Ido ta runtse a daidai lokacin da ta kai aya a tunani...tunanin da ba ya taɓa kare mata, ba dare ba rana kullum ta zauna cikin wannan halin take. Duniya ta yi mata juyin waina a kasko, camfi haramun ne, da sai ta ce komai ya kife mata ne tun daga haihuwar Safiyya, tamkar ita ce ta zo mata da ƙashin muduruƙwi.
Ta shafe idanuwanta haɗe da matse ragowar ƙwallar da take cikinsu. Ta yi ilmi daidai gwargwado na Islama da na zamani, ta yi saukar Al'Qur'ani har da hardar waɗansu littatafai, a ɓangaren boko kuma ta kammala Secondary, wannan dalilin ne ya sa ta tashi da wayewa, take kuma da wayewar zamantakewa, take ƙoƙarin koyar da yaranta abin da Allah Ya sanar da ita. Sai dai a waɗansu lokutan ita kanta takan ga laifin kanta a kan halayen Safiyya; tana ganin kamar gazawarta ce, kamar kuma ilmin da take ganin ta tashi da shi ne ya sanya ta haka, sai take da na sanin koyar da yarinyar, da wataƙila ba ta koyar da ita ba, da ta tashi kamar sauran yara, da ba ta zama mai ƙyamar halin da suke ciki ba.
Sai dai kuma wani lokacin takan ƙaryata wannan tunanin nata, ba ga Shatu ba? Me ya sa ita ta tashi da tsananin jin ƙai da tausayinta? Me ya sa ko ɗaya ba ta taɓa ƙyamar halin da suke ciki ba?
Ta sake muskutawa a karo na ba adadi, ta kalli agogon tsagaggen bangonsu; ɗaya saura kwata ta gani, don haka ta gaggauta miƙewa domin ɗora abincin rana.***
A gajiya liƙis su Safiyya suka shigo gida, a lokacin har an fara kiran sallar la'asar. Tana sakin hamma ta ce,
"Goggo, hantsi fa ya dubi ludayi. Me aka dafa mana? Mun kwaso rana wallahi, na tsaya yi ma 'yan ajinmu lesson ne, wai Asabar ɗin nan mai zuwa ne common entrance."
Murmushi Goggo ta yi, cikin farin ciki ta ce,
"Al...hamdu...alhamdulillahi ashe kun...kun kusa."
"E Goggonmu, to kin san 'yan ajin namu ba komai ba ne suka sani, shi ne suka roƙi in dinga taimaka musu da abin da na sani daga nan zuwa ranar Asabar ɗin. Ita kuma wannan 'yar anacen ba yadda ban yi da ita ba a kan ta dawo gida ta ƙi, ko ba komai ai ta ci gidansu da yunwa ko, sallar da babu lada."
Ta ƙarasa da hararar Shatu.
Ba tare da Goggo ta ce komai ba ta miƙe ta zubo musu jollof ɗin macaroni, ta tarar Shatu na sallah, Safiyya kuma ta yi zaune ko uniform ta kasa cirewa.
"Ai wallahi ba zan jira ki ba Shatu, wannan baƙar yunwar da nake ji ko sallan ban iyawa sai na ba cikina haƙƙinsa. Ai dai an ce ci na gaba da sallah."
Daga haka ta ci gaba da cin abincin Goggo na bin ta da kallo.
Bayan Shatu ta gama sallar ta gaishe da Goggo sannan ta naɗe daddumar sallar ta shiga ɗaki, doguwar rigar light blue plain yadi ce ta saka sannan ta ɗora hijabi kalar rigar wadda ta sauka har bisa guiwarta ta fito. Tuni Safiyya ta kusa ƙoshi, ta zauna da bismillah ta fara ci.
"Ke ni ba na son shegen kilbibi wallahi. A yanzu haka la'asar ta bada bayan ne za ki islamiyya? To ki je, Allah raka taki gona..."
"Yaya Sofi ni ce takin, islamiyyar kuma gona?"
Shatu ta tari numfashinta.
"Ohon miki. Ni dai na gaji gaskiya ba za ni ba."
Fuska tam Goggo ta haɗe, ta kalli Sofi da ke shirin miƙewa bayan ta gama cin abincin, kallon ta take ba wai don ba ta saba jin ire-iren abubuwan nan daga Sofin ba. Kallon ta take yi tana tunanin har zuwa yaushe ne Safiyya za ta canja halaye? Har zuwa yaushe ne za ta yi hankali ta bambance fari da baƙi? Babu alamun wasa ta ce,
"Ki...kijje...ki yi salla ki...sa kayan islamiyya ki zo...ki zo ku tafi."
Ɓata fuska Sofi ta yi, ta hau dire-diren ƙafa tana gunguni. Goggo ba ta sake komawa ta kanta ba sai ce ma Shatu ta yi ta jira Sofin su tafi tare.
Jan lokaci sosai ta dinga yi, har kusan ƙarfe biyar sannan ta fito fuskar nan babu alamun annuri. Ganin ta fito ya sanya Shatu miƙewa ta rungumi Goggo da fara'arta,
"Goggonmu sai mun dawo."
Murmushi Goggo ta mayar mata haɗe da faɗin,
"Allah...Allah Ya yi...ya yi muku albaika."
Da amin Shatu ta bi bayan Safiyya. A hanya ma tafiya Safiyya ke yi tamkar wacce ƙwai ya fashe wa a ciki, burinta su isa an tashi.
Ko da suka isa ba a tashin ba, sai dai an kusa. Babu giccin ɗalibi ko ɗaya, duk suna ajujuwansu suna ɗaukar darasi. Tun daga nesa Mallam Aminu ya hango su Safiyya, ya gyaɗa kanshi haɗe da ƙarasowa inda suke da zabgegiyar bulalarshi a hannu.
"Ku sai yanzu kuka ga damar zuwa makarantar?"
Ya faɗa da fuskarshi tamkar hutaccen koko ya zube a ƙasa.
"Yo Ustaz daga boko fa muke. Lesson muke yi."
Safiyya ta ba shi amsa tana kallon shi tana ɓata fuska.
"Ke ni za ki ma fitsara? Ku rage tsawonku a nan, kuma ban ce ku matsa ko'ina daga nan ba har sai an tashi."
Da gunguni Safiyya ta rage tsawon, yayin da Shatu ta ji murɗawar ciki, haɗa ido da zabgegiyar dorinar Mallam Aminu kaɗai ya isa ya ɗarsa faɗuwar gaba a zuciyar mutum balle mai yarinta kamar Shatu.
Tafiya ya yi ya bar su a nan, Safiyya sai gatsine take bin sa da shi, burinta a yi a tashi ko ta bi ayarin sauran ɗalibai ta gudu, don ba ta jin za ta iya tsayawa.
Ta kuwa taki sa'a ba a fi minti goma ba aka buga ƙararrawar tashi. Ba ta miƙe ba har sai da ɗalibai suka fara bin hanyar, ta kalli Shatu ta ce
"Sarkin ladabi idan kina nan to, ni dai na yi nan."
Ta kakkaɓe kayanta ta wuce.
"Yaya Sofi kar ki ƙara wa kanki laifi, ki dawo mu ba shi haƙuri."
Ai ko kallon inda Shatu take ba ta sake yi ba ta tafiyar ta.
A nan Mallam Aminu ya samu Shatu, cikin al'ajabi yake kallon ta ita kaɗai babu Safiyya, ya kawar da mamakin ya ce
"Ina Safiyya?"
Tsuru-tsuru Shatu ta yi kamar ta yi ƙarya an turke ta, tana tunanin ta hanyar da za ta kare yayar tata, sai dai babu dama. Duk ta inda ta ɓullo zai iya ganewa, musamman da duk cikin malaman babu wanda bai san halin Sofi ba. Kare ta zai yi matuƙar wahala.
"Ta gudu ko? Za ta zo ta same ni ne. Tashi ki tafi kar kuma ki sake zuwa latti."
Da azama ta miƙe tana masa godiya sannan ta bi hanya domin nufar gida.
YOU ARE READING
HAKKIN UWA
Short StoryWannan labari ne mai tsananin ban tausayi da taba zuciya wanda kuma ya faru da gaske sai dai 'yan gyare-gyare wadanda ba za a rasa ba. Shin kun san girman hakki kuwa? Kun san girma da darajar da uwa take da shi? Kun san babbar tabewa ce ga mai murje...