BABI NA GOMA SHA ƊAYA
Watan su Sofi biyu da dawowa Kaduna hutun Shatu ya ƙare, Umma ta kira waya ta ce Shatu ta koma an samar mata admission za ta ci gaba daga SS1 inda ta tsaya. Sai dai abun mamaki Shatu ta tubure ta ce ba ta san da wannan zancen ba, ba za ta iya tafiya ta bar Goggonsu a cikin wannan halin ba.
"Umma, Goggo ba ta da lafiya, yanzu haka cancer ta ci ta har ta cinye, ta kai ta kawo babu suma ko ƙwaya ɗaya a kanta. Ba zan iya tafiya in bar ta ba, Goggonmu na da buƙatar mai kula da ita sosai, kuma kun san halin Yaya Sofi sarai ba ta da wannan lokacin, hidimar gabanta ma ta fi ta ƙarfi. Don haka ni zan ci gaba da karatuna a nan. A harhaɗo min takarduna a ɗoro a motar haya Umma, da kaina zan nemi admission a nan in ci gaba da zuwa makarantar je-ka-ka-dawo ta nan cikin Hayi, sannan ga islamiyya ma, zan koma. Kin ga ina da wadataccen lokacin da zan kula da Goggonmu."
Duk da ba haka Umma ta so ba amma ba ta da yadda ta iya, Goggo ta yi musu abin da ba za su taɓa iya biyan ta ba, sai ta ga lissafin Shatun ma da har ta yi tunanin zama ta kula da ita. Don haka a take ta amince mata tare da alƙawarin za su zo su duba Goggo da jiki, daga nan su taho mata da sauran kayanta da kuma takardun da dole sai an neme su saboda komawar ta makaranta.***
Hassan ya gama bautar ƙasarshi har ya yi wa Sofi alƙawarin zuwa gidansu a cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ba ya so a ɗauki dogon lokaci, daga ya zo ya koma yake son turo magabatanshi domin su nema masa aurenta.
Sofi ta rasa ta yadda za ta fara tinkarar Goggo da zancen, saboda abu ne wanda ba su taɓa tsammaninshi ba. A yadda Safiyya take da ba da himma ga karatu, ko kaɗan Goggo ba ta taɓa kawowa a ranta wai za ta yi aure a ɗan tsakanin lokacin nan ba, shi ya sa ma ta ci burin ta yi karatu.
"Shatu zan yi magana da ke."
Sofi ta faɗa tana kallon Shatu da ke gyaran wake.
"A kan maganar mu da Hassan ne. Ɗazu yake ce min ranan Thursday ɗin nan mai zuwa zai zo nan ya gaishe da Goggo. Shi ne nake so ki faɗa mata don ni kunya nake ji."
Cikin mamaki Shatu ta ce
"Wai Yaya Sofi da gaske dai kike kenan? Yanzu sai ki yi watsi da mafarkinki saboda wani namiji can da ba ki san asalinshi ba?"
"Ya ishe ki haka Shatu! Idan ba za ki faɗa mata ba ni zan iya cire kunya in sanar da ita."
Shatu ta gyaɗa kai kawai tana ci gaba da aikinta.Bayan sun gama cin abinci ne Shatun ke labarta wa Goggo yadda suka yi da Safiyya, sai wani irin mamaki ya kama Goggo.
Ta maimaita kalmar saurayin Safiyya ya fi sau biyar, ko a mafarki ba ta taɓa tsammanin wannan al'amari ba.
Sai kawai ta jinjina kai ta ce Allah Ya kai mu. Duk da a cikin ranta abun bai yi mata daɗi ba, sam bai kwanta mata ba, makaranta take da burin ɗiyarta ta yi ba aure ba, Safiyya ta yi yarinya sosai da aure, musamman kuma auren wannan zamanin da aka fi zaluntar ƙananan yara. Sannan uwa-uba halin Safiyyar, tana da buƙatar zama sosai ta ƙara ɗaukar darasin rayuwa.Ranar Alhamis tunda gari ya waye suka hau shirye-shiryen tarbar Hassan. Shatu ta saki jikinta tana aiki sosai, yayin da Goggo ta saki aljihu daidai ƙarfinta suka kashe masa kuɗi. Karfe sha biyu daidai sun gama haɗa fried rice da salad, sai pepper chicken. Sannan ga lemuka kala biyu da suka sha ƙanƙara.
Da an yi azahar da ma ya ce musu zai zo. Don haka suna gamawa Shatu ta hau gyaran gida Sofi kuma ga shiga gyara jiki.
Biyu da mintuna Hassan ya iso, shigar ƙananan kaya ya yi, navy blue ɗin jeans da farar riga sai hula hana-sallah, hannunshi riƙe da manyan ledoji guda biyu.
Bayan ya zauna suka gaishe shi, sai ga Goggo ma sanye da hijabi suka gaisa duk da ba sosai take jin shi ba kawai tana amfani da yanayin motsin bakinshi ne, kamar yadda shi ɗin ma ba sosai yake fahimtar ta ba sai yake bin ta da kallon rashin fahimta.
Shatu ce ta gabatar masa da abinci da abun sha, har ta miƙe za ta tafi ya kira ta haɗe da miƙa mata ledojin da ya zo da su. Da godiya ta fita daga ɗakin.
"Babe..."
Ya furta yana kallon Sofi da idanuwanta suka yi ƙanana tsabar farin cikin ganin shi.
"Albishirinki."
"Goro."
Ta amsa masa, narkakkun idanuwan nan nashi da har kullum suke ƙara rura wutar ƙaunarshi a cikin zuciyarta, kyam a kan fuskarta.
"Daga na koma iyayena za su zo su nema min aurenki. Ba zan iya jurar zama babu ke a kusa da ni ba."
"Ni ma haka."
Ta faɗa idanuwanta tsam a cikin nashi.
"I miss you. Ya kwana biyu?"
"Lafiya lau."
"Ba zan iya kintata adadin kewarki da na yi ba Safiyya."
Sai ta saki murmushi, kyakkyawan murmushi, tana sunkuyar da kanta ƙasa.
Suka ci gaba da hirarsu ta masoya.
YOU ARE READING
HAKKIN UWA
Short StoryWannan labari ne mai tsananin ban tausayi da taba zuciya wanda kuma ya faru da gaske sai dai 'yan gyare-gyare wadanda ba za a rasa ba. Shin kun san girman hakki kuwa? Kun san girma da darajar da uwa take da shi? Kun san babbar tabewa ce ga mai murje...