BABI NA TARA
Kamar yadda ta kasa ɗauke idonta daga cikin nashi haka shi ɗin ma ya kasa ɗauke nashi idon daga nata. Abun mamaki duk sai 'yan ajin suka tsura musu ido tare da al'ajabin wannan love at first sight ɗin. Saboda idan har ba soyayya ba babu dalilin da zai sanya su tsura ma junansu ido a farkon shigowarshi ajin, farkon zuwan shi makarantar ma duka.
Shi ne ya fara janye idonshi jin kunyar da ta mamaye shi a tsakiyar sababbin ɗalibanshi.
"My name is Hassan Babangida, am from Abuja-Nigeria. Am here to teach you Biology. Please I need your maximum cooperation."
"In shaa Allahu Uncle."
Duk suka haɗa baki wurin faɗi amma ban da Safiyya da ta kasa daina mamakin kanta. Narkakkun idanuwanshi da suka birkita tunaninta take kallo, Sannan ta hau maimaita sunanshi a ƙasan zuciyarta.
"Who is he?"
Ta tambayi kanta. Kamar yadda shi ma yake tambayar kanshi
"Who is she?"
Yana tunanin kamar ya san wannan fuskar shuɗaɗɗen lokaci. Sai dai where?
Sai da ya fara da maimaici na inda wancan malamin ya tsaya, sannan ya ɗora da nashi cike da ƙwarewa wanda su kansu ɗaliban sun yi mamakin ilminshi. Safiyya ma da ta kasa sakin jikinta har yanzu ta fahimci cewa ya san abin da yake yi, da alama za a je da shi.
Bayan ƙarewar lokacin darasinshi wani malamin ya shigo. Shi kanshi malamin ya yi mamakin yadda baki ɗaya Safiyya ta kasa mayar da hankalinta gare shi bayan kuma ya san ta da ƙoƙarin mai da hankali, shi a tarihin karantarwar shi ma bai taɓa ganin yarinya mai ƙwazo da mayar da hankalinta ga karatu ba kamar Safiyya Usman Baba.Bayan an kaɗa ƙararrawar karyawa, Amira ta ɗan bubbuga Safiyya ganin yadda baki ɗaya hankalinta ba ya tattare da ita. Hankalinta na can wata duniyar, tana tuna idanuwanshi masu zama a zuciya.
Da sauri ta firgita tana kallon Amirar.
"Hey miss lover bird. Since when did you start falling in love?"
Duka Safiyya ta ɗika mata da ƙarfi ba tare da ta ce komai ba.
"Seriously Sofi you're in love. Shi kenan daga zuwan Corper sai soyayya? To a bi dai a hankali kar wurin soyewa a ƙone."
Ta ƙarasa zancen tana dariya.
"Wai waye ya faɗa miki son shi nake? Allah Ya kiyaye min soyayya Amira. Ba za ki gane yadda na ɗauke ta ɓata lokaci ba a rayuwata. Kin manta ina da scholarship jira na kawai ake in kammala wannan jidalin in ɗora?"
"Ban manta ba Sofi. Amma dai to..."
"Amma dai what? Am serious fa. Kawai dai wani irin ƙwarjini ne na ji mutumin ya yi min. Ban san yadda aka yi ba tunda na haɗa ido da shi nake jin gabana yana faɗuwa. Idanuwanshi sun gaza ɓacewa daga tunanina. Wa ma ya sani ko ba mutum ba ne."
Dariya sosai Amira ke yi Sofi na harararta. Sai da ta yi mai isar ta kafin ta tsagaita ta ce
"Ba mutum ba ne ba kam, aljani ne mai sace zuciyar mutane. Wait...ko ba ƙwarjini ba? Me ya sa ni da sauran 'yan aji duk bai mana wannan ƙwarjinin ba sai ke? Kawai yarinya ki yi giving up, you're in love with a new Corper. Wa ma sunanshi? Hassan yake ko Hussein?"
Sake dukanta Safiyya ta yi tana jin haushin yadda Amirar ta dage lallai soyayya ce bayan ita kuma ta san ba soyayyar ba ce...babu soyayya a gabanta. Burinta ta yi karatu, ta zama cikakkiyar likita, burinta, sannan kuma mafarkin Goggonta.Tun daga wannan ranar kullum Uncle Hassan kamar yadda ɗalibai ke kiran shi, idan ya shigo idonshi na kan Sofi haka ita ma nata idon yana kanshi. Kuma har yau magana ba ta taɓa haɗa su ba, ko tambaya ya yi shiru take ko da kuwa ta san amsar. Sai dai a kullum ƙara jin kusancinsa take da ruhinta, jin sa take yi kusa da zuciyarta, ƙwarjininsa karuwa yake. Idanuwansa...ba za ta iya fasalta yadda take jin su ba.
Ana cikin haka aka fara yi musu extra lesson na WAEC DA NECO, kuma Hassan shi ne zai ja ragamar Biology. Don haka dole Safiyya ta cire ma kanta komai, don a yanzu ta gama gasgata cewa she is in love ɗin kamar yadda Amira ta faɗa, son Hassan take yi da dukkanin zuciyarta, amma ita kaɗai take haukanta tunda a ganin ta ba ta gabanshi, ko damuwa da ita bai yi ba shi ya sa bai taɓa yi mata tambaya a cikin aji ba.
Fara lesson ɗinsu shi ya jawo fara magana a tsakaninsu. Ranar kuwa daga shi har ita baccin daɗi suka yi. Shi a nashi ɓangaren ganin girman kan yarinyar yake yi ta yadda ko gaishe shi ba ta yi. Sannan ga uwa-uba ƙwarjinin da take yi masa. Ita kuma a nata ɓangaren gani take bai taɓa damuwa da ita ba tunda ko tambayoyi yake yi a aji ba ya kallon ko gefen da take balle har ya tambaye ta ɗin.
YOU ARE READING
HAKKIN UWA
Short StoryWannan labari ne mai tsananin ban tausayi da taba zuciya wanda kuma ya faru da gaske sai dai 'yan gyare-gyare wadanda ba za a rasa ba. Shin kun san girman hakki kuwa? Kun san girma da darajar da uwa take da shi? Kun san babbar tabewa ce ga mai murje...