Page 12

257 23 6
                                    

BABI NA GOMA SHA BIYU

Cike da zallar takaici Shatu ke bin ta da kallo, ta gyaɗa kai ta ce,
"Addini bai haramta ba Yaya Safiyya, sai dai manzon Allah SAW cewa ya yi; idan wanda kuka yarda da addini da ɗabi'arshi ya zo neman auren 'yarku ku aura masa...har zuwa ƙarshen hadisin. Shi kuma Hassan bai da kyawawan ɗabi'un da har za su sa a so shi, a ba shi aurenki."
Miƙewa tsaye Sofi ta yi cikin ƙunar rai ta ce
"Wai me ya yi muku da kuke ƙin sa? Wane abu ya yi da har za a munana masa zato a ce bai da kyawawan ɗabi'u? Ina ce cikin girmamawa ya gaishe da Goggo? Mene ne laifinsa kuma?"
Miƙewa ita ma Shatun ta yi, a ƙufule ta amsa da,
"Yaya Sofi ban ce miki ni ko Goggo muna ƙin Hassan ba, Goggo ba ta hana ki auren shi ba, shawara ce kawai na ba ki kuma da alama ba za ta yi tasiri ba. Ga ki ga Hassan, idan kin so gobe a ɗaura muku aure babu ruwana!"
Daga haka ta fice daga ɗakin.

A bakin ƙofa ta yi kiciɓis da Goggo tsaye kamar an dasa ta, da alama ta ji duk maganganunsu, hawaye sai sauka suke a fuskarta tamkar an buɗe famfo.
Gaban Shatu faɗuwa ya yi, da sauri ta kama hannun Goggon suka nufi ɗakinta, ta zaunar da ita sannan ta hau share mata hawayen da hannunta.
Sun jima a haka zaman kurame, kafin Goggo ta ce,
"Me ya...sa kika...kika tinkaye... ta da maganai?"
"Goggo, shawara ce na ba ta. Saboda duk wani abu da mutum zai yi in dai babu albarkar iyaye a cikinsa to ba zai taɓa ganin daidai ba. Yaya Sofi tana da matsala a rayuwarta, ita babu wanda ya isa ya ce ta yi ba daidai ba ko kuma ya ba ta shawara. Ban sani ba ko so take ta rasa mai faɗa mata gaskiya, ni kuma dai na ga hatta waɗanda suka rasa iyayensu kuka suke yi, suna neman wanda za su ce musu yi ko bari, umurni ma ba shawara ba."
Murmushin ƙarfin hali Goggo ta saki, ta ce,
"Yanzu...me hakan ya...amfana miki? Kin yi...kin...yi nasaya?"
Gyaɗa kai Shatu ta yi,
"Ban yi nasara ba Goggo, amma dai na fita haƙƙinta a matsayina na 'yar'uwarta da muka tashi kan shimfiɗa guda. Ina sa ran ta kyautata wa kalamaina zato, ta nutsu, ita da zuciyarta su yi shawara, na tabbata akwai abin da za ta ɗauka daga cikin maganganun nawa."
"Allah...ya sa."
"Amin Goggonmu. Ki samu ki kwanta dare na yi."
Babu musu ta kwanta, sannan ita ma Shatun ta kwanta sai tariyar maganganun Safiyyar take yi.
Ita kuwa Sofi tun fitar Shatu kuka kawai take yi, wani sashe na zuciyarta na shawartarta da ta tsaya ta yi nazarin kalaman Shatun, yayin da ma fi rinjayen zuciyarta ke ba ta tabbacin Hassan bai da wata matsala, zai kaunace ta fiye da kowa da komai a duniya, zai ba ta gata, sannan zai wadata ta da dukiyar da ba ta tashi ba a cikinta.

Su duka ukun babu wacce ta yi baccin kirki har asuba. Kowa da bikin zuciyarta, dukkansu da tunanin da suke yi musamman Sofi da ke ganin kamar Goggonsu na son raba ta da Hassan ne, bayan kuma ba ta jin cewa akwai sauran rayuwa mai farin ciki da za ta yi a gaba matuƙar ba ta auri Hassan ba.
Hassan shi ne cikashen rayuwarta, da shi zuciyarta ke bugawa, da Hassan take shaƙar kowanne numfashinta. Da dukkanin zuciya da ruhinta take ƙaunarshi.
Ta yaya lokaci guda za a ce ta rabu da shi kawai saboda bai kwanta wa Goggo a zuciya ba?

Jiki sanyaye duk suka tashi. Da wuri Shatu ta shiga kitchen ta hau neman abincin kalacinsu.
Dankalin Hausa ne ta soya sai ta yi masa miyar albasa. Ko da ta gama Sofi har wanka ta yi, tana kwance tana waya da Hassan.
Gyaɗa kai kawai Shatun ta yi ta fice daga ɗakin.
Ganin haka ya tabbatar wa da Sofi dalilin zuwan, sai ta saki sassanyan murmushi tana faɗin,
"Baby zan karya, idan na gama zan maka flashing."
Daga ɗayan ɓangaren Hassan ya ce
"Ni kuwa kin san jin muryarki kaɗai ya ƙosar da ni, da matuƙar yunwa na tashi amma wayar nan da muke yi ta sa na ji ni full."
Cikin muryar shagwaɓa haɗe da turo baki ta ce
"Ba na son kana zama da yunwa, ka daure ka ci wani abu."
Shiru ta ji ya yi, hakan ya sa ta sake marairaicewa tare da faɗin
"Ka ji baby?"
Murmushi mai sauti ya saki, wanda ya daki zuciyar Sofi, ba ta san sadda ta furta 'I love you' ba.
"Zan karya yanzu, sannan an jima idan mun yi waya, zan faɗa miki yadda muka yi da Mommy. Na tabbata ba za a wuce kwana uku ba a zo an nema mini aurenki ba."
"Alhamdulillahi."
Ta faɗa da wani irin sauti, tana jin komai na duniyar yana yi mata tsananin daɗi, burinta yana daf da cika, ta kusa zama mallakin Hassan ɗinta.
"Sai mun yi waya."
Ya faɗa haɗe da yanke wayar ita ma ta miƙe.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now