Page 10

246 27 3
                                    

BABI NA GOMA

Da kuka Shatu ta rungume Goggo, nannauyar ajiyar zuciya Goggon ta sauke, har cikin ranta ta ji daɗin zuwan nasu, saboda tana da tsananin buƙatar mutum a tare da ita, tana ganin idan har tana jin motsin mutum a gidan za ta rage wata damuwar. Sofi kasaƙe ta yi tana kallon su, kafin ita ma cike da ƙaunar mahaifiyar tata ta haɗa su har Shatu ta rungume.
Sun jima a haka kafin suka rabu, Goggo ta ƙirƙiro murmushin da iyakacinshi bisa leɓonta, ta ce,
"Sannu...sannunku da...hanya."
"Yawwa Goggonmu, sannu da gida."
Shatu ta faɗa tana share hawayenta, don ita kam ba kaɗan yanayin na Goggonsu ya tsorata ta ba, kana ganin ta ka san akwai naƙasun lafiya a tattare da ita.
Bayan sun zauna Goggo ta miƙe domin kawo musu abinci sai Shatu ta bi bayanta. Tare suka ɗauko komai suka jera kan tabarmar da ke shimfiɗe tsakiyar falon, sannan suka zauna su duka ukun suka zuba abincin tare suka ci.
Bayan sun gama ne Shatu ta sake dubar Goggo ta ce
"Goggonmu ba ki da lafiya ne?"
"Me...me kika gani...auta?"
Goggon ta tambaye ta da murmushi.
"Goggo komai ma na gani. Kin rame sosai kamar ba ke ba. Ko ba kya cin abinci ne?"
Goggo ta gyaɗa kai,
"Kawai...kawai dai...ina yawan...ciwon kai ne."
Shiru Shatu ta yi tana tarwatsa kalaman Goggon a cikin ƙwaƙwalwarta. Ba za ta iya musa mata ba amma kai tsaye ta san ba gaskiya Goggo ta faɗa mata ba. Babu ciwon kan da zai saka mutum irin wannan mummunar ramar sai dai na hawan jini ko wani babban larurin. Ko da take ƙaramar yarinya ta san cewa akwai babban abin da yake damun Goggon, amma sai ta yi ƙoƙari ta kawar da zancen ta hanyar faɗin,
"Zan kai ki asibiti gobe, gwara mu ga likita mu san dalilin ciwon kan, don kar a je wani ciwon ne na daban kuma muna nan zaune har ya yi tsananin da ba mu fata."
Goggo ta yi murmushin yaƙe tana kallon Shatu,
"Kai...kai ki...damu autata. Akwai maganin...da nake sha. Kuma...kuma ina samun sauƙi...sosai."
Kai Shatu ta gyaɗa cike da tausayin Goggon tasu, tana jin wasu hawayen na taruwa a idanuwanta. Ta ɗaga kanta ta kalli Sofi da kwata-kwata ma hankalinta ba ya gare su, da ƙyar ma idan ta san zancen da suke yi, tamkar ma ba a duniyar take ba.
"Yaya Sofi..."
Shatu ta faɗa tana kallon ta amma shiru, ba ta san tana yi ba.
Ta sake maimaita
"Yaya Sofi."
Da ƙarfi tana tafa hannu a saitin fuskarta.
Firgigit Sofi ta dawo hayyacinta tana murmushin yaƙe wanda ita kanta ta san babu mai yarda da murmushin gaske ne ta yi.
"Yaya Sofi lafiya kike?"
Shatu ta tambaye ta cikin mamaki don tunda suka taho ta lura tunani ya yi mata yawa, tana fatan Allah Ya sa ba soyayyar da ta faɗa a ciki ba ce ta jawo mata wannan mugun tunanin.
"Lafiya lau nake Shatu. Kawai dai ina tunanin yanayin Goggonmu ne, kamar ba ita ba."
Ta faɗa tana mayar da kallon ta ga Goggon tasu.
Shatu ta gyaɗa kai ta ce,
"Ki daina tunani to kar ke ma wani abu ya same ki. Ciwon kai ne yake damun ta kuma ta ce tana shan magani."
Sofi ta ɗaga kai tana kallon Goggo da murmushi,
"Allah Ya ƙara miki lafiya Ya yaye miki Goggonmu."
"Aa...aamin Safiyya."
Goggo ta faɗa ita ma tana mata murmushi.
"Yanzu dai...yanzu kin gama...kayatu...kin gama...sauya ki zama likita ko?"
Shiru Sofi ta yi tana tunanin maganarsu ita da Hassan. Ta ina za ta iya fara faɗa wa Goggo cewa ta canja ra'ayinta ita yanzu ba karatu ba ne a gabanta? Ta ina za ta iya shaida mata ta faɗa kogin soyayya tsundum kuma ba ta jin za ta iya tsamo kanta? Sosai Goggon ta ci buri da karatunta, a kulluyaumin fatanta ta yi tsawon rayuwar da za ta ga Sofinta ta zama cikakkiyar likita.
Sai ga guntuwar ƙwalla a idanuwan Sofi wanda ita kanta ba ta san da fitowarsu ba sai guminsu kawai da ta ji a kwarmin idanuwanta. Sai kuma ta tuna da Hassan da daɗaɗan kalamanshi. Ta tuna da alƙawarinshi gare ta. Ta tuna da nan da lokaci kaɗan za ta zama mallakinsa, kawai sai ta  saki murmushi a saman fuskarta. Goggo da Shatu suna kallon tun daga zubar hawayenta har zuwa murmushin nata, sai abun ya ba su mamaki.
"Lafiya...lafiya kike...kuwa?"
Kamar tana jira ta ce
"Ƙalau nake Goggonmu. Kawai dai da farko na tuna da yadda kika rame ne duk tausayinki ya kama ni. Sai kuma na tuna cewa na dawo gare ki yanzu zan ba ki kyakkyawar kulawa. Sannan ina da scholarship, zan cika miki burinki, yanzu ko ba yanzu ba."
Wani irin daɗi sosai Goggo ta ji, a ganin ta Safiyya ta fara hankali, wataƙila kammala makarantar da ta yi ya sanya mata nutsuwa, ta fara sanin rayuwar duniya.
"Allah Ya yi...muku albaika."
Ta faɗa tana kallon su duka biyun. Suka amsa da amin.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now