Page 6

164 21 2
                                    

BABI NA SHIDA

Dukkansu sai suka sha jinin jikinsu. Guda daga cikinsu ta ce
"Shi kenan Minal kin ja mana masifa. Ni wallahi tsoron yarinyar can nake yi."
Minal ta ce
"Ban ɗauka za ta ji ni ba, Allah kuwa ina tsoron shiga case a wurin Pc, ga shi na ji an ce ƙoƙarin yarinyar ya sa har pc ɗin ta san da zaman ta, kun san ita tana son mutum mai ƙoƙari sosai."
Sai kuma ta yi rau-rau da idanuwa ta ce
"Mun shiga uku! Yanzu ya za mu yi?"
"Ya za mu yi, ko ya za ki yi? Ni dai wallahi ba zan shiga case ɗin da ban ce uffan ba a cikinsa. Dan ana kiran mu zan ce ke ce kika kira ta da mayya."
"Haba Jamila kar mu yi haka da ke mana."
"Ai kuwa an yi an gama."
Jamilar ta faɗa tana tafiya. Gudar ma ta ce
"Wallahi ko ni ba zan tsoma kaina a case ɗin nan ba. Duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka."
Ta bi bayan Jamila.
Sai Minal ta ɗora hannu bisa kai.
"Khadija kin ga abin da kika ja min ko? Da na san abin da zai faru kenan wallahi da ko ta hanyar nan ma ba za mu bi ba. Na shiga ukuna!"
Hawaye suka hau zarya a kunatunta.

Sadda suka isa ɗakinsu duk sauran ba su dawo daga makaranta ba. Sai Sofi ta yi wani irin murmushi wanda ba koyaushe ne take yin irinshi ba sai ƙetarta ta taso. Ta ce
"Na tabbata na tsorata su. Kuma ba wai wurin pc ɗin zan kai su ba, kawai na ji ciwon fasa min bokitina da suka yi ne nake neman hanyar da zan ce su biya ni a sauƙaƙe. Na tabbata idan a haka nan na ce su biya ni sai ma sun zagi uwata da ubana. Don 'yan SS3 ɗin can ba imani ne da su ba."
Amira ta ce
"Ta yaya za su biya ki bokiti bayan kuma kin ce za ki kai ƙarar su?"
Ta sake wani murmushin ta ce
"Za su zo su ba ni haƙuri na tabbata."

Washe gari kuwa sai ga Minal sun zo har ɗakin su Sofi ita da su Jamila da ta shawo kansu da ƙyar. A lokacin ma Sofin ba ta nan ta je ban-ɗaki, don haka suka zauna zaman jiran ta har ta fito ɗaure da tawul da farin hijab a jikinta.
Kallon sama da ƙasa ta hau yi musu, duk da ta san dalilin zuwan nasu amma sai ta basar, ta dai yi musu sallama sannan ta kalli Minal da ke zaune kan bakin kafitarta ta ce
"Excuse me zan shafa mai."
Ɗan muskutawa Minal ta yi, hakan ya sa Sofi ta zauna ta jawo lokarta ta hau shafa mai. Duk suna zaune har ta kammala ta fesa turare ta sanya sport wears ɗinta saboda yau ranar sport ce.
Amira da ke kwance kan up ɗin gadon duk abin nan idonta biyu jira take kawai ta ji inda za a kai ga wasan, ta gaggauta durowa dan kar ta makara, ta san dai Sofi ba jiran ta za ta yi ba.
"Yaya Minal ku ne? Sannunku da zuwa."
Amirar ta faɗa cikin girmamawa tana yi tana ɗan satar kallon Sofi da ta basar har a lokacin tana harkar gabanta.
"Sofi ki jira ni fa, kin san ba jimawa nake a wanka ba."
Ta juyo ta kalli Amira haɗe da maka mata harara,
"To ki jira ni, kin san ba ni da lokacin ɓatawa. Kuma wurin PC zan fara zuwa kafin sport time ɗin."
Sannan ta kalli Minal da duk ta sha jinin jikinta ta ce
"Duk abin da muka dawo muka tarar babu zan iske ku har room ɗinku, sai a yi adding da bucket ɗina da kuka yi silar ya fashe."
Daga haka ta fara ƙoƙarin barin kwanar tasu zuwa wata kwanar domin kwanciya take so ta yi kafin Amirah ta gama shiryawa.
Jawo hannunta Minal ta yi, cikin marairaicewa kamar shege cikin marsandi, ta ce
"Don Allah Safiyya ki yi haƙuri a kan abin da ya faru jiya, ba nufina ba kenan."
Wani irin kakkausan murmushi Sofi ta saki, sannan ta juyo ta ce
"Ba ni za ki ba haƙuri ba Yaya Minal, bari za ki idan mun je gaban PC sai ki tattaro duk wata kalmar ban haƙuri da kika sani ki ba ta. Ba ni mayya ba ce ba?"
Minal ta gyaɗa kai,
"Ke ba mayya ba ce ba, kawai Hausa ce. Kin san ko ƙoƙari mutum gare shi ana cewa ai wane maye ne. To ni nufina kenan. Ya za a yi in ce miki mayya ni da ko sanin ki ban yi ba sai a school ɗin nan?"
"Ni ma dai haka na gani."
Sofi ta faɗa tana janye hannunta daga riƙon da Minal ɗin ta mata.
"Na yi haƙuri for now, amma ki kiyayi shiga gonata. Ko wata kika ji tana son shiga rayuwata ki faɗa mata ruwa ba sa'an kwando ba ne, sannan ba kowane sha'ani nake shiga ba. So, be careful, and make sure kun min replacing bucket ɗina da wani."
Daga haka ta wuce kwanar su Maryam ta kwanta.
Tana jin sauran ƙawayen Minal suna tsaki amma sai murmushi take, ba ta so ta yi dariya yadda za su gane su raina ta, har sai da suka tafi sannan ta fasa dariyar tana faɗin,
"Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha."

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now