Page 3

218 17 0
                                    


BABI NA UKU
Hutun makaranta ya zagayo, da farin cikinsu suka shigo gida dukkansu suna jin daɗin yadda sakamakon nasu ya yi kyau, Shatu ta zo ta biyu a ajinsu mai ɗauke da mutum tamanin da biyu, Sofi kuma ta yi na ɗaya cikin su tamanin da takwas. Goggo ta yi farin ciki sosai, hakan ya sa ta cire kuɗaɗen da aka kawo mata biyan bashi, su kenan, ta sayo kayan miya wadatattu, ta sayi kaza guda aka gyara mata, ai kuwa shinkafa da miyar kaza ta dafa musu.
Washe gari ta ce da Shatu ta shirya domin tafiya hutu wurin dangin mahaifiyarta kamar yadda ta saba tafiya duk ƙarshen zangon karatunsu.
"Ah ni su Shatu za a je a ciyo kayan daɗi. Ni wallahi Goggonmu da ma ki ce mu tafi tare."
Safiyya ta faɗa tana washe haƙora kamar wata sabon shigar hauka.
"Kawai ki shirya mu tafi Yaya Sofi. Wancan zuwan ma da na yi sai da Aunty Fati ta ce kina ina na ce kina nan. Ta so a ce tare muka je."
Shatu ta taya ta washe haƙoran.
Ta mayar da kallon ta ga Goggo da ta yi musu banza,
"Kin gani ko Goggonmu. Don Allah ki ce in shirya in bi ta. Wallahi dangin mahaifiyar Shatu 'yan gayu ne ni burge ni suke. Abinci mai rai da lafiya ake ci, ga shi har da sutura suke mata idan za ta dawo."
Ɓata fuska Shatu ta yi, ta tsani ko me Sofin za ta yi ta nemi kushe ƙoƙarin Goggonsu. Maganar abinci mai rai da lafiya take yi, alhali ko jiya mai daɗi suka ci har ma miyar ta yi saura aka dafa musu taliya yau. Ta rasa gane wace irin mutum ce Sofi, ba ta da godiyar Allah, sannan a kullum burinta ta ɓata ran Goggonsu.
"Ya...ya isa...ya isa haka. Shatu kayanki dan...da na wanke, na goge su...ki...ki haɗa su wuyi guda ci...cicicikin ƙayamai jaka, zan kai...ki tashan Kawo."
Kai Shatu ta ɗaga haɗe da wucewa ɗaki ta hau shirya kayan da Goggo ta wanke ta goge su jiya a cikin makimanciyar jaka.

Bayan Shatu ta gama shiryawa ta fito, Goggo ta ɗauki jakar tata, sannan ta juya ga Sofi da ke ta faman cika tana batsewa, ta gyaɗa kai ta ce,
"Ki...kiz zauna kai...kai ki fita...kai ki fita ko'ina Safiyya, ki tsaye...mana gida...zan kai Shatu...Kawo pack."
Banza Sofi ta mata sai duƙar da kanta da ta yi ƙasa tana gunguni. Ba tare da Goggo ta sake  bi ta kanta ba ta yi gaba, Shatu kuma ta dawo  ta rungume Sofi, cikin soyayya ta ce
"Yaya Sofi me kike so in kawo miki idan zan dawo? Sannan don Allah ki kula mana da Goggo sosai kin ga ni tafiya zan yi. Ki dinga taya ta aiki sannan kar ki dinga fita yawo idan ba dole ba."
Sofi ta ɗago kai ta kalli Shatu haɗe da watsa mata harara. Cikin ɓacin rai ta ce
"To sannu uwar iya. Ke ce za ki faɗa min abin da ya dace in yi? To na ji wannan, sai ki ƙara wa bujenki iska."
"Ki yi haƙuri Yaya Sofi. Ni na tafi; Goggo na jira na a waje. Idan exam ɗinku ta fito Allah Ya ba da sa'a."
Daga haka ta fita har da ɗan gudunta ta samu Goggon a tsaye da maƙwafciyarsu Balki suna magana.
"Kin...kin fito?"
Goggo ta tambaye ta da murmushi. Da murmushi ita ma Shatun ta amsa mata. Bankwana suka yi da Balki sannan suka tinkari bakin titi, ba su wani ɓata lokaci ba suka samu keke napep wadda ta fitar da su Kagoro by express, daga nan kuma suka samu yellow bus wadda ta kai su har tashar Kawo.

Ga dreban da Goggo ta saba damƙa amanar Shatu idan za ta tafi Zaria ta dosa, ta taki sa'a kuwa shi ne a layi, don haka ta biya shi kuɗin motarta tare da takardar lambar wayar Antin Shatu, saboda ba ta da tabbas ko har yanzu yana da lambar. Sai da ta ga tashin motar tasu sannan ta bar tashar, zuciyarta cike da alhinin yanda za ta yi kewar yarinyar da ba ita ta haife ta ba amma sau dubu ta fiye mata wadda ta haifa da cikin nata.

Kwanan Shatu goma da tafiya jarabawar su Sofi ta fito, ta kasance ita ce overall student, ma'ana ɗalibar da ta fi kowa ƙwazo, a duk 'yan aji shidan da suka gama ta fi kowa maki, ta samu adadin makin da ake buƙata har ma ta zarce, don haka da ita da waɗansu mutum biyu sun yi nasarar samun FGGC Zaria, makarantar da da kuɗin mutum ma yana iya nemanta ya rasa, amma ga ƙoƙari da mayar da hankalin Sofi ya kai ta.
Ai ranar murna a wurinta ba a magana, daga ita har Goggo sai annuri suke, Sofi na tunanin yadda za ta ƙara zama babbar yarinya idan ta fara FGGC Zaria, yadda za ta ƙara buɗawa sosai, za ta manta da wata rayuwa ta talauci, saboda duk sun san labarin makarantar, ko provision sai dai idan ka so ka je da shi, amma ana bada abinci da duk wani abu da ya dace a can.

Washe gari Anti Fati ta dawo da Shatu saboda saura kwana biyar hutu ya ƙare. Ba zato ba tsammani sai ga su tare. Ai kuwa Goggo ta ma rasa yadda za ta yi saboda murna. Ta ba su kyakkyawar tarba kafin ta zauna inda suka hau hirar yaushe gamo, kasantuwar sun daɗe ba su ga juna ba. Bayan sallar azahar Goggo ta shiga kitchen ta hau shirya dafadukar shinkafa da wake Shatu na taya ta. Ita kuwa Sofi tana wurin Anti Fati tana ƙara ba ta labarin nagartar FGGC Zaria da irin jin daɗin da za ta tarar a can, washe baki kawai take yi tana gyara zama.

Sai bayan la'asar sannan Goggo ta gama girki, ta zuba ma Anti Fati nata daban, sannan ta zuba wa Shatu da Sofi a ƙaramin faranti.
"Sannu da ƙoƙari Goggon su Shatu. Mun sara miki aiki ko?"
"Ko...ko alama...ko alama Fati."
Goggo ta tarbe ta tana sakin murmushi.
Abincin suka gama ci suka sha ruwa sannan Anti Fati ta ce
"Na san za ki yi mamakin ganin da kaina na dawo da Shatu saboda ban taɓa zuwa da kaina ba sai dai ko idan zumunci ne ya kawo ni. Maganar da ke tafe da ni dole za ta girgiza ki, za ta girgiza Shatu da Sofi, sai dai babu wata mafitar ne dole sai na faɗe ta. Dole ce ta sanya ni wanko ƙafafuwa na zo da kaina."
Ta ɗan muskuta tana kallon yadda Goggo ke bin ta da kallo, sannan ta ɗora da,
"Duk danginmu ne an haɗu an ce Shatu za ta koma kwata-kwata wurinmu da zama. Ki yi haƙuri ba don mun ga gazawarki ba, sai dai kowanne yaro yana da burin ya tashi a cikin danginshi. Babu alaƙar jini a tsakaninku, sannan Shatu na da buƙatar na jikinta sosai. Don haka an yanke shawarar za ta koma gidanmu, kin ga Ummanmu ita ma tana buƙatar jin motsin yara a tare da ita. Sannan ƙaunar da muke wa Anti Binta mahaifiyar Shatu ita muke son miƙawa ga ɗiyarta Aishatu.
Ba zan gajiya da ba ki haƙuri ba, na san irin shaƙuwar da take tsakaninku ke da ita, da kuma uwa-uba Safiyya da suka tashi ɗaki ɗaya komai nasu a tare, dole raba su a lokaci guda zai zauna a zukata. Sai dai komai ya zo da sauƙi tunda ita Safiyyar ta samu gurbin karatu a Zaria. Kenan zumuncinsu zai ci gaba, duk lokacin visiting za mu dinga kai mata ziyara."
Can farkon maganganun Anti Fati ba kaɗan ɗin razana Sofi suka yi ba. Sai dai daga ƙarshe sun wanke mata zuciya, ta washe baki ta ce
"Kin ga Anti Fati har hutu ma idan aka yi ba zan zo Kaduna ba a can zan tsaya ko?"
Murmushi Anti Fati ta yi haɗe da ɗaga mata kai. Goggo da ta kasa ko da ƙwaƙƙwaran motsi, tunanin yadda za ta rayu babu yarinyar da ta gama shaƙuwa da ita take yi, yarinyar da ke tsananin jin tausayi da jin ƙanta. Ta dafe goshinta ta kasa furta komai.
Da sauri Anti Fati ta kama ta ta cire hannun da ta dafe goshin da shi. Cikin kwantar da murya ta ce
"Ba wai mun raba ki kwata kwata da Shatu ba ne Goggo, za ta dinga kawo miki ziyara lokaci zuwa lokaci. Idan har na ce kun rabu kenan ai mun tabbata butulu. Ban manta da taimakonki gare mu ba, ban manta da shaƙuwar da kuka yi da Anti Binta ba. Kalar kyautatawar da kike mana idan mun zo hutu wurinta kaɗai ya isa ya sanya mu saka miki da alkhairi. Sannan tafiyar Shatu ko alama ba mu tsara ta da nufin ɓata miki rai ba, sai ƙoƙarin ganin an gyara future ɗin yarinyar, sannan ke ma ɗin a rage miki nauyi, ga Sofi marainiyar Allah."
Kai Goggo ta jinjina,
"Na...nag...gode."
Kawai ta iya furtawa tana jin gumin hawaye na sauko mata. Da saurin Shatu ta zo tana shafe mata ita ma ɗin tana nata.
"Goggonmu ki daina kuka, idan ba ki bada izini ba wallahi ba zan tafi in bar ki ba."
Goggo ta ƙirƙiro murmushi ta hau ba ta kwarin guiwa har zuwa lokacin da ta ga hankalin Shatun ya kwanta.

Kasantuwar yamma ya yi ya sa Anti Fati cewa za su tsaya su kwana, saboda su haɗa kayayyakin Shatu a tsanake. Ita ko Sofi farin cikinta da ta samu tudun dafawa idan ta fara karatu a Zaria, dangin Shatu masu kuɗi ne ta shaida da hakan.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now