Page 4

176 22 0
                                    

BABI NA HUƊU

Da dare firfir bacci ya gagara zo wa Goggo. Kwana ta yi juyi tana tunanin halin da za ta shiga na rashin Shatu a kusa da ita. Hutun da take tafiya ma kanshi cike take da kewar ta har sai ranar da ta dawo, balle kuma wannan tafiya ce ta dindindin. A ƙarshe dai da ta rasa madosa sai kawai ta miƙe ta ɗauro alwalla ta hau yin nafila tana zikiri har zuwa lokacin sallar asuba.
Bayan ta gama sallah ta nufi kitchen domin haɗa kalaci saboda Anti Fati ta ce tafiyar sassafe za su yi, don ba ta zo da shirin kwana ba, mijinta ma a waya ta kira ta sanar masa zancen kwanan saboda sun yi dare.
Farar doya ce ta soya da miyar jajjage, ko da bakwai ta yi ta gama komai har ruwan zafin wanka ta dafa musu, don haka ta gabatar da komai sannan suka gaisa. Anti Fati ta ce sai ta yi wanka sannan za ta karya.

Ƙarfe takwas da rabi suka kammala komai suka miƙe da shirin tafiya, nan fa ake yin ta. Duk yadda Goggo ta so ta hana ma idonta kuka kasawa ta yi. Sun shaƙu da Shatu ba kaɗan ba, shekaru kusan bakwai ba wasa ba. Ita ta shayar da Shatu duk da ba da ruwan nononta ba ne, da madara amma ita ce komai nata. Da a ce Sofi ce za a zo a raba su da rana tsaka ba ta tunanin za ta shiga damuwa kamar yadda ta shiga a yanzu na rabuwar ta da Shatu. Ita ma kanta Shatun kuka take bayan ta rungume Goggo. Sun jima a haka babu wanda ya yi yunƙurin raba su har sai sadda Goggon dan kanta ta saki murmushi ta raba jikinsu tana kallon Shatun da ke kuka da iya ƙarfinta. Sosai take rarrashinta amma duk da haka ba ta yi shiru ba. A ƙarshe dai a haka suka rabu tana kuka kamar ranta zai fita. Safiyya ta tsaya har suka samu napep sannan ta biyo bayan Goggo suka dawo gida.
"Goggo wannan kuka haka. Ai da wannan wallahi da ma roƙon su kika yi kawai mu bi su har ke ɗin mu koma wurinsu da zama tunda dai masu kuɗi ne ba za su rasa kuɗin riƙe mu ba."
Banza Goggo ga yi mata ta ci gaba da shara tana matsar ƙwalla.
"Goggo fa da ke nake. Allah kuwa ina son dangin Shatu. To idan ke ba za ki koma ba ki ba su ni kawai. Kin ga idan na samu hutun makaranta kamar na term uku sai in kawo miki ziyara. Daga nan ma zan zo miki da..."
"Ya...isa!" Goggo ta faɗa haɗe da nuna Sofi da hannu.
"Ban...ban san koko...ko sai yaushe ne...sai yaushe za...ki hankali...ba Safiyya. Giima kike amma kina cin kashi."
"Allah ba da haƙuri Goggonmu. Ba ni na kar zomon ba."
Ta faɗa haɗe da shigewa ɗaki. Ita kam sauƙi guda da ta samu shi ne karatun da za ta fara a Zaria, shi kenan za ta koma cikin dangin Shatu masu kuɗi. Ta sakar wa kanta murmushi tana jawo littattafanta da ta jima ba ta karanta ba, ta hau dubawa tana karatu.

A ɗakin Goggo ta same ta da littafi a hannu. Gefenta ta zauna, ta kalle ta ta gyaɗa kai, sannan ta ce
"Kamai yanda...kamai yanda kika...ji Fati ta ce, ta ce...babu alaƙai jini, ta jini tsakaninmu da Shatu...shatu to haka ne. Idan ba ki sani ba to yau zan faɗa miki...zan faɗa miki ta yanda muka haɗu. May be idan kika ji...idan kin ji za ki ciye ma...kanki kwaɗayin... yayuwa a cikinsu."
Kasaƙe Sofi ta yi tana sauraren Goggo, ba wai don tana tsammanin labarin na Goggo zai yi tasirin da har za ta cire wa kanta ra'ayin rayuwar 'yan uwan Shatu ba.

Shud'add'en Lokaci
February 1995

Zaune take gaban murhu, idonta cike taf da hawaye saboda hayaƙin itace, ba busasshe ba ne ba iccen ko alama, shi ya sa take ta fama da wahalar bushin wuta kuma abincin ya gagara ya dahu.
Sallama ta ji, ta ɗaga kai da sauri tana gyara hijabin jikinta, ganin mata biyu a gaba sun sako wata macen a tsakiya lulluɓe da mayafi wanda har fuskarta ta rufe, ya sa Goggo saurin miƙewa tana musu maraba,
"Ku iso...iso...daga ciki."
Ta faɗa tana gyara tabarma.
Babu musu suka zauna, sannan a mutunce suka gaisa, ba ta san su ba, ba kuma ta nemi jin ba'asi ba tunda dai ta san dole ne za su yi mata bayanin kawunansu.
Ɗaya daga cikinsu ce ta ƙara sakin fuska, cikin annuri ta ce
"Ni sunana Lanti, wannan kuma Zuwaira. Amaryarmu ce muka kawo mu damƙa miki ita amana, sunanta Fatima Binta. Yarinya ce ƙarama da take da buƙatar kwaɓa, tare da bambance mata ja da fari. Mun bincika a duk eriyar nan an tabbatar mana da ke ce mace mai dattako da kame kai, an kuma shaida mana kina takaba saboda mai gidanki bai jima da rasuwa ba. Wannan dalilin ne ya sa muka ga cancantar mu damƙa amanar Binta a gare ki, ko ba komai kin san me duniya take ciki, sannan za ki kula mana da ita yanda ya dace. Ki ɗauke ta tamkar 'yar'uwarki ta jini, ina da yaƙinin za ta girmama ki tamkar Yayarta ɗaya uba ɗaya. Jiya aka kawo ta, ƙila ba za ki rasa jin labarin amaryar da aka kawo gida biyu tsakaninku ba, to ita ce. Muka tsallake gidaje muka zo gare ki saboda halayenki na gari."
Murmushi Goggo ta saki bayan ta yakice mayafin amaryar, fuska a sake ta ce
"Ina mata...barka da zuwa."
Don a wancan lokacin maganarta ba ta lalace ƙwarai ba, bebiya ce amma ba sosai ba, ba ma kowa ba ne zai iya gane ita bebiya ce ba.
Sun ɗan jima a haka har Safiyya ta tashi bacci, a lokacin tana da shekara uku, ta gaishe su sannan suka yi wa Goggo bankwana cewa za su koma.

Wannan shi ne mafarin ƙulluwar zumuncin Goggon su Sofi da Binta mahaifiyar Shatu. Ta kai ta kawo har dangin Binta idan sun zo gidan Goggo suke ya da zango saboda yadda take kyautata musu, iyakarsu da Binta su leka mata, mijinta ba mazauni ba ne sai hutun ƙarshen mako yake dawowa, sai ita ma Bintar ta dawo nan duka su jibge cike da nishaɗi.

Bayan watanni goma da auren Binta cikinta ya shiga lokacin haihuwa. Tun daga nan Goggo ta dawo da ita gidanta, sai idan mai gidanta zai dawo Jumu'a sannan ta koma nata gidan.
Da wani yammacin Alhamis, Goggo ta tasa Binta gaba sai ta motsa jikinta, ita ko sai tunzuro baki take wai ta gaji, Goggo ta ce a hakan dai za ta daure ta tashi Safiyya 'yar shekara huɗu na taya ta har sai sun yi zarya daga ƙofar gida zuwa ɗakin Goggo sau ashirin, duk suka sa dariya. Tana cikin motsa jikin ne ƙanin mijin Binta ya shigo cikin tashin hankali, muryarshi da alamun kuka yake shaida musu da mummunan hatsarin motar da Adamu ya yi, wanda ta sanadinshi har ya rasa rayuwarsa. Caraf sai a cikin  kunnuwan Binta, wanda hakan ya jawo mata naƙudar dole, tana kuka ta duƙe a wurin tana maimaita sunan Allah, kalmar mutuwar Adamu na mata yawo a cikin kunnuwa da ƙwaƙwalwa.
Cike da tashin hankali Goggo ta fita ta yo shatar adaidaita ta dawo, ita da Salim ƙanin Adamu suka cicciɓi Binta, Safiyya biye da su suka shiga napep ɗin tare da nufar asibitin Barau Dikko (Nursing home).
Bayan an karɓi Binta cikin gaggawa aka hau kanta, daga nan kuma aka shaida wa Goggo ai lokacin haihuwar Bintar bai cika ba, ga shi kuma ruwan da yaron yake kwance a ciki duk ya gama tsiyayewa sannan ga zubar jini, don haka dole sai an mata aiki an ciro jinjirin in dai ana son tseratar da rayuwarsu.
Goggo ta ce ita ba ta da damar da za ta ce a yi aikin har sai ta tura saƙo ga danginta can Zaria, idan sun amince sai a yi.
Babu waya balle ta kira, dole wasiƙa ta rubuta, ta tura Salim da takardar ya kai tasha tare da suna da adireshin mai wasiƙar, Salim ya biya kuɗin motar sannan ya dawo.
Har kusan awanni uku Binta na cikin wani hali. Ganin haka ya sa malamar jinyar ta sake fitowa inda ta shaida wa Goggo matuƙar aka ɗauki dogon lokaci fa da uwa da jinjirin duk za su iya rasa rayuwarsu. Jin haka ya sa ta ce kawai a yi aikin, tunda ga Salim ƙanin mijinta, shi ma ya ba da goyon bayan a yi. Shi da kanshi ya sa hannu aka shiga aiki da Binta.
Bayan tsayin lokaci aka fito da Binta tare da kyakkyawar yarinyarta lafiyayya. Ba ƙaramin farin ciki Goggo ta yi ba. Ita ta ci gaba da jinyar Binta har zuwa washegari da danginta suka iso daga Zaria bayan saƙon wasiƙar Goggo ya riske su.
Bayan sati ɗaya aka sallame ta. Har a lokacin kullum cikin kuka Binta take, ji take rayuwarta ta zo ƙarshe tunda Adamu ya tafi ya bar ta. Damuwa ta samu matsuguni a cikin zuciyarta.
Da ma kuma iyayen Adamu duk sun rasu, daga Salim kaninshi sai Yayarshi mai aure a Bidda, wadda ita kanta cikin halin talauci take ga tarin yara da duk nauyinsu yake a kanta saboda mijinta ya jima da rasuwa kuma su biyu matanshi ya mutu ya bari.
An saka wa yarinyar Aishatu ne saboda tsarin Adamu da Binta kenan tun yana raye, don haka sai ta cika masa alƙawari. Bayan suna da sati biyu ciwo ya ci gaba da bibiyar Binta babu sassauci, hakan ya sa danginta suka ce za su koma Zaria da ita su kai ta Shika ko za ta samu kyakkyawar kula.
Ranar da suke shirin tafiya jini ya sake ɓalle wa Binta, numfashi ma jawo shi take yi da tsiya, a cikin wannan halin ta damƙa amanar Shatu ga Goggo, sannan ta roƙi mahaifiyarta alfarmar su bar Shatu a hannun Goggo, kewar za ta yi mata yawa. Alabishi zuwa wani lokaci sai su karɓe ta idan Goggon ta yi aure ko kuma Safiyya ta girma.
Duk da hakan bai yi wa iyayenta daɗi ba amma sun amince mata saboda halin da take ciki. A ƙarshe ta dora da
"Ni na san rayuwata ta zo ƙarshe, wannan ciwon ba na tashi ba ne. Anti Hafsa ga amanar Shatu nan na damƙa miki, ba sai na faɗa miki ki kula da ita ba don na san za ki yi ɗin. Allah Ya ba ki abin da za ki ciyar da su da tufatar da su. Na gode sosai da ƙaunar da kika nuna min..."
Ba ta kai aya ba Goggo ta doɗe mata baki tana sakin kuka mai ƙarfi.
"Ki...ki daina...ki daina irin wannan maganar Binta. Za ki...za ki warke...za ki raini Shatu da hannunki."
Cikin murmushi mai haɗe da hawaye Binta ta gyaɗa kai kawai tana ɗauke dubanta daga gare su.
Kafin mahaifiyarta ta je ta ƙarasa tattara kayanta ta dawo har rai ya yi halinsa, Binta ta rasu, ta bi mijinta Adamu, bayan rasuwarshi da sati uku.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now