Page 7

170 28 0
                                    

BABI NA BAKWAI

Ranar asambili aka kira Safiyya da sauran mutum biyun da suka wakilci makarantarsu, tare da manyan kyaututtukan da suka samu. Principal ta gabatar da su tare da jinjina musu sannan ta ƙara ƙarfafar guiwar sauran ɗalibai a kan su yi koyi da waɗannan yaran, musamman ma 'yar ƙaramar cikinsu da take JS1 kuma ita ta fi burge kowa a wurin.
Sannan daga ƙarshe ta ce,
"In shaa Allahu nan ba da jimawa ba ɗaya daga cikin ɗaliban wannan makaranta za ta zamto cikin wakilan ƙaramar hukumar Zaria, inda za a yi gagarumin debate da other local governments a Kaduna. Safiyya Usman Baba ita ce za ta zama wakiliyar makarantar nan, sannan mutum biyu daga other schools da suka zo na biyu da na uku. Muna fatan Safiyya za ta ɗauko ma Zaria kambun girma."
Daga haka ɗaliban suka tafa sannan aka kawo ƙarshen asambili ɗin. Tun a hanyar zuwa aji ɗalibai sai kallon Safiyya ake ana jinjina wa ƙoƙarinta.
Amira ta kalli Safiyya da ke ta murmushi ita ɗaya ta ce
"Kuma yanzu Sofi wai sai ki wakilci Zaria bayan kuma a Kaduna kike? Hm uhm ai wallahi idan ni ce Igabi local government zan mawa tunda a can nake."
Safiyya ta harari Amira ta ce
"Yo dilla can ai ni ma ina da alaƙar da Zaria tunda dai a nan second parents ɗina suke. Besides, ni makarantata zan ma aiki ba garinmu ba."
Amira ta jinjina kai kawai tana sauraron Safiyya.

A ɓangaren su Shatu kuwa, tunda suka koma gida take murmushi, wani irin nishaɗi take ji ganin yadda 'yar'uwarta ta nuna bajinta a gaban dubban mutane.
Anti Fati ta kalli Umma cikin mayar da hankali ta ce,
"Ni kuwa Umma wani tunani nake yawan yi. Kamar bai kamata ba a ce duk wani abu da ya shafi Sofi mu ne a kan gaba ba, bayan kuma mahaifiyarta na raye. Kar ta ga kamar muna nuna mata iko a kan yarinya saboda muna taimaka mata."
Umma ta jinjina kai, ita kanta ta yi wannan tunanin, musamman ma a kan wannan muhawarar da aka yi, komai lalacewa ya kamata a ce mahaifiyarta tana wurin domin ita ma ɗin ta yi alfahari da tilon ɗiyarta."
"Maganarki gaskiya ne Fatima. Amma ta yaya kike ganin za mu ɓullo wa lamarin? Ba na so yarinyar ta ga kamar muna ƙoƙarin janye ta daga jikinmu ne. Hafsatu ta yi mana komai a rayuwa; ta kular mana da Binta sadda take raye, sannan kuma ta riƙe Aishatu ba tare da nuna bambanci tsakaninta da ɗiyar cikinta ba. Ba zan so nuna wariya ga tata ɗiyar ba."
Anti Fati ta sauke ajiyar zuciya. Gaskiya ne maganar Umma. Sai dai kuma Goggo na da haƙƙi sosai a kan ɗiyarta, kuma ya kamata su ba ta wannan haƙƙin nata.
Cikin sanyin murya ta ce
"Abu ɗaya za mu yi Umma. Mu shirya mu tafi Kaduna tare da wannan kyautar da gwamna ya ba Safiyya, mu ba ta labarin duk abubuwan da suka faru a wurin na tabbata za ta ji daɗi, sannan jin daɗin zai taushe haushin rashin saka ta a cikin al'amarin. Kuma duk runtsi term ɗin nan idan su Sofi sun samu hutu komai nacin da za ta yi kar mu bari ta zauna ba tare da ta je wajen mahaifiyarta ba. Gwara mu haɗa su ita da Shatu su je su yi hutunsu a can, in ya so idan hutu ya ƙare sai su dawo, mu yi mata duk wani abu da ya kamata sannan a mayar da ita makaranta."
Sosai Umma ta ji daɗin shawarar Anti Fati. Ranar Jumu'a kuwa suka shirya suka tafi Kaduna.

Da Anti Fati ta fara ba Goggo labarin muhawarar ta su Safiyya kasa rufe bakinta ta yi. Farin ciki ya yi babakere tsakanin ƙirjinta, har yana tona asirin kanshi a saman fuskarta. Nishaɗi sosai ta shiga kamar yadda suka yi tsammani. Tana kunna rediyo sosai tana saurare, sannan ta ji labarin muhawarar, sai dai da yake ita bebiya ce ba fahimtar abun sosai take yi ba, kawai naciyar jin rediyon ne.
Ashe wai har da 'yarta cikin waɗanda suka gabatar, ita ce ma ta zamo gwarzuwa. Wannan abu ba ƙaramin daɗaɗa zuciyar Goggo ya yi ba.
Daga nan Anti Fati ta buɗe ambulan ɗin, a nan suka ci karo da abun mamaki; domin kuwa dalar Amurka ne masu tarin yawa, da suka ƙirga dala dubu biyu ne a ciki. Dalilin da ya sa gwamnan da ya tashi bada kyautar bai nemi shugabar makarantar su Sofi ba sai ya nemi iyayenta, gudun kar su cinye mata haƙƙi, domin kuwa ita ya ba, ba makarantarsu ba.

Da suka tashi tafiya babu yadda Goggo ba ta yi ba da su a kan su ɗauki wani abu daga cikin kuɗin amma firfir suka ƙi. A ƙarshe da ta fasa musu kuka sai Umma ta zari dala ɗari ta miƙa wa Anti Fati ta ce wannan ma sun isa, Allah Ya sa musu albarka.
Har bakin mota Goggo ta raka su sannan ta dawo. Ta kalli kuɗin ta tsura musu idanuwa tana sakin hawaye, wai waɗannan maƙudan kuɗaɗen duk albarkacin ɗiyarta ne suka same su.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now