Page 8

168 23 0
                                    

BABI NA TAKWAS

Jin shiru babu amsa ya sa Sofi ta ɗauka ko Goggo ba ta fahimce ta ba ne, sai ta maimaita,
"Goggonmu kuɗina da na samu na debate da na yi, wanda gwamnan Kaduna ya ba ni, ina son su duka, zan sake sababbin kaya ta yadda duk Rigasa za a shaida Sofi is now a big girl. Na dai san babu abin da za ki yi da su tunda dai ke kuɗi ba sa gabanki."
Murmushin takaici Goggo ta yi, kafin ta ce
"Ke ma...ke ma da kike...ƙayamai yayinya...kin san kuɗi...kin san...su suna gabanki...balle ni da na haife ki...safiyya?"
Gaban Sofi ne ya faɗi jin amsar da Goggon ta ba ta. Sai ta saki gajeren murmushin da iyakacinshi bisa leɓonta. Ta ce
"Ai Goggo ke na ga in dai kika samu na abinci shi kenan an wuce wajen. Sutura ma daga sallah sai sallah kike mana, alamun duniya ba ta gabanki kenan."
Dafe haɓa Goggo ta yi tana sake bin Sofi da kallo.
"Beside, kuɗin nan dai nawa ne, ni aka ba ba ke ba..."
"Haba Yaya Sofi!"
Shatu ta faɗa cikin ɓacin rai tana kallon Safiyya da ke neman wuce gona da iri.
"Goggon kike faɗa ma haka?"
Ta ɗaga ma Shatu hannu tana cewa,
"Ke fa banza ce Shatu, ba kya son gaskiya ko alama. Ke kanki kin san haƙƙina ne, ni ya kamata in yanke hukuncin abin da zan yi da kuɗina."
Gyaɗa kai kawai shatu ta yi, yarinya mai ƙarancin shekaru amma ta san daidai, ta san cewa babban kuskure ne 'yar'uwar tata take aikatawa. Domin kuwa an sha jaddada musu muhimmancin uwa tare da haƙƙoƙinta a kan 'ya'yanta.
"Na kashe...kuɗinki...na kashe Safiyya. Ki ɗauko...ki dauko 'yan...sanda...Ko kuma...KASTLEA... su...kama ni."
Daga haka Goggo ta fice domin nema musu abin da za su ci.
Saƙaƙa Sofi ta yi kamar dolo a cinema, tana bin Goggo da kallo. Fatanta kar zancen goggon ya tabbata, domin kuwa in har da gaske ta kashe kuɗaɗen nan to ita kam ta cuce ta. Wannan fa shi ne kura da shan kiɗa...
Ta yi kwafa tana kwashe jakar kayanta haɗe da nufar ɗakinsu.

Tun daga wannan lokacin Sofi ta tsiri fushi da ɓacin rai a cikin gidan. Daga Goggon har Shatu babu wanda take kulawa cikinsu. Iyaka a girka abinci ta ci. Da yamma ta fice yawonta har sai an yi maaghrib sannan ta dawo. Ba ta da aiki sai shiga cikin manyan matan unguwa, tana bin bakunansu da kallo idan suna magana, shi ya sa ta iya juya harshe tare da salo da hilimin maganganu.
Daga haka har hutunsu ya ƙare suka fara haramar komawa.
Sababbin kayan makaranta Goggo ta ɗinka musu har Shatu, sannan ta haɗa musu sha tara ta arziƙi ta ce su tafin ma Umma da shi.
Cikin ɓacin rai da gunguni Sofi ta ce
"Da ma tunda mutum ba kuɗinsa ba ne ai dole ya yi ta facaka da su."
"Me...me kika ce...Safiyya?"
"Ban ce komai ba ni."
Ta ba Goggon amsa tana barin wurin.
Gyaɗa kai kawai Goggo ta yi, a cikin zuciyarta tana ma 'yar tata fatan Allah Ya shirya ta, Ya ganar da ita gaskiya tun kafin lokaci ya ƙure mata.

BAYAN SHEKARA BIYAR

Abubuwa da dama sun faru a cikin waɗannan shekarun. Daga ciki akwai zama cikakkiyar budurwa da Safiyya ta yi, budurwa mai ji da kanta fiye da yadda take a baya. Tun daga kan tsararrakinta har zuwa kan malamai duk kallon wata ɗiyar masu kuɗi suke yi mata, saboda har a lokacin babu wanda ya taɓa sanin cewa ba gidansu ɗaya da Shatu ba. Motocin da ake zuwa ɗaukar Safiyya kansu abun kallo ne balle kuma ƙwarjinin da take da shi. Shatu ma ta zama budurwa sosai amma ita ba makarantar kwana take ba nan wata makarantar kuɗi ce ta je-ka-ka-dawo take zuwa, sai dai lokacin ziyartar ɗalibai kawai take je wa Sofi.
A yanzu haka Safiyya suna SS 3 ne, manyan makaranta, kuma ita ce shugabar ɗalibai.

Cike da yauƙi take tafiya ita da Amira, biye da su yara biyu ne 'yan js 2, ɗaya hannunta riƙe da jakar abincin Sofi, ɗayar kuma ƙaramin bokiti ne hannunta kuma duk na Safiyyar ne.
Tun daga bakin gate ɗin hostel Sofi ta cire hijabinta ya zamto daga ita sai burgujejen wando da ɗagaggiyar rigar uniform, kanta ko ɗankwali babu sai baza gashin da ta yi ya sauka har bisa kafaɗarta.
Daga nesa wata metiran ta hango su, da hannu ta yi musu alama da su zo inda take sai dai Sofi na kallon ta ta ɓata rai alamun ba ta son zuwa. Metiran ɗin ba ta fasa kiran su ba daga inda take zaune gaban new blue.
"Ai fa idan ba mu je ba waccan jarababbiyar matar ba za ta ƙyale mu ba."
Sofi ta faɗa tana ɓata fuska.
"Mu je Amira mu ji me take son faɗi. Idan kuma na ji akwai kuskure a maganarta ni na san maganinta. Don na lura tun ranar da aka kawo ta makarantar nan duk ta bi ta saka min ido, komai nake tana ankare da ni na rasa ko uwar me na tsare mata. Mtswww!"
Hanyar new blue ɗin suka nufa. Amira ce ta gaishe da matar sai yaran da ke biye da su amma Sofi ko ɗaga kai ta kalle ta ba ta yi ba.
"Wai ke wace irin fitsararriyar yarinya ce wacce sheɗan ya fitsare wa kai? Ina lura da ke kwata-kwata ba kya son rufe gashinki. Surar jikinki ma kanta ba ki damu da ki suturce ba, ke ko tsoron shaiɗanu ma ba kya yi."
Shiru Sofi ta yi tana kallon ta sama da ƙasa. Tana ji ta ci gaba da faɗin
"Ko da me kike taƙama Safiyya an yi dubunki ba kuma za a gama ba a kanki. Idan rashin kunyar ne ma akwai waɗanda suka zarce ki. Idan kina taƙama da kuɗi to ke ba kowan kowa ba ce a kan wasu. Ilmi ma kafin ki same shi wasu ne da shi suka koya miki har kika iya. Gwara ma ki rufa wa kanki da rayuwarki asiri tun wuri ki san me kike yi. Wallahi idan lokaci ya ƙure miki za ki yi da na sani, da na sani mara amfani."
Sai da ta kai ƙarshe sannan Sofi ta ɗan motsa bakinta kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma can ta ce
"Thank you."
Ta yi gaba kawai ba tare da ta tsaya sauraren wata maganar ba.
Bayan ta bar wurin metiran ɗin ta yi kwafa tana bin ta da kallo.
"Yarinya in dai duniya ce ta ishi kowa riga da wando, kya yi kya gama, wanda bai zo cikinta ba ma jiran sa take yi."

Safiyya tunda suka tafi take sababi.
"Kamar akwai hassada a kalaman matar can. Whatever dai nan gani nan bari karkataccen rawanin mai gari. In shaa Allahu nan da watanni kaɗan za mu tafi mu bar musu makarantar sai kuma in ga wadda za a saka wa ido."

Washe gari a asambili aka gabatar musu da sababbin 'yan bautar ƙasa. Kallon su kawai Safiyya ke yi tana yatsina, tamkar wadda ta ga ɗanyen kashi, saboda ita gani take ta fi ƙarfin ɗan bautar ƙasa ya koyar da ita, kamar ilminta ya fi ƙarfin nasu. Sun sha hawa sama su fado ita da 'yan bautar ƙasar, wasu su bar ta, wasu kuma su saka ƙafar wando ɗaya da ita har zuwa lokacin tafiyar su.
Ƙoƙarin nan da take da shi shi yake kuɓutar da ita, shi kuma yake janyo mata farin jini ga kowa. Sannan uwa uba ga ta da wani irin aji da ƙwarjini na ban mamaki. Ba wani kyau na a zo a gani take da shi ba, sai dai tana da ƙwarjinin da ko haɗa ido da ita ba kowa ke iyawa ba ballantana a yi zancen horar da ita idan ta yi laifi, tun tana jiniya bare yanzu da ta zama babba, ta zama shugabar ɗalibai baki ɗaya.

Tana ji dukkansu suka gabatar da kansu da sunayensu. Bayan sun gama ta fito da takarda a hannunta a gaban asambili ɗin, sai ga mutum biyu ma sun fito suka tsaya daga gefenta na haggu. Sifika aka ba ta, ta ɗan gyara muryarta sannan ta fara da
"Hello and welcome to FGGC Zaria weekly news. I am Safiyya Usman Baba with the latest..."
Daga nan ta ci gaba da nata ɓangaren na news kamar yadda suka saba kowanne sati. Sannan sauran biyun ma suka gabatar da nasu ɓangaren. Daga nan suka sake mayar mata ta yi ƙarƙarewa sannan aka tafa musu suka bar wurin.
Tunda ta fara ya yi kasaƙe yana sauraron ta, duk da baya ta ba su, ba ya ganin fuskarta amma sosai Turancinta da yadda take kalmasa harshe ya tafi da shi, uwa-uba kuma da ta kalmashe takardarta ta yi ƙarƙarewar a cikin ƙwaƙwalwarta ba tare da ta karanta ba, cike da ƙwarewa sannan ta bar wurin ba ta ɗaga kanta ta kalli kowa ba.
"Safiyya Usman Baba."
Ya maimaita sunanta cike da wani irin yanayi da bai taɓa tsintar kansa a cikinshi ba. Bai ga fuskarta ba sai muryarta, sai dai ba ya jin zai iya haƙuri ba tare da ya binciki ko wace ce wannan yarinyar da take neman tafiya da kuzarinsa ba cikin ƙanƙanin lokaci.
Idanuwanshi ba su daina yawo a kanta ba har sai da ya hango inda ta nufa daga can gefe, ba ta ma shiga cikin sauran firifets ba don ita a tsarin rayuwarta ba ta shiga cikin ƙawaye. Amira ce kaɗai ƙawarta duk da ita ma ɗin har yanzu ba ta gama sanin ainahin wace ce Safiyyar ba, hakan ne ma ya jawo tsayintar amintakar tasu.
Tunda ta tsaya yake kallon ta. Hijabinta jar kala ce a maimakon ta sauran ɗalibai da take ruwan ƙasa mai haske, sannan ya ga wasu daga cikin firifets duk da kalar bula ɗin hijabai, wasu kuma tsanwa, amma nata ne kaɗai ja. 'That's means she is special. Oh yeah! The girl is really special. And she deserves to be the special.' Ya maimaita a zuciyarshi.

Bayan an gama asambili an shiga aji Safiyya ma ta nufi ajinsu, saboda ita sam ba ta yarda da wannan yawace-yawacen da firifets suke yi ba na rashin zama aji. Ita ba ta haɗa karatunta da komai ba shi ya sa ma tun farko da aka ce za a ba ta, ta ce ba ta so don kada ma ya shiga cikin karatunta. Amma PC ta ce dole sai ta karɓa saboda ta cancanta. 'She deserves to be the head of the students' PC ɗin ta faɗa mata, don dolenta kuma ta karɓa amma ta ce sai an mata uzuri don ba za ta iya barin darussanta ba ta tafi wata harka ta shugabannin ɗalibai ba.

Bayan ta zauna ta ciro biology textbook littafin rubutunta saboda shi ne darasi na farko da za a yi. Guntun tsaki ta saki sadda ta tuno da assignment ɗin da ba ta yi ba kuma ga shi yanzu za a karɓa. Sam jiya ba ta samu kanta ba saboda extra lesson da take yi ma wasu ɗalibai da suka roƙe ta saboda suna son su ci jarabawar qualifying ɗinsu.
Tana cikin yi ne ya shigo, sanye da kayan 'yan bautar ƙasa ya karkace hular kayan ta hana-sallah ta kalli baya. Duk suka miƙe suka gaishe shi. Ba tare da ɓata lokaci ba ya ba su izinin zama. Sai dai abin da ya ba shi mamaki shi ne ganin yarinya ɗaya ba ta miƙe ta gaishe shi ba kamar sauran, kanta sunkuye a ƙasa tana rubutu, kamar ma ba ta san da wanzuwar shi ba a wurin.
Bayan ya ba su izinin zama ne ta ɗan ɗago fuskarta ta kalle shi. Ta so ta sunkuyar da kanta sai dai daga sadda idonta ya shiga cikin nashi, sai ta nemi duk wani girman kanta ta rasa. Shegen son girman ma babu. Sai wani irin yanayi da ta tsinci kanta a cikinsa wanda ko a mafarki ba ta taɓa jin irinshi ba.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now