27&28

34 3 0
                                    

❤️ *ZUCIYA CE*❤️

*Nana Halima*🌚

*27&28*

Not edited🥺

"Kiyi hakuri Haleema ki daina kuka haka ni nasan wacece ke nasan abinda zaki aikata nasan kuma Wanda baza ki aikata ba share hawayen ki" Uncle ya fad'a yana dafa kanta da yake kan guiwoyin ta tana  kuka sosai. D'ago kai tayi ta share hawayen da yake fuskar ta tace, "Uncle ina Abba na? Ya yafe min ko har yanzu yana fushi dani?." "Mama na Abban ki ya yafe miki yana kuma kewar rashin ki tare da dana Sanin abinda ya aikata miki." "Mama na fa da Aunty Hafsat dasu Yaya Sadik duk suna lafiya?" Ta fada tana kafe shi da ido, "duka suna lafiya kowa kuma yayi kewar ki, ina so ki saki jikin ki Haleema ki zauna a gidan nan kamar kina zaune a gida na domin mai gidan nan aboki nane sosai ki dauka kamar nine in kina tare dashi kin gane?." Kallan sa tayi alamun karin bayani yace,"baza ki koma gida yanzu ba baku zan basu labarin ki ba har sai lokacin da Wanda ya kulla miki sharrin ya dawo ya fad'i abinda ya saka yayi miki Sharrin da har mahaifin ki yayi fushi dake a sannan ne kowa zai gane ke ba fasika bace ba ke Nafi so yayi kewar ki akan rashin aldalcin da yayi miki da kuma rashin bincike da baiyi ba akan ace yana kewar sabida ya Kore ki Dan kin aikata ba dai-dai ba, bazan nuna musu mun had'u ba haka kema kada kiyi gangancin kiran kowa a waya ki kyale su dukkan su sai kowa yasan mahimmacin ki kana Sai ki koma gare su kin gane abinda nake nufi?." D'aga kai tayi murya a sanyaye tace, "Na gane Uncle zan kuma kiyaye insha Allah, amma Dan Allah ka kira Abba na yanzu ina so naji maganar sa kaji." Bai musa ba ya saka hannu a aljihu ya d'auko waya ya danna number sa sai dai tana ta ringing ba'a d'auka ba ya sake kira nan ma ba'a d'auka ba ya kashe wayar ya saka a aljihu yace, "Ki kwantar da hankalin ki zan kira shi anjima zaki ji muryar sa insha Allah, yanzu ki koma ciki ki cigaba da kula da Auta kinga babu abinda mutanen gidan nan basu yi miki na alkhairi ba ki saka musu da alkhairi kema ta hanyar kula da d'an su da kuma matsayin ki na malamar lafiya ki bashi kulawa sosai kinji ko?" D'aga kawai ta yi jikin ta a sanyaye yace, "Tashi kije anjima zan kira ki." Kamar wacce aka zarewa laka haka ta mike ta fice sai a lokacin Uncle ya kalli daddy fuskar sa d'auke da murmushi yace, "Kaga ikon Allah ko? Ashe wacce nake baka labari  ina da tana nan zan bata auren Fahad Ashe tana tare daku ma ba tare da an sani ba." Daddy da mamaki da kuma tausayin Haleema ya cika masa zuciya yace,"yanzu Haleema Yar yayan kace? Kuma nurse ce?." "Yar Yaya nace Wanda muke uwa daya uba d'aya kuma nurse Dan saura watanni ta kammala karatun nata Allah ya saukar mata da wannan iftila'in da ta tsinci kanta a ciki." Jinjina kai Daddy yayi ya sake fadin, "Gaskiya mahaifin ta yayi kuskure babba a wannnan zamanin ko y'arka da gaske ta aikata abinda ake zargin ta dashi ba'a korar ta daga gida sabida silar hakan zai ya saka ta Shiga karuwanci balle bata aikata ba, ta bani tausayi matuka kana ganin ta kaga yarinya mai hankali ko a fuska bata nuna mana bata san kula da Fahad ba sai ma nuna mana da tayi ai lafiya tafi komai koni na yaba da hankalin ta sosai sosai." Ajiyar zuciya Uncle yayi yace,"kaga yanzu kaya ne ya tsinke a bakin ga6a ko da mahaifin ta nine mad'aurin auren Haleema Dan haka yau basai gobe ba in an sakko daga sallar juma'a zan bawa Fahad auren Haleema ta cigaba da kula dashi amma fa in kun amince." Murmushin Farin ciki Daddy yayi yace, "mu ai mun riga mun amince babu Wanda zai ja da wannan maganar daman abinda yasa suka ki rashin sanin asalin Haleema yanzu amincewar ta muke bukata kawai, kuma Kasan Allah tunda naga Haleema nake ganin kamar tana min kama da Wanda na sani Ashe da kai take kama." Murmushi Uncle yayi yace, "Haleema bata da matsala amma duk da hakan ka shiga gida yanzu kayi musu bayani in sun amince sai a turo min Haleeman itama naji ta bakin ta." Da hanzari Daddy ya mike ya fice jikin sa sai tsuma yake sabida farin ciki.
Cikin farin ciki Daddy yayi musu bayanin komai suma suka nuna jin dadin su tare da farin ciki da kuma goyan baya mummy tace, "Ai kawai ka kira shi yazo wannan falon ya tambaye ta a gaban kowa kar a tauye mata hakki." Yayi na'am da maganar Mummy yaje ya tawo da Uncle suka zauna a falo aka kira Haleema ta shigo jikin ta a sanyaye ta zauna a saman carpet uncle yace,"Haleema nasan kin San lalurar da take damun d'aya daga cikin yaran gidan nan kin kuma San da ke kadai ya saba a yanzu, a matsayi na na uba gare ki mun yanke hukuncin aura masa kee shine na kira ki muji ta bakin ki in kinga bakya so kada ki cuci kanki. " _to me zance? A gaban iyayen sa dai bazan ta6a cewa bazan aure shi ba kodan haliccin da suka min a duniyar da ba kowa ne yake taimakon Wanda bai sani ba tabbas in ban amince ba nayi butulci, in na amince tabbas na cuci kaina meye matsayin auren? Da ya warke zake ni shikenan na koma karamar bazarawa? Kuma shi fa auren sa zaiyi ya manta da babin wata Haleema ma a duniya anya zan amince_ "ke muke jira" Uncle ya katse mata tunani ta dago ta kalle shi tace, "Duk abinda ka yanke uncle shine dai-dai". " A'a ki fadi abinda yake ranki zabin ki ra'ayin ki ake so aji bana uncle din ki ba" Daddy ya fada, "babu komai" ta sake fada a sanyaye jikin ta duk ya mutu, "to madallah Alhamdulillah Allah yayi miki albarka, tunda ta amince shikenan bayan masallaci za'a daura insha Allahu, tashi kije" a sanyaye ta mike ta bar wajan zuciyar ta na bugawa da sauri-sauri. Daddy yace,"ina Fahad din ne na ganku a nan?." "Ya samu bacci an kwance fuskar yanzu" Abbah ya fad'a cikin fara'a. "To masha Allah, yanzu Ku tashi muje masallaci lokaci yana tawowa." A tare suka mike suka fita. Bangaren mummy farin cikin da take ciki ba'a cewa komai wani irin nishad'i take ji ko babu komai za'a zamu maganin matsalar Fahad ta biyu. Haleema kuwa bata wuce ko ina ba sai bayan gidan kawai ta fashe da kukan da bta san dalilin sa ba. Kamar daga sama taji ance, "Haleematus Sadiya". Wni irin bugu kirjin ta yayi ta juyo da sauri ta kalli shi bata San lokacin da ta saki k'ara ba ganin fuskar Fahad a bayyane a tsaye a kusa da ita yana kiran sunan ta, hannu ta saka ta murza idon ta ta bude amma still shi take gani a gaban ta, wani irin rawa jikin ta soma kamar mazari ta tattare rigar ta zata gudu caraf ya kama hannun ta duk da ba lafiya gare shi ba haka ya jata tana tirjewa har ya kaita falon sa. Zama yayi ya nuna mata waje alamun ta zauna ita kam kallan sa kawai take idon ta a waje sabida tashin hankalin, ganin taki zama sai ya mike shima ya tsaya kusa da ita ya zaro ido kamar yadda ta zaro itama, d'aga kan da zatayi idon ta ya Sauka akan photon sa shida Hafsat sai dai yayi k'ura ba'a ganin fuskar Hafsat din sosai ai kawai sai ta zauna a kan tayel tare sa fashewa da wani marayan kuka. Yadda tayi shima haka yayi tana kuka yana kuka. Bata San tsahon lokacin da ta d'auka a wajan ba kamar an tsungule ta ta mike tsaye tare sa fadin, "aure fa" sai kuwa ta ruga a guje ta fice daga falon shi ma ya bi bayan ta amma ya kasa gudu ganin tayi nisa sai ya zauna a wajan yana kuka yana kiran sunan ta, a bakin gate sukayi kaci6us da Uncle tana hakki tace,"Kada a d'aura auren nan Uncle". Murmushi yayi yace,"Auren kam tsakanin ki da Fahad ya d'auru ga sadakin ki ma" ya fad'a yana mik'o mata. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ta furta tana dafe kai sabida biyu-biyu take gani.


Ayyuka sunyi min yasa ne wallahi shiyasa kwana biyu ake jina shiru🤒 yanzu ma katse wani abun nayi na samu nayi wannan sai dai ayi hakuri babu yawa.


Comments and share.

❤ZUCIYA CE❤Место, где живут истории. Откройте их для себя