Page 31&32

48 5 2
                                    

❤️ *ZUCIYA CE❤️*

*Nana Halima*🤪

*31&32*

Nufar d'akin suke faduwar gaban Hafsat ta tsananta runtse ido tayi ta bud'e dai-dai lokacin da Mummy ta bud'e kofar da zata sadaka da falon Fahad, tana saka kafar ta a falon faduwar gaban ta sake tsananta jikin ta har rawa yake sabida yadda take jin zuciyar ta na karkarwa, "Ku zauna mana" Mummy ta fad'a cikin kulawa tana kallan su kafin ta karasa inda Fahad yake zaune ya juya musu baya kamar bai ji shigowar su ba, "Fahad ka juyo Ku gaisa sun zo duba ka" Mummy ta fad'a tana dafa kafad'ar sa, a hankali ya juyo ya d'aga ido ya kalle su cikin sa'a idon sa ya fad'a cikin na Hafsat, kasa d'auke idon yayi daga kanta yana juya idon kamar mai tunani kafin ya janye idon daga kanta ya mayar kan tv da take mak'ale a bangon Falon, Hafsat da take ji kamar taje ta rungume shi ta fashe da kuka mai sosa zuciya sai a lokacin ta lura Mummy bata falon, "ki daina kuka Hafsat Allah zai bashi lafiya" Khamis ya fad'a cikin tausayin duka su biyun dan harga Allah Fahad ya bashi tausayi matuk'a. Mikewa tayi ta isa gaban sa ta tsuguna tace, "Fahad ka kalle ni ka tuna dani dan Allah ko zaka manta kowa bai kamata ace ka manta ni ba Fahad ka tuna nice Hafsan ka." D'aga ido yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa ya cigaba da kallan sa, hannu na rawa ta d'auki wayar ta ta lalubo hotunan  da suka d'auka tare tace,"kalli ka nice da kai Fahad ka tuna mana nice wacce kake so kake kuma burin mallaka matsayin mata dan Allah ka tuna ni tun kafin zuciya ta ta buga" ta fad'a tana sake fashewa da sabon kuka. Kallan wayar yayi kamar yadda ta buk'ata ya zubawa hoton ido saurin dauke kai yayi ya runtse ido wani gumi ya shiga keto masa jikin sa ya soma rawa ya dafe kansa da hannun sa sabida barazanar tarwatsewar da yake yi ya saki k'ara yana jujjuya kai, hankalin Hafsat ya sake tashi ta sake rudewa ganin halin da ya shiga tana kuka tana fad'in,"Fahad me ya faru?." Amma ina baya ma sauraran ta sabida yadda kansa yake wani irin tafasa ji yake kamar ya cire shi ya ajjiye. Dai-dai lokacin Mummy ta shigo ganin halin da yake ciki Hankalin ta ya tashi ta kira Abbah a waya Allah ya saka yana daf da gidan yana zuwa ya had'a allura yayi masa bacci ya d'auke shi har lokacin Hafsat kuka take. Kallan ta mummy tayi cike da tausayawa rana da farko da taji Hafsat har zuciyar ta ta karasa gare ta tace, "Ki daina kuka kinji addu'a zaki cigaba da yi masa Allah ya bashi lafiya." Da kai ta iya amsawa sabida yadda kukan yaci karfin ta baza ta iya magana ba.
Abbah ya kalli Mummy yace,"Mummy ba na fada kada a dinga barin sa yana kokarin tuna baya ba? Wannan kokarin tunanin da yake zai iya shafar kwakwalwar sa fa, ya kamata a kula duk lokacin da yake irin wannan tunanin ayi Sauri a kawar masa dashi." Mummy bata amsa ba tayi shiru kawai sabida tausayin Hafsat da shi kansa Fahad din ya cika mata Zuciya, "Ku koma falo Mummy sabida ba'a San hayaniya tunda ya samu bacci, ina Haleema take?" Abbah ya fada yana d'an kalle-kalle. "Ban ganta ba nima ina tunanin tana bandaki ne." Babu Wanda ya sake magana tare suka dawo falo Mummy nata rarrashin Hafsat. Khamis yace, "Mummy mu zamu wuce jirgin karfe sha biyu zamu bi mu koma Allah ya kara lafiya" ya fada yana mikewa tsaye, "haka zamu tafi Baku ci komai ba?". " Babu komai Mummy ai duka d'aya ne." "To shikenan angode Allah ya bar zumunci". Har waje mutanen gidan suka rako su aka saka driver ya kaisu Airport. Haleema da take cikin bandaki ta dinga tsintar kanta da faduwar gaba ba tare da ta San dalili ba haka ta dinga maimaita addu'a a zuciyar ta har ta gama wanka ta fito ta shirya ta dawo falo ta sami Fahad a kwance yana bacci, Abbah da Yaya da suke tsaye a kansa ta tsuguna har kasa ta gaishe su suka amsa da fara'a Abbah yace,"Haleema kada ki dinga Barin sa yana tunani da kinga alamun ya fara tunani kiyi sauri ki kawar masa dashi in ba haka zai samu matsala sosai a kansa." "Insha Allah za'a kiyaye". " Yauwa Allah ya taimaka." Daga haka basu sake magana suka fita suka barta dashi.

After some day's.

Cikin kwanakin Fahad ya saba da Mummy har ya kanje wajan ta ba tare da Haleema ba a lokacin har an kwance daurin hannun sa,fitowar ta daga wanka kenan daga ita sai towel k'arami a jikin ta dake tasan yana wajan Mummy shiyasa ta fito da towel in yana nan sai dai ta saka hijjabi ta fito, tana tsaka da shafa ya bud'e kofa ya shigo ta zaro ido tana kallan sa, tunda ya shigo yake kallan ta ya kasa dauke ido a kanta yana sauke ajiyar zuciya a hankali saurin daukar hijjabi tayi ta saka dake dogo ne har kafar ta ya rife ba tare da ta dauke ido daga kansa ba, ba tare da yace komai ba ya dawo kan gadon ya zauna ganin hakan ya saka ta dauki abinda zata bukata ta bud'e bandaki ta shiga ya lumshe ido sabida wani irin murd'awa da cikin sa yake masa. Sai da ta shirya tsaf sannan ta fito ba tare da ta kalli inda yake ba ta nufi inda akwatin kayan ta Dan ta ajjiye hijjabin hannun ta, numfashin sa da yake fita da k'arfi ya saka ta juya da sauri ganin sa tayi a kwance ya rike ciki yana juye-juye a kan gado, cillar da hijjabin tayi ta nufi inda yake a rud'e take fadin,"Fahad! Me ya same ka?" Ta fad'a tana jijjiga shi cikin tashin hankali, a lokacin Fahad zafin ciwon da yake ji ya hana shi ko magana yayi yadda take jijjiga shi ba karamin ciwo yake k'ara masa ba sai ya sake lumshe ido cikin rashin sanin ina zaice yana masa ciwo, jin yayi shiru ya sake sawa ta rud'e hawaye na bin idon ta ta d'ago shi ta kwantar a cinyar ta tana sake girgiza fuska sa amma idon sa a lumshe yana sauke numfashi dakyar, "me ya same ka? Ina ne yake maka ciwo? Dan Allah kayi magana." Duk abinda take fad'a yana jin ta amma azabar da take ratsa shi baya tunanin ko nuni zai iya yi mata balle yayi magana, hannun sa ya saka ya zagaya dashi bayan ta ya rike kugun ta gam zuwa lokacin ci jikin sa har ya soma rawa ya cize baki sabida wata irin kullewa da marar sa tayi bai San lokacin da ya sake kankame Haleema ba zazzabi ya rife shi sosai,kuka take sosai cikin rashin Sanin abinda zatayi k'okarin mikewa take dan sai a lokacin ta dabarar taje ta fadawa Mummy ta yunk'ura zata tashi ya sake riko ta yana goga kansa a cinyar ta sabida bala'in ciwo.Motsi taji a falo cikin d'aga murya tace, "dan Allah a shigo a taimaka mana." Khadeeja da Mummy ta aiko ta ta kawo abinci taji abinda Haleema take fad'a cikin hanzari ta bud'e kofar d'akin ta shiga, "Aunty Khadeeja Fahad" ta fad'a tana kuka tana sake rike k'ansa da ya kifa shi a cinyar ta,"Subahanallahi Haleema me ya same shi haka?" Khadeeja ta tambaya a rud'e tana karasowa wajan. Girgiza kai haleema take amma ta kasa furta komai sabida kukan da yaci karfin ta, wayar hannun ta ta kira Mummy ta sanar da ita babu jimawa suka zo gabadayan su suna tambayar lafiya,  Abbah ya k'arasa wajan da Fahad ya yake ya tab'a jikin sa da sauri ya d'auke sabida yadda jikin sa yayi zafi  sosai, kallan su Mummy yayi da suke tsaye hankali a tashe baice komai ba ya fita, babu Wanda yayi magana babu abinda ake ji a d'akin sai kukan Haleema da nishin da Fahad yake. Abbah ne ya dawo hannun sa d'auke da sring yana zuwa wajan da Fahad yake yayi masa allura kafin ya kalli Haleema cikin tausayawa ganin yadda take kuka yace,"Ki daina kuka zai samu lafiya insha Allah." Ajiyar zuciya take saukewa tana jin rikon da yayi mata yana sassautawa alamun ya samu bacci. Juyawa Mummy tayi ta fita sauran ma suka bi bayan ta har falon ta aka bar Haleema da Fahad a d'akin, "Abbah me yake damun sa haka?." "Mummy kamar yadda kuka sani ne matsalolin da guda biyu ne wannan itace matsalar da aka fad'a." Shiru Mummy tayi dan ta gano inda maganar ta dosa cikin sanyin jiki ta shiga d'aki ba tare da ta ce komai ba, Khadeeja ta kalli Abbah tace,"Kana nufin akan matsalar ciwon marar nan nasa ne?". "Eh shine wannan ma ai ciwon marar ne ya saka shi a wannan yanayin kina ganin yadda yasha wahala sabida a yanzu bashi da hankalin da zai fahimci me yake damun sa shidai kawai yasan yana jin bak'on yanayi a tare dashi." Yaya da yake zaune a gefe yace,"to indai haka ne me amfanin auren da aka masa? Hala sabida wannan matsalar ya saka akayi auren  to amma gashi babu amfanin da auren yayi akan matsalar." Ajiyar zuciya Abbah yayi yace,"in ka fahimta yanzu Fahad dai-dai yake da yaro dan shekara biyar Wanda bai San me ake kira da aure ba dole bai San yadda zaiyi wai har ya samu abinda yake so ba, mafita d'aya ce shine ta hanyar matar tasa sai dai ita ta taimaka hakan ta kasance in na haka ba ciwon da zaiyi na gaba wallahi sai yafi wannan." Khadeeja tace,"insha Allah bazai sake faruwa ba zan sami Haleeman nayi mata bayanin komai duk da Abu ne mai wahalar gaske a wajan ta amma mijin tane ai". "Ni sai nake ganin kar taga kamar mun cika san kanmu da yawa Mahmah, an daura mata aure dashi ta amince ta yadda zata kula dashi kuma yanzu mu bijiro mata da wannan maganar? Anya mun mata adalci?". "To Abbah ya za'ayi? Wannan shine mafita kawai kace zan mata bayani ta yarda zata fahimta." "To shikenan Allah ya kara lafiya, ni bara naje masallaci" daga haka suka fita ita kuma ta nufi d'akin Mummy.
A zaune ta same ta tayi shiru ta zauna kusa da ita tace,"Mummy tunanin me kike yi haka?." Ajiyar zuciya tayi tace"Khadeeja tunanin Fahad nake." "Mummy insha Allah matsalar zata zo karshe ni da kaina zan samu Haleeman nayi mata bayani yadda zata gane." Mummy ta kalli Khadeeja tace,"Khadeeja Haleema yarinya ce mai hankali da nutsuwa da kuma kunya tayi mana halacci da yawa a cikin rayuwar mu bana so a takura ta bana so muso kanmu da yawa fa." "Mummy Fahad a yanzu mijin tane babu wacce ta cancanci ta taimaka masa a halin da yake ciki sama da Haleeman, Mummy inda Fahad yana cikin hankalin sa a yanzu da babu Wanda zaiji maganar rashin lafiyar nan tasa da yanzu ya samawa Kansa mafita a wajan ta amma Mummy a yanzu fa bai san komai ba in akace ina ne yake masa ciwo a yanzu bazai iya fad'a ba sabida yanayin da yake ciki inda wacce ta cancanci ta taimaka masa a yanzu to Haleema ce, ki kwantar da hankalin ki ai tasan abinda take yi tunda tana da karatun addini tasan hakkin sa da yake kanta."
"Wannan dalilin da kika ce baya cikin hankalin sa ya sa nake tausaya mata Allah kadai yasan irin wahalar da zata sha a hannun sa tunda bai san ya kamata ba a yanzu bai san kuma taimakon da zai mata ba." Khadeeja tayi shiru kafin tace,"babu komai insha Allah, ki kwnatar da hankalin ki bara naje na same ta" tana gama fadar hakan ta mike ta fice Mummy ta bita da kallo.
Haleema kuwa ta samu ta zame jikin ta ta dawo falo ta zuba uban tagumi tana hawaye Khadeeja ta shigo d'akin da sallama. Saurin goge hawayen tayi ta amsa tana kallan ta, a kusa da ita ta zauna ta dafa ta tace,"yame jikin Haleema?." "Da sauqi yayi bacci ma ai" ta bata amsa murya a dashe. "Amma Haleema ya akayi hakan ta faru? Ina nufin daman yau da ciwon ya tashi ne? Na ganshi a wajan Mummy dazu garau dashi." Sai da ta goge kwallar da ta zubo mata tace,"lafiya lau ya shigo d'akin lokacin na fito daga wanka kafin na saka kaya na ganshi a wannan condition din." Murmushi Khadeeja tayi tace,"a matsayin ki na mace a kuma matsayin ki na malamar lafiya baki gane dalilin ciwon nasa ba?". Haleema tace,"ban fahimci komai ba sabida ya kasa fada min ina ne ma yake masa ciwo." "Ciwon Mara ne Haleema". Damm gaban Haleema ya fad'i ta d'ago suka hada ido da Khadeeja ta d'aga mata gira tace," eh ciwon Mara kuma yanzu kin fahimci abinda ya kawo masa shi ko?". Sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, rike hannuwan haleema tayi tace,"Haleema nasan ki fahimci cewa ganin da yayi miki da towel ne ya saka shi a wannan yanayin, kamar yadda na fada miki Haleema Fahad yana buk'atar taimakon ki nasan kina bukatar lafiyar sa tunda gashi har yanzu kuka kike akan abinda ya same shi, Fahad mijin kine kin san hakkin sa da yake kanki duk da baya cikin tunanin sa amma wannan hakkin yana nan a wuyan ki a yanzu kece maganin da zata magance matsalar da take damun sa, nasan Abu ne mai wahala Haleema a matsayin ki na budurwa amma ki duba halin da yake ciki sabida an tabbatar mana da cewa in ciwon ya sake tashi to tabbas xaifi na yau illah shiyasa Nazo na same ki a yanzu bashi fa wacce zata bashi wannan taimakon sama dake, ba lallai sai ya kai da wani Abu ya shiga tsakanin Ku ba Haleema amma ki san abinda zakiyi ya samu relief" ta d'anyi shiru tare da kallan Haleema tana karantar yanayin ta, murmushi tayi dan ta hango tashin hankali da kuma tsoro a fuskar ta tace,"kada kiji tsoro fa ki kwantar da hankalin komai zai zo da sauki, kar kiga kamar mun cika san kanmu me da yawa wallahi haleema ba haka bane in Fahad ya samu lafiya kema kin samu  dan na tabbata a lokacin zaki san me ake kira da dadin aure zakiyi farin ciki Wanda baki tab'a yi ba kiyi hakuri ki jure ki dauka wannan kamar jabawar kice." Shiru Haleema tayi bata amsa ba Ta cigaba da fadin, "Nasan kin gane komai ni zan koma" ta fada tana mikewa har lokacin kan haleema a k'asa yake ta yi murmushi tace,"Haleema sarkin kunya na fada miki ki dauke ni kamar k'awar ki duk wata matsala taki ki fada min zan taimaka miki" daga haka ta fice tabar Haleema da sak'a da warwara.

******
Cikin kwanakin Hafsat ta rame daman ita ba jiki ta ta koma kamar bulala bata da aiki sai tunani ko a makaranta bata iya komai sai tunani har ya kai ga ta kwanta rashin lafiya, ta koma wata so silent bata shiga harkar kowa kullum tana daki tana kuka.

Abba ne da iyalan sa gabadaya a falo Abba ya kalli wanda yake durk'ushe a gaban sa yace,"to bawan Allah ina jinka." Gyara zama Wanda yake zaunen yayi yace,"Alhaji suna na Dr Nasir d'aya daga cikin likitocin asibitin da yake bayan gidan nan wad'an na zaunen sun sanni ni" ya fada yana nuna Sadik da Khamis. Khamis kallan sa yayi sosai yace,"Tabbas na gane ka Kaine wanda ka karb'i Haleema lokacin da muka kaita asibiti." "Kwarai nine wata magana ce mai mahimmaci ya saka nazo wajan Ku gabadaya." Abba cike da mamaki yace, "Muna jinka." Ajiyar zuciya yayi yace,"tunda nake a aikin asibiti ban tab'a cin amanar mutane ba bai ta6a biyewa zuciya sabida san kud'i nayi aiki mara kyau ba sai akan Yar gidan nan kuma wacce tayi practical a asibitin mu wato Haleema, wato Alhaji tazarar kwana d'aya da ya kama za'a kawo Haleema asibiti aka zo aka same ni aka biya ni akan zasan yarda za'ayi haleema ta fara rashin lafiya sun san asibitin da nake nan asibiti mafi kusa daku nan zaku kawo ta ni kuma ga abinda zance in an kawo ta." Kallan kallo aka shiga yi tsakanin Mama da Abba Sadik yace,"muna jinka." "Ban san ta yaya aka saka ta fara rashin lafiya ba aka kawo ta aka yi sa'a nine akan duty, na fadi abinda yake damun ta guda biyu d'aya Gaskiya ne d'aya kuma karya nake Na fad'a ne kawai sabida an saka ni." Abba da ya k'agu yaji me zai ce yace, "muna sauraran ka." Sai da ya kalle su kafin ya cigaba da fadin,"tabbas a lokacin ciwon zuciya gab yake da kama ta wannan ba karya nayi ba Gaskiya ne amma magana akan cikin da nace tana dashi wallahi! Wallahi!! Karya nake Na had'a result na k'arya na bayar ne sabida kudin da aka bani, cikin kwanakin nan Allah ya k'ar6i ran mahaifiya ta wasiyyar ta ta karshe a gare ni shine kada na cuci kowa kada a had'a baki dani a cutar da wani ko wata kada na biyewa san zuciya na cutar da wata zuciyar, tun daga lokacin abinda nayiwa Haleema yake min yawo a kai wannan dalilin ya saka Nazo na fad'i gaskiya na kuma rok'e ta akan ta yafe min." Muryar Mama har rawa take tace, "yanzu kana so kace karya kake haleema bata da wani ciki?". Girgiza kai yayi alamun eh yace, " Ko shakka banayi Haleema bata da ciki karya nayi Na fad'a jinin tane ya hau a lokacin shine ya haifar mata da zazza6i sai kuma ciwon da yake zuciyar ta."
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un shine abinda suke furtawa gabad'ayan su, Abba ya dafe kai hawayen suna sakkowa daga idon Mama ma kukan take Sadik ne yayi karfin halin cewa, "Waye ya saka ka wannan d'anyen aiki ?". D'ago kai yayi ya kalle su dukkan su kafin ya sunkuyar da kai yace.......


_Ina jin daga wannan page din zan daina posting WhatsApp zan koma yi a wattapad duk wata Masoyiya ta ta WhatsApp indai tana comments na santa na kuma san sunan ta zan dinga tura mata ta private insha Allah, in kuna san cigaban labarin zuciya ce zaku neme shi a wattapad @Neatlady11 na gaji da rashin comments gaskiya._🙌🏻🙌🏻

Comments
Vote
Share.

❤ZUCIYA CE❤Where stories live. Discover now