❤️ *ZUCIYA CE❤️*
*Neat lady*
*37&38*
Jijiyoyin jikin ta gabadaya ji tayi sun daina mata aiki ko ina ya tsaya cak hatta kwakwalwar ta ta tsaya da aiki jikin yayi bala'in saki ko kwakwkwaran motso ta kasa ta saki jikin ta tana karb'ar sak'on da yake aika mata dashi cikin zafi-zafi, sun kwashe kusan mintina goma a haka ba tare da ya fasa abinda yake yi ba zafin da lips din ta suke mata ya saka ta dawo hankalin ta ta fara k'okarin mik'ewa daga jikin sa amma ta rik'e ta gamm ko numfashi bata iya fitarwa sosai, _Fahad fa wanda zai auri Yayar kine kike a kwance a jikin sa a cikin wannan yanayi,_ wannan tunanin ne ya fad'o mata ta tattaro iyakacin karfin ta zata kwace daga rik'on da yayi mata amma ina k'arfin namiji dana mace ba d'aya bane da ta motsa zai sake rik'e ta, zafin da lips din ta suke ya saka ta fara k'okarin kwace kanta daga rik'on da yayi mata amma kamar kara zuba shi take, kuka ne ya kubce mata hawaye ta fara zuba daga idon ta tana yi tana k'okarin mik'ewa, _Haleema Fahad mijin kine ke kadai ce zaki taimaka masa a cikin wannan halin da yake ciki Barin sa a cikin wannan yanayin kamar kaurace masa ne tunda baya cikin tunanin sa kuma kin san hukuncin wacce ta kwaracewa miji a wajan Allah._ wannan tunanin ya saka hankalin ta ya tashi zubar hawayen ta ya k'aru, "ta ina zan fara?" Shine abinda take maimaitawa a ranta tana hawayen takaici da tausayin kanta. Cikin k'arfin guiwar da tazo mata ta tattaro dukkan dauriyar ta ta had'a waje d'aya ta runtse ido ta fara yawo da hannun ta a jikin sa.
*After 30minutes*
K'okarin mik'ewa take ta kai kanta band'aki amma abin yaci tura ko yaya ta gwada hakan sai taji kamar babu k'afa a jikin ta balle ta har ta iya mik'ewa tsaye, ajiyar zuciya take irin ta wacce taci kuka ya k'oshi idon ta sun kumbura ko bud'e su bata iya yi, agogon da yake manne a jikin bangon d'akin ta kallah lokacin sha biyu dai-dai, runtse ido tayi cikin rashin Sanin abinyi ga azabar da take ratsa ko ina na jikin ta gashi tana so ta mik'e kodan ta gyara kanta ta kuma gyara wajan har shi Fahad din yana buk'atar taimakon ta gashi itama a irin wannan lokacin take buk'atar a taimaka mata amma babu yarda zatayi bata tunanin zata iya Sanar da Mummy abinda yake faruwa shiyasa take k'okarin mik'ewa da Zarar ta tashi zaune zataji kanta yana juyawa sai ta koma ta kwanta take jin dai-dai. Kallan inda Fahad yake tayi yana kwance ya cure waje d'aya yana rawar sanyi kana ganin sa kasan yana tare da zazzab'i mai zafi, Hasbunallahu wani'imal wakil ta fad'a tana lumshe ido tare da cize baki. Mik'ewa zaune tayi ta saka hannu biyu ta dafe kanta ta d'auki hijjabin ta da yake gefe ta zura ta sakko da hannun ta k'asa ta dafa tayel sannan ta sakko da k'afafun ta, k'okarin fara rarrafe take tana tana fara jan k'afar ta tsaya cak ta saki wata k'ara sabida wata irin azaba da taji tana ratsa ta babu shiri ta zauna tare da sakin wani irin kuka mai k'arfi, kukan ta ya saka Fahad bud'e fuskar sa da take lullub'e da blanket ya d'ago idon sa da suka koma jajaye ya kalli inda yake jin kukan ya ganta a zaune ta mik'e k'afa kamar wacce take nak'uda, mik'ewa zaune yayi tana kallan ko ina na d'akin kamar mai son tuna wani abu, washh ya furta yana dafe kai da hannu biyu sakamakon wani irin Sarawa da kansa yayi ya jima a haka kafin ya d'ago har lokacin yana jin sautin kukan ta hakan ya saka ya mik'e tsaye dakyar ta k'araso inda take muryar sa a dashe yace, "Ki daina kuka". Jin sautin maganar sa ya saka tayi saurin d'ago ta kalle tayi saurin kawar da kanta cikin kuka ta furta, " Ka saka kaya". Jin abinda tace ya saka ya kalli kansa a sannan ya tuna babu kaya a jikin sa, a gefen mudubin d'akin yayi gamo da jallabiya ya saka tare da k'arasowa inda take yace, "To ki daina kukan." Kallan sa tayi ganin ya saka kaya yasa tace,"Dan Allah ka had'a min ruwan wanka a toilet." Ba musu ya nufi bandakin yana tafiya yana dafe kansa sabida jirin da yake d'ibar sa yayi kamar yadda tace ya dawo, ganin ya dawo ya saka tace, "Ka taimaka min na shiga bandakin k'afa na ciwo yake." Hannun ta ya kama duka biyun ta mik'e tsaye amma tsayuwar ta gagara tayi kamar zata fad'i yayi saurin taro ta fad'o jikin sa kwanciyar da tayi a jikin sa nan taji mutun zazzab'in da yake a jikin sa har wani wuci jikin sa yake sabida zafin yayi yawa, a hankali ya taka ta d'aga k'afar da niyar takawa wani rarad'ad'i ya kawo mata ziyara ba shiri ba mayar da k'afar baya, juya kanta tayi ta kalli agogo taga 12;40 ganin lokacin yana sake kurewa ya saka ta runtse ido ta taka k'afar tana kuka sosai tana tafiya kamar yar shayi tana hutawa har suka k'arasa cikin band'akin, tama manta da wani Fahad a tsaye suna shiga ta cire hijjabin jikin ta ta shiga cikin ruwan ta kwanta duk da zafin da take ji hakan bai saka ta fito ba sabida tasan shine Maganin ta. Kwanciya tayi a ciki ta lumshe ido hawaye na sauka a idon ta tana kuma ajiyar zuciya.
Zuba mata ido kawai yayi cikin wani irin yanayi da ya tsinci kansa a ciki da bai san yarda zai kwantata shi ba kawai ji yake wani Abu na yawo a jikin sa kamar jini, yana nan tsaye yana kallan ta ta bude fanfo ta zubar da ruwan da take ciki ta kunna na sanyi dana zafin a had'e har yayi zafi yadda take so kana ta mik'a hannu ta sake kashewa ta koma ta kwanta a cikin ruwan, bacci take ji yana furzar ta ta bud'e idon dakyar ta mik'e duk a zaton ta zataji ta dawo dai-dai amma ina sai zafin yana nan sai dai ya d'an ragu ne Kawai, shower ta kunna ta tsaya a ciki ruwan yana sauka tunda kanta har yatsun k'afar ta, sai a lokacin ta d'ago kai suka had'a ido da Fahad sai ta dabarbarce ta fara k'okarin neman abinda zata suturta jikin ta amma ta makara tuni shima ya k'araso inda take ya tsaya a shower ruwan yana sauka a kansu, wata irin azababbiyar kunya ce take yawo a jikin ta ji take kamar ta nutse a band'akin amma shi ko a jikin sa ya zuba mata ido kawai, a haka suka tsarkake jikin su ta d'aura towel har lokacin bata sake bari sun had'a ido ba shima ya d'aura ta fara takawa a hankali tana k'okarin had'e k'afar ta duk sa zafin da take ji har suka k'araso wajan gadon, ta kalli gadon gashi nan kaca-kaca ya zare bedsheet din ta nad'e kawai ta tura k'asan gadon dan a yarda take ji bata tunanin zata iya komawa toitel, doguwar riga kawai ta tura shima ya zura jallabiya ta haye gadon ta kwanta tare da rufe kanta da blanket. Shima yarda tayi haka yayi ya matso jikin ta sosai ya rungume ta sosai a jikin sa sabida wani irin so da qaunar ta da suke ratsa shi ba tare da yasan hakan ba ji yake kamar in yayi nisa da ita za'a kwace masa ita. Dukkan su da zazzab'i mai zafi suka kwanta ga ciwon kai da ko wannen su yake damun sa, gab da asuba Fahad ya farka sabida ciwon sa kansa yake masa bazai barshi bacci ba mik'ewa yayi da niyar d'auko magani yasha wani jiri ya kwashe shi ya zube a k'asan d'akin. Duk da baccin ta yayi nisa amma jin kamar Abu ya fad'i ya saka ta bud'e ido ta juyo ta ganshi a zaune yayi zaman yan bori ya dafe kansa da hannu biyu, ta bud'e baki zatayi magana amma sai bakin ta ya kasa furta Kalmar FAHAD! Kamar ko yaushe bata san lokacin da tace, "Yaya Fahad meya same ka?." Da hannu ya iya nuna mata kansa ta sauke numfashi ta mik'e dakyar ta bude bedside ta d'auko sudrex sai dai babu ruwa a d'akin dole ta mik'e tsaye tana girgiza kanta ta dafe kan nata ta soma takawa a hankali a hankali ta k'arasa jikin kofa ta jingina da k'ofar ta huta sannan ta bud'e ta fito falon ta d'auko ruwan ta dawo d'akin ta zauna ta b'allo maganin ta mik'a masa ya saka a baki ta bashi ruwan yasha itama tasha ta zauna tana kallan sa. _Rayuwa kenan nidai komai nawa daban yake dana mutane na rasa mahaifiya ta na taso cikin soyayyar mahaifi na na rabu dashi na fada hannun kidnappers na kub'uta ba tare da ko sisi yayi ciwon kai ba na zo gidan nan na had'u da Fahad baya Sanin da nayi masa amma shi bai gane ni ba, ana aure cikin nishadi da walwala da farin ciki ana gayyatar mutane amma ni nawa akasin hakan ne, na tashi daga matar sa na dawo mai kula dashi, ango shine yake neman amaryar sa amma ni nice na nemi miji na nice na taimaka masa akan komai, miji shine yake kula da matar sa a daren farkon su na aure shine yake bata kulawa ya fad'a mata kalamai masu dadi amma ni kuma nice nake kula dashi, ya Allah ka sa wannan shine karshen wahala ta a rayuwa ta gabadaya Allah ka sa in ya dawo dai-dai komai yazo min da sauqi._ ajiyar zuciya tayi ta kalle shi a lokacin bacci ya fara d'aukar sa tace,"Ka dawo nan ka kwanta." Baiyi musu ba bai yi kuma magana ba ya mik'e ya dawo ya kwanta itama ta kwanta a lokacin aka fara kiran assalatu. Basu koma baccin ba sukayi sallah sannan suka kwanta.*Monday 10:00am*
"Yanzu Musleeha zaki tafi ki barni ko?" Mummy take fad'a tana kallan Musleeha da take goye da yar k'aramar jakar ta baya tana wasa da alawar hannun ta, "Nikam Mummy yau ina Haleema?" Khadeeja ta tambaya tana kallan Mummy. "Ita nake ta tunani Nima tun d'azu yau shiru bata fito ba har yanzu anya lafiya kuwa? Nasan Haleema bata da nauyi." "An kira wayar ta kuma?". "Tun dazu nake kiran number da kika bani amma ba'a d'auka, kije ki dubo ta Allah ya sa dai lafiya." Batayi magana ba Khadeeja ta fita Musleeha ma tabi bayan ta. Knocking Aunty Khadeeja take amma shiru ba'a bud'e ba sai ta murd'a handle din akayi sa'a a dub'e yake ta shiga cikin falon, yana nan fess dashi sai dai pillows din kujeru da suke a k'asa hakan ne ya tabbatar wa da Aunty Khadeeja Haleema bata jin dadi. Cikin bacci Haleema taji ana knocking din k'ofa ta mik'e zaune a hankali ta dafe kai ta zuro k'afafun ta k'asa ta saka hijjabi ta tako a hankali ta fito daga d'akin. Ciwon kan da yake damun ta yasa ta zura k'afar ta ba dai-dai ba sai kuwa ta gurd'e tayi kamar zata fad'i, da hanzari Khadeeja ta k'araso wajan ta ta rik'e ta tana fadin,"Subahanallahi Haleema baki da lafiya haka?." K'okarin k'ak'alo murmushi take tace, "Ina kwana?". " Meya same ki kinji zafin jikin ki zuwa? Kalli idon ki yadda kika rame bara na kira Abbah ya duba ki" ta fad'a tana k'okarin danna waya. Hannun ta ta d'ora akan wayar tace,"A'a Aunty basai kin kira shi ba zazzab'i ne kuma nasha magani zai sauka" ta fad'a muryar ta a sanyaye. "Wanne irin kin sha magani kuma? Ji maganar ki ma ta canja tsabar ciwo, Musleeeha jeki kice Mummy tazo". " Zo Musleeha, Aunty naji sauqi fa dan Allah kar ki Sanar da Mummy " Haleema ta fad'a tana dafe kai sabida jirin da ya soma d'aukar ta, a wajan ta zame ta zauna Khadeeja ma ta zauna tace,"Babu yarda za'ayi kice kar a sanar dasu alhalin baki da lafiya do......" Maganar ta makale ganin Fahad ya fito yana yatsine fuska, bai kula da Khadeeja ba hankalin sa na kan Haleema yace,"Shine kika gudo kika barni" yayi maganar kamar mai shirin yin kuka. K'are masa kallo Khadeeja take shima ya rame sai dai fuskar sa ta sake yin haske sosai tace, "Fahad". Inda aka kira shi ya kalla ganin Khadeeja ya saka yace," Yauwa gwara da kika zo ma bata iya tafiya tun jiya da daddare" ya fad'a yana nuna mata Haleema da hannu cikin tausayawa. Kallan Haleema tayi tace, "Ciwon k'afa kuma? Fad'uwa kika yi?". " A'a ba fad'uwa tayi ba jiya da daddare ne bayan an...." Saurin tarar numfashin sa Haleema tayi tace,"Jiya da daddare ne na bige da kujera shiyasa." "Kaii! Mummy tace fa karya babu kyau ba fad'uwa tayi ba kawai jiya ne...." "Aunty fad'uwa nayi kuma yanzu ma k'afar tayi sauqi." Cikin tuhuma Khadeeja tace,"yace kuma ba fad'uwa kikayi ba ki fad'a min gaskiya mana Haleema." Shiru tayi ta Kalli Fahad da ya zuba musu ido ta Kalli Musleeha tace, "Fahad kai da Musleeha ku jira ni a nan ina zuwa" ta fad'a tana k'okarin mik'ar da Haleema itama tana mik'ewa, dakyar ta tashi tsaye suka shiga d'aki tafiyar tace ta tona mata asiri Khadeeja ta kalle ta cikin tausayawa ganin tana hawaye tace,"Kada kiyi kuka Haleema na fahimci komai yanzu" ta sauke numfashi ta cigaba da fadin, "dolen dole nasan ki sha wahala daman nasan zaki ga kamar bakiyi sa'a ba a rayuwar ki amma kiyi hakuri aure duk sunan sa kuma ki saka a ranki bautar sa kike kuma daman ita bauta tana da wahala sai an jure za'a samu nasara, yanzu ki tashi muje ki gasa jikin ki." Kanta a sunkuye ta goge hawayen fuskar ta tace, "nayi". " A'a ki sake yanzu na tabbata zaki ji dadi sosai tashi muje" ba musu suka shiga ta had'a mata ta fito ta barta, bata wani jimawa tayi sosai ba ta fito kuma taji dadi sosai ba kamar d'azu ba, tas ta Tarar da d'akin Khadeeja ta gyara shi ta shinfid'a sabon bedsheet da tayi karo dashi a cikin wardrop, a bakin gadon ta zauna tana addu'ar Allah ya sa bata ga wanda ta b'oye a kasan gado ba, dan lek'awa tayi ta ga yana nan tayi ajiyar zuciya Khadeeja ta debo mata kaya ta bawa waje ta shirya tsaff kafin ta dawo d'akin. Agogon d'akin ta kalla kafin ta kalli Haleema tace,"Jirgin mu ya kusa tashi Na kusa missing flight amma zamuyi waya kinji kada kiji tsoro. " "to amma dan Allah kada ki Sanar da Mummy." "Kar ki damu babu wanda zaiji maganar sai munyi waya" tana gama fad'ar hakan ta fice a falo ta rik'e hannun Musleeha suka fice bayan tacewa Fahad ya koma ciki.
Koda Khadeeja ta koma bata fad'awa Mummy komai ba fada mata kawai tayi bata jin dadi a aika musu da breakfast ta fito ta Shiga mota sai airport._Dan Allah ayi hakuri dani lamarin ayyuka ne suka yi min yawa shiyasa ba'a ganin update da wuri wannan ma ko editing ban samu nayi ba, ina godiya da tarin addu'o'in ku gare ni fan's na WhatsApp dana Wattapad ina godiya sosai._💝
Comments and share.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
❤ZUCIYA CE❤
Fantastik"Abba gaskiya kana nuna banbanci tsakani na da Haleema kamar ba kai ka yafe ni ba." Kallan ta yayi cike da takaici yace,"Banbancin ki da Haleema kenan Hafsat baki da labadi ko kadan." ***** "Wayyo wai me nayiwa Haleema ne? Ta raba ni da Abba na yanz...