Page 17&18

32 3 0
                                    

❤️ *ZUCIYA CE*❤️

*Nana Halima😎*

*17&18*

"Oga ta suma fa." Tsaki wanda aka kira da Ogan yayi tare da tab'e baki yace,"Tama farfado dan uwar ta, ku d'auke min wannan gawar ku turawa iyayen ta" yana gama fad'ar hakan kawai ya Mike mutum biyu suka dauki gawar sauran suka bi bayan sa.

*********

Gidan Abba ya koma shiru babu walwala a cikin sa kowa ka gani haka yake sukuku kamar Mara lafiya Hafsat kuwa har wata rama tayi sabida kewar y'ar uwar ta, kamar kullum Abba yana zaune ya kafawa hoton Haleema ido  yayi shiru ya rass tunanin ma me zaiyi, har Mama ta zauna a kusa dashi bai Dani ba sai da tayi gyaran murya sannan ya d'ago kai ya kalle ta bai ce komai ba ya mayar da kai kasa tare da fad'in,"ance anyi kidnapping din ta meyasa har yau an kasa yo waya a fad'i kudin fansar da ake nema? Hadiza bana iya bacci kullum cikin tunani nake da naga sabuwar number har sauri nake na dauka sabida ina tunanin ko sune amma sai naji akasin haka, Allah ka kare min Haleema ta da abinda yake cikin ta." Ajiyar zuciya Mama tayi tace,"Muna addu'a insha Allah za'a samu labarin ta, amma ina so na tambaye ka wani Abu." "Ina jinki." "Lokacin da abin nan ya faru naji kana cewa ka ga Haleema kwance a kirjin wani shine ban fahimta ba yaushe kaga hakan? A ina kuma?." Ba tare da yace kala ba ya dauki wayar sa ya shiga cikin gallery ya mikawa Mama wayar, amsa tayi tare da kallan wayar da ya bata, wata irin guguwar tashin hankali ce da faduwar gaba ce ta ziyarci Mama ganin Haleema a kwance a jikin wani kato daga ita sai pant ko brezia babu ya zagoya da hannun sa ya rike kugun ta hannun sa daya na saman kirjin ta  Suna dariya, hannun ta har rawa yake ta tura wayar gaba sai ga wani ya bayyana wannan kuma a cikin bathtub ne da ita da wani mutumin kuma ba wancan ba suna kwance cikin kumfa babu komai a jikin su, bata san lokacin da ta saki wayar ba bakin ta na rawa zuciyar ta kamar zata fito waje sabida bala'in bugu. "Kinga dalilin da ya saka na dauki mataki akan Mama na ta bani mamaki sosai ban dauka haka halayyar ta take ba wnnan shine ya fusata ni har nayi mata baki ba tare sa na sani ba." Mama da hawaye ya wanke mata ka bakin ta na rawa tace,"a ina ka samu wad'an nan hotunan?." "Tura min su akayi na rasa wacce number ce har yanzu in na kira a kashe har yanzu kafin ki shigo ma na kira amma shiru."
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, shine kadai abinda Mama take iya furtawa jikin ta har rawa yake sabida firigici da tashin hankali,  ganin yadda ta rude ya saka yace,"kije ki huta naji kamar ma kinyi baki" daga haka kawai ya Mike ya fad'a bedroom. Duk yadda Mama taso ta saita nutsuwar ta kasawa tayi kana kallan ta kaga a firgice take hakan yasa ta dauki waya ta kira Hafsat tana dauka tace,"Hafsat ki cewa bakuwar ina sama bazan sakko yanzu ba" bata jira abinda zatace ba kawai ta datse wayar ta mayar da kanta a jikin kujera ta jingina tana sauke numfashi.
Hafsat da take kwance a d'aki ta fito falo ganin Aunty Salamatu ce ya saka tayi dan murmushi ta karaso wajan ta zauna tace,"Ina wuni." "Lafiya lau Hafsat ina Maman naku?." "Tana sama tana bacci." "Daman ba wajan ta nazo ba wajan ki nazo." Hafsat ta gyara zama tace,"to Aunty." Aunty Salamatu ta matso kusa da Hafsat sosai tace, "To ya kika ga aikin? Ina fatan yayi yadda kike so?." "Aiki kuma wanne aiki kenan?." "Aikin mu na korar y'ar uwar ki daga gida mana yanzu baga shi ke kad'ai kike walwalar ki a gidan ku ba kina kuma tare sa saurayin ki babu abinda yake shiga tsakanin ku." Bakin ta har rawa yake wajan furta, "Kenan kece kika..." Tarar numfashin ta tayi tace, "aikin da kika ce kina so shi akayi aka kori y'ar uwar ki daga gidan nan." A zabure Hafsat ta mike tsaye ta zaro ido waje cike da firgici tace,"wai kina nufin da saka hannun ki a barin Haleema gida? Kenan b cikin gaskiya gare ta ba hadawa kika yi?." "Keee daina d'aga murya kar wani yaji ki, aikin mu dai ba aiki na ba kuma wanne irin ciki kike magana a akai?." "Cikin da akace Haleema tana dashi nake nufi."  Cike da mamaki ta kalli Hafsat tace,"ciki kuma? A'a ban san labarin ciki ba gaskiya wannan sai dai in da gaske cikin gare ta nidai nasan kin saka an miki aikin da Abban ku zai tsane ta."
"Kenan da gasken tana da cikin? Meyasa zaki min haka Aunty meyasa zaki so ki raba Haleema da Abba?." "Ke malama kefa kika same ni kika ce kina so dan na taimaka miki sai ya zama abin magana kuma, kinga ki rike sirrin ki in ba haka ba kece a ruwa dan ni daga yau babu lallai ki sake gani na kinga tafiya ta" tana gama fadar hakan ta nufi hanyar fita daga falon tare da ficewar ta. A wajan Hafsat ta zube tana kuka babu abinda take hangowa sai lokacin da Abba ya furtawa Haleema Allah ya isa runtse ido tayi, "yanzu da saka hannu na a Barin Haleema gida? Na shiga uku ni Hafsat meyasa na aikata hakan? Haleema fa" kamar an tsungule ta ta Mike da sauri ta fad'a daki.

*********

Iskar dake kad'awa ce ta Farkar da Haleema da take sume, a firgice ta mike zaune tana kallan Inda akayi harbin jikin ta na rawa babu abinda take gani sai matar a idon ta, curewa tayi waje daya hakoran ta har garuwa suke da na juna  tsbaar tsoron da take ciki. Sai da ta kwashe mintina sama da ashirin a haka kafin sanyin wajan ya fara ratsa ta sabida gabatowar sallar magariba gashi bata jin motsin kowa a wajan sai na tsuntsaye  ta waiga amma bata ga kowa ba alamun masu tsaron nata ma basa nan, nan take zuciyar ta bata karfin guiwar guduwa daga wajan ta mike a hankali duk da juwar da take ji hakan bai hana ta kokarin tsayawa tsaye cak ba, a hankali ta fito daga cikin rumfar buhun da take kwance tana kalle-kalle can gefe ta hango d'aya daga cikin su ya juya baya yana fitsari a hankali take baya tana kallan sa har ta wuce runfar buhun bata juya masa bayab ba har lokacin shi kuma bai juyo ba bai kuma mike daga tsugunon da yake ba, juyawa tayi taga hanya ce mik'akkiya gashi duhun magariba ya fara ga sanyi a hankali take bin hanyar gudun kada tayi gudu ya jiyo ta, sai da ta d'anyi nisa dashi kafin ta falla a guje bata kallan hanyar da take bi ma kawai gudu take, tayi nisa sosai da gudu amma bata hango ko alamun titi sai daji kan da take ketawa tana bi,k'ara ta saki hade sa hawaye ta sunkuya tana hakki sabida k'ayar da ta taka ta huda mata kafa jini na zuba, amma dake ceton rai yafi fitar ran wahala haka ta take kafar ta cigaba da gudu. Tana gab da isa titi karfin ta ya kare k'afar ta ta rike ta gaza gudun ta zauna a wajan tana hakki, wani irin jiri ne yake d'aukar ta sai juya kai kawai take idon ta a lumshe hannun ta na dafe da zuciyar ta bata sake sanin Inda kanta yake ba.
"Likita me yake damun ta?." Sai da yayi y'an rubuce-rubuce sannan yace,"ta samu rauni a k'afar ta bayan wannan kuma tana da heart attack ciwon kuma ya tashi a wannan lokacin, kuma ta kwana biyu bata ci abinci ba haka malara tayi mata mugun kamu amma insha Allah zamu yi kokarin ganin komai ya tafi dai-dai." Ajiyar zuciya ya sauke ba tare da yace komai ba yaja gefe ya tsaya. "A'a wa nake gani kamar Yusuf?" D'ago ido yayi ganin wacce take magana ya saka yayi murmushi yace,"Nice Aunty ina wuni?." "Lafiya lau, waye bashi da lafiya?." "Wallahi Aunty wata yarinya ce na gamu da ita bata san Inda kanta yake ba abin tausayi wallahi." Zaro ido tayi tace,"Yusuf kasan wacece? Kasan duniya fa ta lalace yanzu." "Allah yaga zuciya ta ai Aunty ni da niyar taimako na taimake ta." "To Allah ya bata lafiya, nima wata kawata nazo na duba muje na duba ta." "No sun ce kar a shiga yanzu."
"Okay na dawo wani lokacin, yayan ka kuwa yana neman ka tun jiya kazo ka same shi" Sai da ya sosa kai sannan yace, "To Aunty Khadeeja zan zo a gaida Musleeha." Bata ce komai ba tayi murmushi kawai ta bar wajan. Ajiyar zuciya ya sake yi ya kalle dakin da Haleema take kwance cike da tausayin ta ya d'auke kai ya zauna yana duba agogo gashi dare yanayi har takwas ta kusa.   Koda Khadeeja ta koma gida a can ta Tarar da Fahad yana zaune suna hira da Abban su Musleeha da mamaki take kallan sa tace, "Autan Mummy sukar yaushe kuma?." "Saukar d'azu" ya bata amsa yana kallan ta ransa a had'e, "too qalau kake wani b'ata min raii?."  "Ai wallahi an bata min rai uba ne fa ni a wajan Musleeha amma ace wai anyi kidnapping din ta har na tsahon kwana biyu amma ace ba'a Sanar dani ba ko a waya ai wannan ba abinda za'a boye min bane ba." Sai da ta zauna sannan tace,"kayi hakuri wallahi lokacin hankalin kowa baya tare dashi shiyasa, kuma tsoro na kada a sanar dakai kace baza'a kai kudin fansa ba sai da police kuma sunce in aka hada da police sai sun kashe ta." "To naji Allah ya kiyaye gaba, amma tana ta bani labarin wata a can Inda aka sace ta din." "Eh daman jira nake ka dawo muyi maganar ni a gani na cikin kidnappers din ne sai nake ganin kamar kama su bazai wahala ba." "Anya kuwa sai dai cikin wanda aka sace bana tunanin cikin kidnappers wani zai kula da Musleeeha gaskiya." Abban Musleeha dake zaune sai yanzu ya saka baki a hirar su yace,"Shine abinda nake fad'a mata nima sai dai cikin wanda aka sace amma ba wanda suka sace ba."
Girgiza kai tayi kawai tace,"to ko wacece ma Allah ya saka mata da alkhairi, kaga yanzu kuwa naga Yusuf a asibitin da naje ya kai wata patient da ya taimaka mata yace zai zo ma." "Yusuf sarkin taimako to sai yazo."

A 6angaren Yusuf kuwa nurses ya biya kudi su biyu suka zauna da Haleema shi kuma ya koma gida dan dare yayi lokacin.


Ayi min hakuri pls🤒🤒🤒

Comments and Share.

❤ZUCIYA CE❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora