Page 43&44

42 5 1
                                    

*❤️ ZUCIYA CE*❤️

*Neat Lady*

*43&44*

         A razane ya kalli mahaifiyar tasa bakin sa na karkarwa yace,"Mummy akan wannan karuwar kika mare ni?". Sauke masa wani Sabon marin tayi tana wuci ta nuna shi da yatsa tace,"Ko yanzu ka sake kiran ta da karuwa sai nayi maka abinda yafi wannan shashasha mara hankali da tunani, a ina kasan ta harda kake jifan ta da irin wannan kalamai masa dad'i?." Hannun sa dafe da kuncin sa ya d'ago idanun sa da suka koma ja bakin sa har rawa yake sabida b'acin rai ya kalli Abbah ya kalli Yaya ya mayar da kallan sa ga Mummy yace,"ba jifan ta nake dasu ba Mummy gaskiyar asalin gaskiyar ta nake fad'a, amma tunda baki yarda ba zan kawo miki evidence da zai saka ki gasgata magana ta." Banzan kallo ta jefe shi dashi ta nuna masa k'ofar fita tace,"B'ace min da gani." Mamaki k'arara ya bayyana a fuskar sa yau shine Mummy take cewa ya fita saboda wata y'ar iska karuwa, "Mummy ni?" Ya fad'a yana nuna Kansa da yatsa. "Fahad kaje tunda tace ka fita" Abbah ya fad'a yana nuna masa hanya shima, a fusace ya juya ya fita kamar zai tashi sama. Haleema da take wajan a tsaye kamar gunki ko motsin kirki batayi sai hawaye dake ambaliya daga idon ta, rik'o hannun ta Mummy tayi ta zaunar da ita a kan kujera ta kalli Abbah tace,"Bani ruwa a fridge". Karasawa wajan fridge din yayi ya d'auko ya mik'o mata, b'alle murfin robar tayi ta mik'awa Haleema kamar jira take ta karb'a ta kafa kai sai da tasha rabin robar sannan ta sauke sai a lokacin ta samu damar fashewa da kuka mai sauti.
Zama Mummy tayi kusa da ita tana shafa bayan ta a hankali alamun rarrashi, cikin sanyin jiki Abbah da Yaya suka nufi hanyar fita maganar Mummy ta dakatar dasu da fadin,"idan kun tashi daga aiki kuzo". Da to suka amsa suka fita. Sai da Haleema tayi kuka mai isar ta ta koma sauke numfashi Mummy tana zaune kusa da ita tana rike da hannun ta tana kallan ta cikin tausayawa, rasa Kalmar da zata fad'a mata ta bata hak'uri tayi sabida tasan Fahad ta gama lalata komai bata San me zata furta ba, "ina mai bai dawo tunanin sa" Mummy ta furta a fili ba tare da ta sani ba hakan ya fargar da Haleema abinda yake faruwa tayi saurin d'ago kai tana girgiza shi tace,"kamar yadda ya fad'a Mummy ni karuwa ce a idon sa sun kasa fahimtar ba laifi na bane ni ba fasik'a bace ban tab'a zina ba wallahi ban tab'a ba" kuka ne yaci karfin ta ta kasa k'arasawa, Mummy ta jawo ta jikin ta tana buga bayan ta tana fad'in, "ki bar fad'ar wannan maganar Haleema kiyi hakuri ki daina kuka ni na yarda dake". Kuka take sosai Mummy na rarrashin ta tana jin tausayin ta na sake ratsa ta zuciyar ta cike da haushin Fahad tunda yake da ita wannan ne karo na farko da ya tab'a bata mata rai kamar haka.  Kafin wani lokaci zazzabi mai zafi ya rufe Haleema magani Mummy ta bata tasha bacci ya d'auke ta. Fahad kuwa yana fita part din sa ya koma ya zauna akan kujera babu abinda yake masa yawo a kai sai kalaman Mummy, dukan hannun kujerar yayi ya mik'e yace," bazai yuwa ba wallahi bazan zauna da Haleema matsayin mata ba ko babu halayyar ta bazan iya auren ta ba Sam bata cikin type d'ina, ya zama dole na nemo mafita." Zaro ido waje yayi a lokacin da idon sa ya dauka akan hoton Hafsat yace,"Hafsat! Haleema k'anwar tace dole na San abinyi bazan tab'a bari Hafsat ta kubuce min ba."
A fusace ya fad'a daki ya fara bincika kayan sa yana yi yana Jan tsaki har ya gano abinda yake nema ya fito a fussace ya nufi parking space din gidan, Bello driver ya ya karasa inda yake bai mai magana ba yace,"Bani key din motar Mummy". Ba musu ya bashi ya k'arasa wajan motar ya Shiga ya ja ta a guje ya fice daga gidan, bai wuce ko ina ba sai MTN office bai jima sosai ba aka yi masa swapping din sim card din sa ya fito ya sake Shiga mota ya nufi kasuwa, tafiya yake kallan gari yana girgaza kai tabbas ya amince yayi watanni cikin ciwo ganin yarda garin ya canja masa, koda ya karasa kasuwar shagon waya ya Shiga ya siyi waya ya dawo Mota, jona wayar chaji yayi ya kunna motar ya tafi. Maimakon ya wuce gida sai ya karkata motar zuwa wani wajan daban, a bakin kofar wani gida mai kyau kana ganin sa kaga sabon gini yayi parking ya fito ya Shiga gidan, a harabar gidan ya zauna akan kujera ya kunna wayar tare da d'ora sim card din hannun sa, sai kuwa sakkonni suka dinga shigowa bai damu ya bud'e ba kati ya Siya ta bank ya siyi data ya Dora email din sa akan wayar take komai ya dawo kan wayar kamar tasa ta da, tun daga kan photos, contacts, videos etc, hannun sa na rawa yayi Darling din numbers masoyiyar sa sai dai har ya gama ringing ta katse ba'a dauka ba. Numfashi ya sauke kamar mai jin tsoro ya Shiga photos yana runtse ido ya bud'e photon Haleema da take kwance a jikin wani jikin ta babu komai, switch din wayar yayi ya runtse ido yana sauke numfashin b'acin rai, "Wai wannan za'a kalla a kira ta da matata, impossible saina rabu da ita bazai yu ba." Mikewa yayi ya fito ya kulle gidan ya fad'a mota ya nufi gida.

❤ZUCIYA CE❤Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang