Page 39&40

42 5 2
                                    

❤️ *ZUCIYA CE*❤️

*Neat Lady*

*39&40*

Kallan Up and down Haleema tayiwa Fahad tayi saurin kawar da kai tana rufe idon ta Sam bata so ta tuno abinda ya shiga tsakanin su a jiyan ko wacce macen kirki tana alfahari da daren farkon ta amma ita ta rasa meyasa bata alfahari dashi kodan nata dana sauran mata ba iri d'aya bane oho.  "Sannu" ya furta can k'asan mak'oshi, juyo da kanta tayi ta kalla shi yana tsaye a jikin bango ya rungume hannun sa a kirji yana kallan ta yana lumshe ido, "Yauwa" ta fad'a tana kawar da kai. Zai sake magana yaji ana Sallama a falo hakan ya sa ya fasa ya fita jim kad'an ya dawo ya kalle ta yace,"Kizo ki bani abinci gashi Mummy ta kawo" yayi maganar a shagwab'e kamar karamin yaro, "kaje kaci kwanciya zanyi" ta fad'a tana niyar kwanciya a akan gadon, "A'a nidai ki tashi ki bani yunwa nake ji". Zuba masa ido tayi cike da takaici ji take kamar ta tashi ta makure masa wuya amma sai ta danne zuciyar ta ta mik'e ta fito falon ta zuba masa ta koma gefe tare da d'auke kai daga kallan sa. Zuba mata ido tayi kafin yace," Kizo kici". "Bana ci" ta bashi amsa a takaice. "Nima bana ci." Karamin tsaki taja a hankali ta furta, "Cikin ka". Gefe ya koma ya zuba mata ido kawai yana kallan ta ita kadai ce take masa yawo a cikin kwakwalwar sa ji yake kamar ya Santa a wani waje daban amma ya kasa tunawa ji yake kamar ya tab'a rayuwa da ita amma ya kasa tuna komai game da hakan, ajiyar zuciyar da ya sauke ya saka ta juya ta kalle shi ya sunkuyar, tausayin sa ta ji yana ratsa ta tace," Muje kayi wanka sai muci abincin ko?". Kamar jiran maganar ta yake ya d'aga kai kamar k'aramin yaro yana dariya ya mike suka shiga bedroom ya shiga wanka ita kuma ya d'auko masa kaya.
Haka rayuwa ta fara tafiya sakunkuna suna komawa mintina, mintina suna komawa awanni, awanni na komawa kwana, shak'uwa da soyayya mai zafi ta sake shiga tsakanin Fahad da Haleema koda yaushe suna tare ko wanne su baya qaunar yaga wani baya tare dashi hatta mutanen gidan sun fahimci irin qaunar da take tsakanin su, cikin yan watan ni kad'an Haleema ta sake sosai da mijin ta ta dage tana bashi kulawar da ko wanne magidanci yake fatan samu hakan ya k'ara ninka shak'uwar su fiye da ta da.  Rayuwar su abin sha'awa in ka gansu baza ka d'auka Fahad yana tare da wata matsala ba sabida yarda yake samun kulawa ta musamman, bangaren addinin Fahad yasan abubuwa da dama a yanzu Haleema tayi k'okari wajan koyar dashi musamman b'angaren tsarki, alwala, da kuma sallah, kamar yadda mummy ta umarce su akan yau su shirya a zaga dasu gari hakan ce ta kasance Fahad ya shirya cikin yadi kofi mai kyau ya dora hula kofi abin ka da farar fata sai ya fito tas kamar ka sace shi ka gudu, jar abaya Haleema ta saka tayi rolling kanta da mayafin abayar ta fashe jikin ta da turaruka masu sanyin kamshi ta kalli kanta a mudubi bata san lokacin da ta saki murmushi ba tana kallan ta, ta baya Fahad ya rugumo ta ya zagayo da hannun sa ya rike cikin ta tare da kwantar da kansa a kafad'ar ta yana shak'ar kamshin jikin ta yana lumshe ido, hannun ta ta d'ora akan nasa tana murmushin farin ciki qaunar Fahad na sake zagaya ko ina na jikin ta, wayar ta ta d'auka ta shiga d'aukar su mirror shoot, sosai sukayi kyau a wayar kamar ka Ciro su kana ganin su kaga sun dace da juna babu wanda zai kalli Fahad yace yana tare da wata matsalar tunani haka itama Haleeman kamar bata tare da ko wacce damuwa sabida yadda ta canja lokaci d'aya. Sai da ta gaji da kanta kafin tace, "Ya kamata muje driver yana jiran mu." Bai sake ta ba haka kuma bai d'aga kansa daga jikin ta ba wani irin nishad'i ne yake ratsa shi duk da yana jin fad'uwar gaba amma hakan bai saka ya danne nishad'in da yake ciki ba,  "Yaya Fahad! Kana ji ina magana fa" ta fad'a a shagwab'e tana turo baki gaba. Kamar bada shi tayi magana ba sai ma sake rike ta da yayi, "Yaya Fahadddd!" Kamar wanda aka tsikara yayi saurin ja baya kana kallan ta yace,"sake fad'a naji". Haleema da ta d'an rikice tace,"Yaya Fahad nace, lafiya dai ko". "Ashhhh" ya fad'a yana dafe kan sa da hannu biyu tangad'i kamar zai fad'i, saurin riko shi tayi ta zaunar dashi akan gado tace,"Yaya Fahad lafiya?". Bai magana ba sai sake dafe kansa da yayi yana jin yadda sunan yake shiga cikin kwakwalwar sa da sauri,  bata motsa ba dan ta fahimci yana k'okarin tuna baya ne sai tayi shiru tsoro da fargaba suka cika mata zuciya nan take farin cikin da take tare dashi ya kushe ya koma zallar tashin hankali, sai da ya kwashe mintina shida a haka kafin ya sassauta rik'on da yayiwa kan ya kalle ta yace, "wani lokacin sai naji kamar akwai wata wacce na sani tana kira na da wannan sunan kuma har maganar ku tana min kama da ta waccan duk lokacin da nayi k'okarin tunawa sai na kasa ina jin a mafarki na santa" ya fad'a yana cize bakin sa.
Dammm kirjin Haleema ya buga jikin ta yayi sanyi dan tana da tabbacin itace wacce yake magana akai dan ko a baya ita kadai take kiran sa da Yaya tabbas ita yake k'okarin tunawa, baya tayi ta zauna a akan tayals din tace, "Sannu" tare da sunkuyar da kanta. Mik'ewa yayi yace,"Tashi muje." "A'a mu hak'ura kaga baka da lafiya." "Naji sauqi muje" ya fad'a yana fitowa falo. D'aga kan da zaiyi idon sa ya fad'a kan hoton Hafsat da yake bangon d'akin a hankali ya taka ya karasa wajan ya tsaya yana karewa hoton kallo, "a ina na Santa? Meyasa nake jin fad'uwar gaba in na kalli hoton ta? Me tsakani na da ita?" Tambayar kansa yake a bayyane amma babu mai bashi wannan amsar, Haleema ganin sa yana kallan hoton Hafsat jikin ta ya sake yin sanyi tabbas tunanin sa yana gab da dawowa ya zama dole ta fara shirin Barin garin da mutukar Fahad ya dawo hankalin sa baza su sake ganin ta ba zatayi nisa dasu na har abada, hawaye suka sakko mata tayi saurin gogewa tana tunanin yarda rayuwar ta zata kasance. "Me ya saka ki kuka? Dan na kalli wannan?" Ya fad'a yana nuna hoton Hafsat da yatsa, "ki bar kuka bazan sake kallan hoton ba bana so kina kuka ki daina" ya fad'a yana rike kafad'ar ta, maimakon tayi shiru sai kukan ta ya k'aru jin abinda yake cewa ba k'aramin Tayar mata da hankali yayi ba, "Dan Allah ki bar kuka kinji" ya fad'a shima muryar sa tana rawa alamun shima kukan zaiyi. "A'a Autah lafiya?" Mummy da take k'arasowa ta fad'a hankali a tashe, "Yauwa Mummy kice ta daina kuka na daina kallan hoton wannan din tunda bata so." "Haleema me ya faru?". "babu komai Mummy" ta bata amsa muryar ta na rawa, "Babu komai kike kuka? Fad'a min gaskiya." "Kaina ne yake min ciwo shiyasa". " banda abinki da kanki na ciwo sai kiyi kuka kuma? Kin sha magani?". Daga kai tayi alamun eh, "shikenan ku hakura da fitar ayi gobe in Allah ya kaimu, abokan Fahad ne na Kano suka dawo zasu duba shi nazo na duba daman naga kun fita, ki shiga ki huta ke tunda bakya jin dadi kai kuma ka jira yanzu zasu shigo." Bata jira mai zaice ba ta fita ta sanar da bakin suje can yana nan, da sallama suka turo k'ofar falon suka shigo Fahad ya amsa yana binsu su da kallo har suka zauna, hannu d'aya daga cikin su ya mik'a masa yace, "Suna na Yazeed" shima hannu ya bashi suka gaisa ya kasa d'auke ido daga kansa. Wani ya sake miko masa hannu yace,"Ni kuma Ahmad" shima suka gaisa yana dai binsu da kallo, na karshen ya mik'a masa hannu yace,"Ni kuma Kamal." Gaisawa sukayi yana maimaita sunan Yazeed, Ahmad, Kamal a ransa, shiru babu wanda ya sake magana a cikin su Yazeed da idon sa ya ciko da kwallah sabida tausayin aminin nasa yace,"Hafsat tana gaishe ka". "Hafsat!" Ya fad'a a firgice sai kuma ya zaro ido waje yace,"wace ita?". Waya Yazeed ya d'auko ya nuna masa hoton ta yace, "wannan ce take gaishe ka." "Wannan! Shiiiii daina fad'a bata so ina ganin hoton ta" ya fad'a yana d'ora yatsan sa daya a bakin sa alamun yayi shiru. Kallan junan su sukayi kafin Yazeed ya mayar da wayar aljihu Dan shi yayi hakan ne ko Allah zai saka abokin nasa ya dawo dai-dai. Shiru ne ya sake biyo baya babu wanda ya sake magana a cikin su sai daga baya suka mik'e suka yi masa sallama suka fita.

Mik'ewa Fahad yayi ya shiga d'akin ya Tarar da ita a zaune tayi tagumi ya kalle ta kana yace,"zo muje wajan Mummy." Ba musu ta mik'e ya rike hannun ta suka fito zuwan wajan Mummy, a falo suka Tarar da Mummy da Abbah da kuma Yaya daman Daddy yayi tafiya, "Mummy Wacece Hafsat? Waye Ahmad? Waye Yazeed? Waye Kamal? Meyasa nake jin kamar na tab'a  ganin su? Ina so na tuna amma sai kaina ya fara ciwo" Fahad ya fad'a murya a sanyaye, kallan Abbah Mummy tayi kafin ta dawo da kallan ta ga Fahad zatayi Magana Abbah ya riga ta yace,"A mafarki ka sansu Fahad." "Mafarki? To meyasa nake jin kamar na San mai irin muryar Leema?". Murmushi Mummy tayi jin sabon sunan da ya rad'awa Haleema tace," Duka cikin mafarki ka sansu Fahad ka kwantar da hankalin ka ka daina cewa zakayi tunani." Shiru yayi badan ya yarda ba sai Kawai ya juya ya fita daga falon, "Alhamdulillah Mummy wannan alama ce da take nuna yana gab da dawowa tunanin sa" Abbah ya fad'a yana fad'ada'a murmushi, sosai Mummy ta nuna jin dadin ta Haleema kam kawai yak'e take wanda ake kira da yafi kuka ciwo.

*Kano.*

"Aunty nayi yarda kika ce wallahi na zuba a abincin Abba kuma ina da tabbacin yaci amma har yanzu basu daina maganar Haleema ba ni na rasa me zanyi ma wallahi" Hafsat take fad'a cikin k'unar rai da waya a kunnen ta. Daga can 6angaren Aunty tace, "Kada ki samu damuwa zai fara aiki sai a hankali amma ki tabbatar dai sunci abincin nan in basu ci ba to ki sake zubawa gudun kar a samu matsala." "Shikenan kawai zan sake zubawar mu gani". " yauwa to yayi, yanzu nayi bak'uwa zan kira ki" bata jira mai zatace ba ta katse wayar tare da binta da kallo ta saki wani shu'umin murmushi tace, "shashashar yarinya duk ta d'auka taimakon ta nake bata san tsuntsu biyu nake jifa da dutse d'aya ba, hmmmm har yanzu basu san true colour na Salamatu ba" ta k'are maganar da y'ar k'aramar shewa.


Comments and share.

❤ZUCIYA CE❤Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora