last page

67 4 2
                                    

❤️ *ZUCIYA CE*❤️

*Neat Lady*

*50*

Mayar da kallan ta tayi ga Haleema tace, "Zaki bini Borno mu tafi?" Ta tambaya da sigar zolaya, murmushi Haleema tayi ba tare da tace komai ba tana sunkuyar da kai qasa, itama murmushin tayi tace, "ya kamata ki koma kije ki huta zamu zo yiwa Abban ki sallama sai mu sake yin sallama dake." D'aga kai kawai tayi tare da mik'ewa tsaye, tare suka fito da Mummy Fahad yana zaune a cikin mota ya kifa Kansa a kan sitiyarin motar, gaban motar Mummy ta bud'e mata ta shiga sai a lokacin ya d'ago kai idon sa yayi ja kamar Wanda yayi kuka ya kalli Mummy baice komai ba ya rife kofar side din sa itama shi take kalla Mummy tausayin sa yana k'ara kamata amma babu yadda xatayi sai abinda Haleeman ta yanke dole take daurewa take nunawa bata bayan sa, sai da suka fita daga gidan sannan ta koma ciki jikin ta a sanyaye.
Jinginar da kanta tayi jikin motar idon ta a rufe babu abinda nake sha'awar ci sai shawarma yawu sai tarar mata yake baki in ta tuna da shawarma gashi bata tunanin zata iya fad'a masa zata ci, dan k'aramin tsaki taja ta bud'e jakar ta ta jefa alawa a bakin ta ta mayar da kanta ta jingina idon ta a rufe, jin da tayi motar ta tsaya ya saka ta bud'e ido ta kalli inda suke, waje ne me kyau da tsari shiru babu hayaniya sai sautin mota kad'an, kallan wajan tyi ta kalle shi tace, "ina ne nan?." "Hotel ne?." Ya fad'a fuskar sa a had'e shima yana kawar da kai gefe, cike da mamaki tace, "meyasa ka kawo ni hotel?." "Magana zamuyi". "Okay, kaf fad'in gidan mu babu wajan magana sai munzo hotel? Kaga ni ka mayar dani gidan mu ko kuma na fita na tafi akan me zaka kawo ni hotel?." Ajiyar zuciya ya sauke ya kamo hannun ta duka biyun ya zuba mata idon sa da suka fara washewa daga jah yace,"Haleematu" sai da tsigar jikin ta ta tashi sabida yadda ta ambaci sunan da wani irin salo me d'aukar hankali, maimakon ta amsa sai ta kawar da kai daga kallan sa ta mayar da kanta ga taga ba tare da tace komai ba, "ki amince mu shiga ciki kuyi magana Dan Allah Dan annabi badan halin Fahad ba." Jin yadda yake magiya yana rok'on ta kamar itace mijin yasa tace,"naji" a fusace ta fad'a tana zare ido irin an dame ta din nan, murmushi yayi kafin ya bud'e ya fita ya barta a ciki, jim k'adan sai gashi ya dawo ya zagayo side din ta ya bud'e yace," Bismillah gimbiya" sai da ta d'ago ta zabga masa harara ta d'aure fuska kana ta fito ya kalle motar  yana murmushi suka shiga ciki.Yana bud'e dakin suka shiga ta k'arewa d'akin kallo tana tab'e baki ta samu waje ta zauna tare da jan dogon tsaki tace,"Sai kace wata karuwa an kawo ni Hotel koda yake ai na saba zuwa dole a d'auko ni a kawo ni nan" ta fad'a rai a b'ace, yana jin ta sai ya runtse ido yana jin haushin Kansa da ya furta mata wannan kalma ta Karuwa! Tsugunawa yayi a gaban ta guiwa biyu ya zube ya rik'o hannayen ta duka biyu yana matsawa a hankali ya kalli cikin idon ta tayi saurin d'auke ido yace,"Na cancanci kiyi min hukuncin da yafi haka Leema komai zakiyi min indai zaki huce kiyi min nidai buri na ki amince dani matsayin mijin ki, Haleema ina sanki ina kuma qaunar ki kin sani kin kuma fi kowa sanin hakan kin San dukkan abinda nake yiwa Hafsat ina yi ne Dan kiji babu dad'i kamar yadda nake ji ina yi ne dan kin sadaukar dani ba tare da kin lura da wanne hali hakan zai gefa ni ba, har biki na da Hafsat ya rage y'an kwanaki addu'a nake Allah ya dawo min dake cikin rayuwa ta sabida kece zab'i na kece wacce nake so  sai gashi Allah ya dawo min dake a lokacin da banyi tunani ba kika kuma zama matata mallaki na kuma sirri na harda ciki na ajikin ki, kece wacce kika sadaukar da farin cikin ki a kaina kika xauna dani a lokacin da bani da tunani ba tare da kinyi tunanin xan cutar dake ba kika amince min kika kuma bani kanki a cikin wannan yanayin da nake ciki, na zama butulu Nima na sani amma cikin rashin sani nayi hakan duk da baki cancanci hakan daga gare ni amma Dan Allah kiyi haquri ki yafe min" ya karasa fad'a a lokacin da idon sa yake k'okarin kawo ruwa.
D'an kawar da kai tayi sabida hawayen da suka cika mata ido tayi kokarin mayar dasu kana ta juyo tace, "Naji amma ka tashi daga tsugune a gaba na Dan Allah". "Bazan tashi ba Haleema sai kince kin yafe min laifukan da nayi miki". Runtse ido tayi tare da yin ajiyar zuciya tace, " Shikenan na yafe maka amma ban amince da cigaba da zama tare da kai ba kuma bawai na yafe maka Dan kalaman da ka fada bane na yafe maka ne on my on right, so ka tashi ka kaini gida bana San zaman nan wajan" ta fad'a tana k'okarin mikewa ya rike mata k'afafu ta koma ta zauna tana kallan sa da mamaki tace, "Nace na yafe maka ba shikenan ba? Dan Allah ka barni naje gida." Maimakon yayi magana sai hawaye suka fara zuba daga idanun sa ya kuma kafe su a fuskar ta yana karantar yanayin ta, Cize baki tayi ta kalle shi ba tace komai ba ta d'auke kai, shima shiru yayi ya rasa da wacce kalma zai bata hakuri ta hakura fuskar ta a juye tace, "kace na yafe maka na yafe maka to kuma me kake nema?". "ki kasance a tare dani har abada." "Wannan kuma ba Abu bane me yuwa saki na zakayi na Haifi wannan kaddararran cikin na dire maka d'anka nayi aure." "Kut na rantse da Allah matuk'ar ina raye baki isa ki auri wani ba bayan ni wai sakin ba'a hannu na yake ba? Nace bazan sake ki ba, kar kuma ki sake kiran ciki na da kaddara" a fusace yake maganar sai abin ya bata dariya har ta kasa b'oyewa ta dara ta dage gira d'aya ta kalle shi ta tab'e baki tace, "wai miji su miji manya, ni ai na jima na dad'e da daina amsa sunan matar ka sai dai matar me rabo." Ta kaishi kololuwar b'acin rai ya d'aure fuska yace, "Ko a yanxu na bar duniya dole kiyi min takaba da iddah har a gobe matsayin mijin ki nake ke har abada ma." Cike da rainin hankali tace, "Allah ko Malam Fahad? Ni kuma ban gani ba." "Zaki gani" ya furta a fusace tare da mikewa tsaye ya jawo ta da karfi ta mik'e ta fada jikin sa, ta bud'e baki zatayi magana ya had'e da nasa, duk iya yarda Haleema tayi ta kwace kanta abin ya ci tura tun tana ture shi har ta fara biye masa,
Kuka take sosai kamar ranta zai fita wani d'aci take ji a zuciyar ta ga kullewa da marar ta take sai abun ya taru yayi mata yawa ji take kamar ta bindige kanta sabida takaici, yana zaune ya kafa mata ido yayi rarrashin amma taki daina kukan dole ya kafa mata ido kawai yana kallan ta cike da so da kauna yana jin zafin hawayen ta da suke zuba. "Dan Allah ki daina wannan kukan" ya fada muryar sa a sanyaye Sam bai zata abin nata zaiyi zafi har haka ba da baiyi abinda yayi ba, banza tayi masa ya taso daga Inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna ya jawo ta ya kwantar a kafad'ar sa yana shafa gashin kanta yace, "ki daina Dan Allah ina jin zafi sosai." Bata tashi daga jikin sa ba ba kuma ta daina kukan ba sai ma kara volume da tayi,"Ya rabbi, Haleema Allah fa nace ya kamata ai ki daina." Runtse ido tayi sosai marar ta me juyawa ta cize baki ya d'go da fuskar ta yana kalla ido ta a kulle yace,"Me kike so nayi miki ki daina kukan nan?". "Ka fita" ta furta a hankali tana ajiyar zuciya. "Baxan iya fita na kyale ki kina wannan kukan ba kina bukatar na taimaka miki ki gyara jikin ki." Sai kuwa ta sake fashewa da sabon kuka, bai saurare ta ba ya sunkuce ta ya kaita bandaki ya sakar mata shower, hauka ta fara masa tana ya fita dole ya fito ya kyale ta tana wanka tana kuka har ta fito. Yana kallan ta ta karaso ta d'auki kayan ta ta koma bandakin ta saka sannan ta dawo sai a lokacin ya lura da cize bakin da take, da hanzari ya taso ya rike ta yace,"Me yake miki ciwo?." "Ina ruwan ka mu tafi gida." Har lokacin hawaye take yace,"Hmmm haleema kenan sai kuka kike ai ko zina muka aikata sai haka" harara ta zabga masa yayi murmushi yace,"Yanzu kin tabbatar da har yanzu ina nan matsayin mijin ki ko? To tun wuri ki daina ambaton saki Dan ni Fahad bazan sake ki ba har abada, Zuma ta Gaskiya Allah yayi ajiya a tare dake zak'i har kin zarce Zuma" ya fad'a yana kashe mata ido d'aya.
sai kawai ta sake fashewa da kuka yayi murmushi sosai yace,"yi Hakuri bazan sake fad'a ba amma fa gaskiya nayi enjoying sai na tuna da first night din mu nida ke kece kika sha wahala a hannu na amma kece kike taimako na a lokacin ban San nayi b'arna ba." Ya fad'a yana lek'a fuskar ta, ganin kukan take fa sosai dole ya d'auko mukullin mota suka kulle dakin suka fito. A mota ciwon marar ya dame ta ya kalli yanayin ta yace,"Dan Allah me yake damun ki?". "Mara ta" ta fad'a tana runtse ido sosai, "Subahanallahi muje asibiti kar kiyi miscarriage bana San rasa baby na, wayyo Allah na cutar da baby na da kaina". " A'a basai munje ba ba miscarriage bane muje gida kawai". "To meye? Nifa bana San ganganci da baby na gwara muje kawai." "I'm nurse, so kawai muje". Ajiyar zuciya yayi suka d'auki hanyar gida yana ta murmushi hannun ta yana cikin nasa yana murzawa tana so ta kwace amma ta kasa.
Su mummy suna shirin fitowa daga gidan suka shigo kowa ya tsaya har suka fito daga motar mummy tace, "ina ka kai min daughter na sai yanzu ka dawo da ita?" Ta fad'a fuska a had'e, zaiyi magana Mama tace, "tsakanin mata da miji ne ko ina ya kaita a mijin tane". Sosai yaji dadin amsar da ta bata yayi murmushi yana kallan Haleema, ita dai kunya kamar ta nutse haka sukayi sallama suka tafi Borno shi kuma Fahad ya koma gidan da su Mummy suka taso Dan yace bazai bar Kano ba sai Haleema ta amince dashi.
A daki Haleema tana ta b'ara tana bude abinda mummy ta bata turare ne masu kamshin gaske na Maiduguri ya ajjiye gefe sai ga Hafsat ta shigo ta kalle tace, " karb'i Fahad nasan magana dake akwai tsohuwar wayar ki ma ya kamata ki karb'a tana wajan Mama." Tsaki tayi tace, "Ni ba wani magana dashi da zanyi nifa sai dai ya sake ni." Zama kusa da ita Hafsat tayi tace, "meyasa?". " ni na tuna da abinda ya fad'a min ne wallahi sai naji na tsane shi na tsani cikin sa." "Innalillahi Haleema kina cikin hankalin ki kuwa? Mijin ki kike cewa kin tsana? Haba Hakeem a ina ilimin ki yake? Ansan ya b'ata miki amma ya nemi afuwar ki kuma kin tabbatar da San da yake miki ko?". D'aga kai tayi alamun eh, " to Haleema meyasa baza ki yafe masa ba? Duk laifin da yy miki bai kai Wanda nayi miki ba nice silar da ya saka yayi miki abinda yayi miki amma ni kika yafe min shi meye laifin sa? Mijin kine har yanzu yana da hakki a kanki komai kika yi masa na rashin kyautawa sai an rubuta miki zunubi, ki dawo Haleeman ki ta da Dan Allah ki yafe masa bashi da laifi ko kadan nice da laifi ni ya kamata ki hukunta bashi ba tunda kika yafe min babu Wanda baza ki yafewa ba Haleema ko waye ya b'ata miki a wannan abin da ya faru a baya na yake Dan Allah kiyi hakuri" ta karasa maganar muryar ta na rawa.kuka itama ta saka ta rungume Yar uwar tata sosai nasihar ta ta ratsa ta. Mama tana kallan su tayi murmushi ya bar wajan tana goge hawaye.
Tun daga lokacin Haleema ta d'an rage abinda take yiwa Fahad duk da bata sake sosai ba shima yaga canji har ranar da aka yanke ta zago ta bayyana zata cigaba da zama dashi, farin ciki wajan Fahad da dangin sa ba'a magana cikin satin aka kawo lefe dan sati me zuwa aka saka zata tare har da su kunshi an mata gyaran jiki ne ba'a zage sosai anyi ba sabida cikin jikin ta andai yi na fata da Dan abinda ba'a rasa ba, sati ya zagayo akayi walima aka tasa keyar haleema zuwa Borno.
Farin ciki da kwanciyar hankali da soyayya ita suke shimfid'awa a gidan su gwanin sha'awa har lokacin dawowa aikin sa yayi ya tattaro ya dawo Kano ya siyi gida a wajen gari yaje makarantar da haleema take ya nema mata aka bata level 3 sabida tayi asarar watanni da yawa dole ta dawo ta maimaita shekara daya. Koda taji labari tayi farin ciki sosai  bayan ya koma suka tattaro suka dawo Kano ta cigaba da makaranta. Cikin kwanakin Allah ya kawowa Hafsat mijin aure aka saka lokaci wata uku haka su Khamis ma akayi sa'a aka tsayar da lokacin bikin d'aya.
Lokacin cikin haleema tana da wata takwas aka sha shagalin biki aka kai amare gidan su.
Kwanci tashi babu wuya wajan Allah haleema ta haifi y'arta kyakkyauwa mai kama da Fahad aka saka mata suna Maryam wato sunan Maman Haleema aka kiran ta da Janan. Ansha shagalin suna anci ansha bayan suna da wani kwanaki ta koma schl, kwanci tashi sai gashi yau Haleema ta gama rbuta National exams din ta tana result.
Bayan result ya fito aka sama mata aiki a asibitin Murtala b'angaren A/E ta fara aikin ta cikin kwanciyar hankali tana kuma rainon y'arta.
Haka rayuwa ta cigaba da kasance a gidan Haleema da Fahad ta farin ciki da soyayyar juna.

*Alhamdulillah.*
*Friday 11/3/2022*

*_A nan na kawo karshen wannan labari me suna ZUCIYA CE kuskuren da nayi a cikin sa Allah ya gafarta min abinda na fad'a dai-dai Allah ya yafe min._*

_Labarin Zuciya ce yana kunshe da abubuwa da yawa na farko: ga iyayen mu masu nuna banbanci a tsakanin yaran su hakan ba karamar illa bace domin yana jawo tsana da gaba tsakanin y'an uwan, shaidan kuma zai dinga inziga mutum wani har ya kai ga kisa. Na biyu: ribar Hakuri kamar yadda hausawa suka ce mai hakuri zai iya dafa dutse sha roman sa. Na uku: ba lallai ne duk abinda kake so ka samu ba akwai wani tanadi da Allah yayi maka Wanda yafi zabin ka alkhairi, duk wanda yaga yana nemi Abu bai samu na Indai yana Neman zabin Allah akan hakan to ba alkhairi ne a tare dashi ba alkhairin yana gaba zai kuma zo ya riske shi a duk Inda kake._
_Fata na Allah ya saka wannan littafi ya saka masu hali irin na Hafsat su nutsu su canja, haka me nuna fifiko k'arara akan yaran sa ko uwa ko uba su dinga k'okarin b'oyewa sabida gudun b'arna, Allah yasa a amfana da abinda yake cikin labarin._

*_Godiya ga Aminiya ta Ummu Nabil🥰😅 Allah ya saka miki da alkhairi kinyi kokari wajan ganin labarin nan an gama shi lafiya. Oum Ramadan uwar daki na  ina godiya matuka Allah ya kara basira._*

*_WhatsApp fan's, wattapad Fan's ina miko sakon godiya ta a gare Ku Allah ya saka da alkhairi ya bar kauna ya kuma bar zumunci, kun bani goyan baya wajan ganin labarin nan yazo karshe Allah ya saka muku da alkhairi amin. Albishir gare ku sabon Littafi na mai take MUWAFFAQ yana nan tafe maybe bayan sallah maybe kuma Kafin sallah, zaku ji dadin labari sosai da sosai domin labarin na daban ne yana kunshe da rikita-rikitar soyayya me ban dariya😂 Allah ya sada mu da alkhairin sa._*

Comments and share.

❤ZUCIYA CE❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora