Page 7&8

38 4 0
                                    

*ZUCIYA CE*

*7&8*

Tun bayan fitar Hafsat daga d'akin ta take faman gurshek'en kuka ta rasa gane kukan me take yi, bata son irin wannan sab'anin da yake shiga tsakanin su da yayar taa ko kad'an, sai da ta gaji da kanta kana ta mik'e ta shiga band'aki ta d'auro alwala ta fito ta zauna a bakin gado tare da zabga uban tagumi.

Har aka idar da sallah bata ji motsin kowa a falo ba sai a lokacin ta tuna itace da girkin dare jiki a salub'e ta fito falo Hafsat Na zaune akan kujera tana kallan tv, maimakon tayi kitchen sai ta k'arasa inda Hafsat take tace, "Aunty Hafsat dan Allah kiyi hak'uri wallahi shine yace na shiga motar sa amma tunda bakya so bazan k'ara ba." In ta amsa to remote d'in dake hannun ta yayi magana ganin hakan yasa ta juya ta nufi kitchen dan abin ya so.a 6ata mata rai itama, ai laifin Fahad ya kamata ta gani ba laifin ta ba.

******

Tunda Hafsat ta kashe masa waya yake zaune a wajan ya zubawa wayar ido kiran sallah kad'ai ta tashe shi yaje yayi sallah ya dawo ya zauna tare da yin shiru ya kasa koda motsin kirki, shigowar Yazeed ya saka ya kalle shi kafin ya mayar da kai k'asa yana furzar da iska daga bakin sa, "A'a Fahad qalau kake kuwa?."

Sai da yayi ajiyar zuciya sannan yace, "Lafiya lau kawai Hafsat ke bani mamaki wai har ni zata kashewa waya ta kira ni kuma tana yi min ihu kamar wani mate d'in ta?."
"To uban y'an san girma me kayi mata?." Bai 6oye masa ba ya bashi labarin kaf abinda ya faru ya d'ora da fad'in, "Ina sane naki kiran ta har naje Borno bata kira ni taji ya na sauka ba dana kira ta kuma bata amsa ba amma ni zata dinga yiwa tsawa a waya."

"Gaskiya bata kyauta ba ita kishin nata ma harda k'anwar ta?, tab tana da aiki wallahi." Mik'ewa Fahad yayi tare da d'aukar makullin mota Yazeed ya kalle shi yace, "Ina kuma zaka?." "Zanje gidan nasu ne sabida kada kishin ta yaja ta aikatawa baiwar Allah wani abun bata ji ba bata gani ba gwara naje" bai jira abinda Yazeed din zaice ba ya fice da sauri.

Lokacin da ya shiga unguwar ana kiran i'sha sai da yayi sallah a masallaci sannan ya k'arasa gidan, parking yayi kamar kullum ya zauna a cikin motar tare da kiran layin Hafsat, a lokacin suna zazzaune ana shirin cin abinci wayar sa take shigowa tana gani sai tayi banza ita a dole fushi take dashi, dogon tsaki yaja tare da fitowa daga motar dai-dai shigowar Khamis ya dawo daga masallaci, "A'a Fahad!" ya fad'a cikin sakin fuska yana k'arasowa inda yake.

Musabawa suka yi Khamis yace,"To ka tsaya a nan ka k'araso ciki mana ku gaisa da Abban yana nan ai." Baiyi musu ba suka nufi hanyar falo daman can ya ke son zuwa shima.
A can falo kuwa Hafsat ta kalli Abban su da yake cin abinci tace, "Abba d'azu wani ne ya ajjiye Haleema a mota."

A fusace ya ajjiye cokalin hannun sa ya tattare naman goshin sa yace,"Kamar ya wani ne ya ajjiye ta a mota? yi min bayani dakyau yadda zan fahimta."
"D'azu taje school yin printing d'in assignment tayi almost 3 hours da tafiya kuma da sunan printing kawai sai yamma can wani ya ajjiye ta a mota ni kuma lokacin naje gidan su Rufayda karb'o assignment."

Kallan Haleema yayi idon ta da ya ciko da kwallah murya na rawa tace, "Wallahi Abba mota na rasa kuma ba wani ne ya kawo ni Fahad ne Wanda zata aura tun d'azu ta tambaye ni kuma na gaya mata."
"Wallahi Abba k3arya take ba Fahad bane shi yana Borno ma baya kano balle ya kawo ta."

Abba zaiyi magana Khamis da Fahad suka shigo da sallamaFahad da yaji abinda Hafsat take fad'a yayi murmushin takaici tun daga bakin k'ofar yace, "Abba Gaskiya Haleema take fad'a nine na kawo ta nima hanya ce ta bi dani ta makarantar tasu sai na ganta tsaye a kan titi gashi yamma tayi shiyasa na tawo da ita."

Hawayen dake idon ta suka sakko ta runtse ido zuciyar ta na harbawa da sauri,  murmushi Abba yayi cike da gamsuwa da maganat Fahad yace, "ka kyauta, k'araso mana ka tsaya a nan kamar bak'o."
K'arasawa yayi suka gaisa cikin girmamawa ya tambayi Mama akace tana d'aki, "Abba zan koma daman zuwa nayi na gaishe ka."
"kai madallah nagode naji kuma dad'in zuwan ka in badan kazo ba da nayiwa Mama na mummunan zato nagode."
Murmushi yayi kawai kafin yace, "A gaida Mama, sai anjima" ya fad'a yana fita daga falon.

❤ZUCIYA CE❤Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon