PAGE 1

44 6 13
                                    

Helllllo Lovelies
Am back again with another stunning Hausa/English novel,Nemesis Of Ayeesherh which is also a free novel....

Jos,plateau state Nigeria.
Monday,7:55am
Its a medium sized room containing not much things,just a bed,a bedside drawer and then a large wardrobe..
She quickly grab her veil and bag and dash out of the room after glancing at the time,,she head to the room opposite hers wrapping her veil around her shoulders,she opened it after saying"assalamu alaikum" in her very calm,gentle and pleasant voice,a voice of an averaged age woman gives her the permission to enter,"mama na tafi" she said as she enters,"sai kin dawo,aisha kiyi abinda ya kaiki,inkinga dama kuma sai kibi kawaye Allah ya bada sa'a"the averaged woman answers her,,
"Ameen mama insha Allah" said aisha after listening to what mama finished saying,she then moves out of the house adjusting her side bag's position,she had to trek to the road before she gets napep and she is running out of time already,,as she is walking,she keeps on thinking of their conversation with baba last night and what mama told her earlier,,"Aishatu,we discussed these after you graduated from your secondary school and i will still repeat it today,if you have any suitor then you are free to send him,you can study after you get married there is nothing wrong with that"
Well she is A'isha Joda,the second born of Alhaji muhammad jodah and Barrister Maryam,a girl with unique attitude,in hakuri yana yawa toh tabbas hakurin Aisha ya mata yawa,batada problem koh kadan zaku iya one good month tare da ita bata taba bata maka rai ba,she put others first a duk abinda zatayi,koh da ita zata cutu indai zata faranta maka rai shikenan..
Tana da friends sosai amma duk cikinsu toh zainab itace babban kawarta,babu abinda bata sani ba a tattare da ita,Aisha mutum ce mara boye boye da munafirci hakan yasa duk kankantar abu toh bata boye ma zainab,hatta da maganar da sukayi da baba jiya sai da ta fada mata yanda sukayi,tanasan zainab so na jini so na yan uwantaka,tare suka fara tindaga Jss 1 har Ss3 a Al-iman secondary school though ita zainab scholarship tasamu,harta da wasu litattafai da kananan payment duka aisha ce take biya musu koh ince baban aisha ne yake biya musu hakan ne yasa iyayensu ma yin sabo har suka zama kawaye suma...duk da iyayen zainab naja da baya ganin su ba masu hali bane amma sam iyayen aisha basa nuna hakan...
Khaleed Muhammad Joda is her only senior brother,a rayuwa bayan iyayenta,daga shi sai zainab take kauna,bakaramin sansu takeyi ba da har inta zauna watarana takanyi sake sake a ranta sai dai ta barma zuciyarta tana jiran lokaci,,Khaleed yana masters dinshi a Malaysia inda anan yayi degree dinshi kwanan nan kuma ya koma domin yin masters dinshi...
Afrah da hanif sune kannenta,duka suna secondary school din da ta gama dan gaba dayansu nan suka attending tin daga nursery har secondary...
"Main camp mai adaidata"she said to the man that parked his napep in her front..
"Shiga muje",,she entered and sit beside a guy who keeps staring at her,she brought out her phone that is ringing,tasani dama it must be her,"hello kawata" ta fada bayan ta ansa wayar,,"wai Aisha kina ina,kinsan an fara lectures",ta fada kasa kasa sabida kar lecturer din yajita though the class is a little bit noisy,,"zee wly makara nayi,am on my way na kusa",,a 20 minutes drive took her to main camp na Uni jos,,ta mika mishi 200 naira,"ba chanji","kabarshi" ta fada tana shiga gate din not minding abinda na cikin napep din yake fada na tazo ta karba kudin zai biya...
Ta kusa hall din da ake lectures din taji wani irin iska ya bugeta a take kuma ruwan daya taru akan titin ya fesa mata a jiki,kawai da ido tabi motar batareda tace komai ba,kayanta bai baci ba sai kawai ta fito da water bottle din dake jakanta ta dauraye kafanta ta karasa cikin hall din tana mamakin hali irin na wasu mutanen....

"Alhaji,wai bazaka tashi bane"
The old woman that her age can't be predict says it tapping the bed,the person she addresed as alhaji who looks Masha Allah opened his eyes saying"Hajiya naji fa"..
He is saeed Bello saeed,the first son of the famous businessman Alhaji Bello,and late Hajiya zahra'u,,his mother died when he was at the age of 4,and his father married another wife after his mother forced him to,,his step mum Hajiya fatima has never been the good one..
Duk da haka he never disrespects her and still he is not afraid of her for a bit..
He is the only child of his mother...having four younger sisters Zahra,zainab(zee baby),fareeda and Halima(lily)...
Unfortunately,two of them have to inherit their mother's behavior,zee and fareedah though they are so much afraid of their only brother..
He mostly stays with his grandmother,who forced his father to remarried after 2 years of loosing his mother thinking that saeed lacks mother's love and yes he lacks it up to date..
"Alhaji,wai bazaka fito bane",he didn't answer knowing even if answers her she will keep on disturbing him,he is starting his master's degree today,not his Bachelor's degree but she keeps on disturbing,he quickly pick his car key and walk out of the room..
He met her at the dinning area and give her a side hug saying "Hajiya ina kwana",,"quickly have your breakfast and leave",before he answers her,he peeped at his phone,it him the only person that will disturb him,he pick the call and place the phone over his right ear,"yane",
"Kasan Allah,prof is here where are you right now?"
"Home of course"
"And you know the lectures is 8 kuma you are still at home har yanzu bayan kasan halin prof ba yau ka fara attending lectures dinshi ba"
"Common this is Ess Bee Ess we are talking about,i can't go and wait for a lecturer u know that"..
Hanging faysal yayi sanin saeed sai abinda yayi niyya yakeyi,,abincinshi yaci hankali kwance sannan ya fito ya kama hanyar main camp da masifan gudu kaman zai tashi sama,daya daga cikin halayenshi kenan shi baya driving a hankali.....

Batada wani walwala har suka gama lectures dinsu around 2,suna tafe suna hira dan fita bakin gate kowa ya samu napep din hawa,hira sukeyi kamar yanda suka sabayi tin a secondary school,dukansu kawayene sai dai kace wasu sunfi shakuwa....
Kowa ya samu napep banda zainab da aisha da dama da gangan sukaki hawa,they have something to talk about,kallanta zainab tayi tace"ina jinki",,"zee a titi muke,mutafi gida mana sai muyi magana achan",haka akayin kuwa,they head to aisha's house,gidan ba kowa sai masu aiki,a parlour suka zauna sukaci abinci sannan suka fara hira
"Zee munyi breakup da musty",tashi zainab tayi ta sha rawa sannan ta koma ta zauna tace"dama na jima ina jiran hakan,ae na fada miki ba sanki yakeyi ba kinki yarda",,hada rai aisha tayi tace"baki fa ji yanda akayi ba zaki daura ma mutum sharri,ni nasan yanaso na kawai dai bansan dalilin shi na yin haka ba,zee men are scary,na hakura da soyayya kila is not my calling,zuciyata ta karaya i can't love someone again na hakura na hakura",ta karasa cikin rauni,cikin tausayawa zee ta rungumeta tana fadin"karkice haka esha,komai zai wuce ki dena fadan haka,Allah zai kawo nagari",sai da ta comforting dinta,sannan ta tattara tace zata tafi,har sai da tasamu abun hawa sannan ta dawo a hankali take tafiya har ta kusa gida taji horn a bayanta,tana juyawa taga motar mama sai ta karasa suka koma gida tare.....
Washegari ba kaman jiya ba,da wuri ta shirya ta tafi lectures,dukda tanada sanyi amma in kaganta zakasan takara sanyi akan da,maybe sabida abunda ya faru tsakaninta da musty ne,yau ita ta fara zuwa a cikin friends dinsu gaba daya....
Lecturer baizo ba,sai kawai sukayita hira bayan su zee sun zazzo,,aisha na zaune shuru wata budurwa da bazata wuce su ba ta karaso wajenta tana murmushi ta zauna a gefenta,tace"sannu sis,am Zahra Bello Saeed,kefa?",murmushi aisha tayi tace"aisha muhammad Joda",daga nan sukayita hira sama sama har sauran ma hankulunsu ya dawo kansu suka cigaba da hirar tare har sai da lokacin next lectures dinsu yazo sannan suka maida hankalinsu kanshi.....

Ihu da sukaji anayi a gefe ne ya maida hankalinsu wajen,zahra na kallan motar tagane nashi ne ta kuma ji sunan da ake kira,hakan ya sa ta dauke kanta a hankali tana me cigaba da tafiya,kaman yanda aisha ma bata koh kalli wajen ba,matasa ne cike a wajen suketa ihun"Ess Bee Ess",har sun kusa wucewa,zee tace"dan Allah kuzo muje mu kalla",zahra tace"what is new about drifting,mu tafi kawai infact yunwa nakeji sosai",aisha bata tanka musu ba illa cigaba da tafiyan da tayi hakama zahra bata sake cewa komai ba sukayi gaba yayinda zee suka tsaya debating da zuciyarsu na suje su kalli drifting din da akeyi,zee ce ta fara isa wajen sannan sauran sukabi bayanta....
Sai da su aisha suka isa cafteria har sukayi ordern abinci a wani eatery dake wajen,tukun suka lura da sauran basu biyo bayansu ba,zama sukayi aka kawo musu ordern aka ajiye,wata waitress ce ta iso wajen da sauri tace"sannunku ladies,idan ba damuwa amuku take away",da mamaki suka tsaya kallanta,aisha tace"we didn't ask for that","i know ma'am,yanzu aka fada mana zaizo",zahra ce wannan karan tace"kaman ya zaizo,waye? Can you please go straight to the point?",ta karasa more in a commanding way not a question,,"Ess Bee Ess" waitress din ta fada tana dan sunkuyar dakai,kallan juna aisha da zahra sukayi,dan basu fahimci komai ba amma ita zahra taso ta fahimta sai tace"okay",tana kallan aisha,ganin aishan batayi magana ba yasa taji hankalinta ya kwanta,batasan ganinshi,bata kuma so ya ganta,bayan waitress din tabi ta karba takeaway dinsu ta dawo ta dau jakanta tana fadin"mu tafi masallaci,sai ki kira su zee su samemu achan",hakan akayi da dan sauri take tafiya dan bataso yaganta koh a hanya ne ma,aisha ta tsaya kiran zee din motoci ukun da suka taho a jere badan tayi saurin yin baya ba da sun bugeta,gaba daya sun tada kura a wajen,jin zee ta ansa ne ta maida hankalinta wajen fada musu su samesu a masallaci sannan ta karasa wajen zahra da ta juya ma wajen baya suka tafi masjid.....
Da dan sauri suke tafiya ganin Hadari ya hadu,sabida yanayi na damuna..bayan zahra ta sauke wayan dake kunnenta ta kalli aisha tace"ku tsaya azo akaimu gida",girgiza kai aisha tayi tace "karki damu,yanzu zamu karasa gida insha Allah",haka kememe aisha taki yarda ta tsaya amma zee tace ita zata jira,so tare gaba dayansu su aisha suka fita,suka bar zee da zahra akan zaazo a daukesu...
Hanging video call din tayi tana kallan afrah dake saka kayan bacci tana mata magana"ya aisha ai nadau bazakuyi bacci bane",harararrta aisha tayi tace"kwana zamuyi da muna wayan",,"cool down sis,wlh naji zahrahn nan ta birgeni",aisha bata sake kulata ba ta juya tayi kwanciyarta,itama dai lokaci daya taji zahran ta birgeta,daga dazu da suka hadu zuwa yanzu she knows alot about her,yanzu ma sun kusan 30 minutes suna video call,tanata bata labari akan siblings dinta,the secondary she attended and alot more....

11:20pm
Hajiya ta kalli agogon dake manne a parlournta,lokacin kuma taji shigowar motarshi da tin daga farkon layin akejin bugun speakernshi,da sallama ya shiga parlourn kaman bashi ya sauka a mota mai beats din nan ba,zaro ido yayi ganin hajiya na tsaye dukda ba bakon abu bane,kafin yayi magana hajiya ta rigashi da fadin"wlh alhaji nidai bazaka sakamin ciwo ba,zaka tattara gobe goben nan ka koma gidan ubanka nidai bazaka kasheni lokaci na beyi ba",dariya yayi yace"hajiya bacci kikeji,kije ki kwanta abinki,akwai abinci",bata kulashi ba ta wuce daki tana kwafa,dining ya wuce yaci abinci sannan ya wuce dakinshi bai kwanta ba sai da yayi waya da yanmata sunkai biyar,kuma ba wacce ya kira duk su suka kirashi...
Meerah"s Pen🖋

Nemesis of Ayeesherh(on Hold)Where stories live. Discover now