Kamar yanda ya mata alkawari haka aka daina koran mutane a cafteria,kullum insunje a bude take indai ya tashi cin abinci haka yake hakura yaci acikin mutane though shi kallo da munafurci na mata ya tsana,ayita nunashi ana kallanshi amma haka yake dannewa ya hakura yana gamaci su tattara da zugar sa suyi gaba dan su dama basa zama waje daya..
Ita ta futo last daga lecture hall din ta samu kasan bishiya ta zauna tana jiran su dawo daga sallah dan ita her monthly friend visited her jiya,wayanta ta dauka ta karema fuskarta kallo ta duhun screen din sannan tayi tsaki tana shafa fuskar,a haka suka zo suka sameta suma suka zazzauna a resting benches dake wajen...
Hira suka dan fara sama sama dan ba yunwa sukeji ba basu ma dade da shigowa cikin school din ba,zee tace"lets play the game we played the other day" a take gaban aisha ya fadi ta dauke kai dan dama she is not in the mood,nan kowa yayi naam da shawarar zee,kusa da aisha zee ta dawo tace"yau kam u are not escaping",kin kulata aisha tayi,sai ma wayarta da ta dauka ta dialing numbern zahrah dan jin dalilin rashin fitowarta lectures yau din...
Bata dauka ba sai ta maida wayar ta ajiye cikin jakarta,tana maida hankali wajen wasu da suke lectures tare dasu suna musu sannu,wani ihu taji su zee sun sake ta juyo tana kallansu dan koh kadan hankalinta baya kansu bare tasan mai sukace,zee ce ta tabota tace"your turn",bata ce komai ba sanin ta musu alkawari dan haka ta zuba musu na mujiya tana jiran taji irin tambayar da zaa mata,gyran murya meenah tayi tace"TRUTH OR DARE",,sarcastically a'isha answers with"DARE" tana juya musu idanu,sai kuma tayi sauri tace"No,no truth",dariya sukayi zee tace"nooo,no way ai kin riga kin zaba baa chanjawa that the rule",,hade rai tayi tana jiran taji dame zasu daring dinta,meenah ce har yanzu ta bude baki dan bata amsa,saudah tayi saurin amshewa da fadin"WE DARE YOU TO PROPOSE TO THE HOTTEST GUY A MAKARANTAR NAN",ihuu wajen ya dauka hadda wadanda sukazo wucewa sukaji mai aka fada..
She feels blank and shocked,as in she can't even explain the mood she is in,it is something she never experienced in her life yanayin da take ciki,kawai da ido take kallansu,tanaganin kamar ba itace a zaune ba,masu rawa nayi sai shewa wasu sukeyi,wasu kuma na magana amma she is not understanding any of them....Ahankali ta sake juwaya ya zamana tana facing afrah da ta dade tana bacci,tanajin dama ace itace afrah da bata da wani problem,its been hours tinda friends dinta suka daring dinta amma maganar na nan yana yawo a kwakwalwarta batasan dalili ba,tasan tana iya dakewa tace bazatayi ba ya zauna kuma duka friends dinta ne they were together since childhood,they were together through the good and the bad times,why is she feeling strange batasan dalili ba..
Ba abun damuwa bane a wajenta dan taje tayi proposing ma mutum kuma intagama ta fada mishi it was a game,she sees nothing there amma meyasa zuciyarta takeso ta maidashi babban abu,tasan koh ma waye hottest guy din will understand idan ta fada mishi game ne,blanket din ta yaye ta sauka daga gadan ta wuce kitchen ta dauko bottle water mara sanyi sosai ta koma dakin nasu,kadan tasha ta koma ta kwanta dakyar bacci ya dauketa...
Washegari afrah ta sata agaba wai ta fada mata meke damunta amma sam taki fada,daga karshe dai afrah ta tafi school ta barta bayan taki fada mata,itama haka ta shirya kaman batada jini a jiki ta fito tayi breakfast,tana gamawa,baba na fitowa dan haka ta karasa inda yake ta gaisheshi har kasa kamar yanda ta saba,yana murmushi shima kamar koh da yaushe yace"ummina an shirya,Toh Allah ya bada sa'a" tace"ameen baba,injira zaka saukeni", ta fada ganin ya kama hanyar dinning,mama dake fitowa da jakanshi ne itama cikin shirin fita tace"bazakiyi latti ba,you know better than anyone ai yanda lecturers din Uj suke gwara ki wuce ki samu napep ki tafi",bata fuska tayi tana kallan baba,yace mata"zauna kayanki just few minutes and i will be done insha Allah",haka ta jira suka gama,mama ta shige tata motar ta fita,ita kuma ta shiga na baba suka fita suma...
Kamar an tsundumasu a aljanna haka sukaji jin angama announcing lecturer bazai samu zuwa ba,hakan yasa masu fita nayi,masu tsaki nayi,masu mita nayi sai bayan wasu mintuna sannan hall din ya dan daidaita,ana watsewa gaba dayansu suka dawo kusa dasu aisha da zahrah da zee,dan su tare suka zauna sauran ne suka zauna daddaya a jejjefe,,meenah tace"aisha ya maganar mu ne munji shuru fa",,"toh bazanyi ba,it either you change it or you forget about it",cewar aisha tana dauke kanta daga kallansu,zahra da batasan akan mai ake magana bane ta musu kallan bata fahimta ba,zee da bata shuru ta zayyana mata abinda ke faruwa,wani irin murmushi ne ya kubce mata,daga gani kuma kasan daga zuciyarta yake,maybe it is an opportunity ta sako yayanta,tasan gang dinsu basaji gaba daya,tasan kuma dole a cikin gang dinsu zaa samu Hottest guy din kamar yanda saudah ta fada,zatasan yanda zatayi,amma dole bazata bari wannan damar ta wuce ta ba,,hakan yasa tayi saurin dena murmushin tace"aisha zatayi,you must have to do it esher,show them you are capable of",ita dai aisha bataji dadi ba dan azatanta zahra ta goyi bayanta,bata tanka musu ba dan jin yanda zuciyarta keh race...
Kamar yanda zuciyar Aisha keh race haka na zahra ma keyi,she wants to ask them the question amma tana tsoro,tana tsoron taji abinda bashi bane,dakewa tayi tace"yau zatayi bama sai gobe ba,WHO IS THE GUY",kallan kallo suka farayi,ita kuwa zahrah rintse ido tayi dan jiran jin sunan wanda zasu ambata sai kuma taji shuru,ta bude ido a hankali tana binsu da kallo,sannan ta sauke ajiyar zuciya kafin tayi magana zee ta rigata da fadin"bamu sani ba,amma zamu tambaya",,zahra tace"zan tambaya mana insha Allah",meenah tace"mu tamabayi kawar adda,sake jamb tayi muka samu admission tare amma da yanzu ta gama degree dinta nasan maybe tasani tinda ita ta dade a makarantar" nan kowa yayi naam banda zahrah da ta so ta dage ita zata nemo,amma kar a zargeta yasa ta sharesu sai kuma Aisha da ta koma shuru tana sauraran duk mai suke cewa.....
Sai a next lecture dinsu kawar yayar meenah mai suna Nana ta zo,bayan lectures din ya kare har zata fita sai meenah tayi saurin tashi tabi bayanta lokacin tuni ta fice,tace abu zasu tambayeta,"ameenah wlh ana jirani,sai dai muyi waya koh muyi chatting koh ki bari sai monday",tana gama fadin haka ta kama gabanta yayinda ta bar meenah a tsaye speechless,cikin sanyi ta ja kafarta ta koma ta sanar musu da yanda akayi,babu wanda yaso jin haka sai aisha,ita kadai maganar ta saka farin ciki...11am ya hau motarsa yabar cikin Uj,yana driving kamar yanda ya saba da mugun gudu wayarsa ta fara ringing hakan yasa yadanyi slow down sannan ya connecting da bluetooth din motar da dama waka yakeji,yanayin yanda yaji muryar yaqoob yasan yana cikin damuwa,"speak up guy,banajinka sosai fa",,"Ess Bee Ess save me wlh framing dina sukayi,sun saka min white lady a jaka",ajiyar zuciya Saeed ya sauke yace"nasha fada muku stay away from those stuff,nikam bazanzo ba",,magiya yaqoob ya dinga mishi,hakan yasa har zai karya kwanan filin sukuwa kuma ya fasa ya cigaba dabin kan titin,"where are you?",ya tambayeshi kai tsaye,,"ina hanyar mista'Ali",hanging yayi yana jan tsaki dan niyyarshi ya tafi gida ya huta ma ranshi,yafi kwana nawa baiyi baccin da yakai 4 hours ba,zai kwanta late kuma ya tashi early sabida fitinar hajiya,shi yau bar mata gidanma zaiyi ya huta gwara yaje yayita ganin waccan munafukar matar....
Yana isa wajen police na isa gurin,har ma sunso su rigashi isa wajen motar yaqoob,hakan baisa ya fasa sauka ba although bai san koh dayansu ba,karasawa yayi wajen,daya acikin police din yace"ae abokanaye ne,kazo ka karba kenan",wani kallo saeed ya mishi hakan yasa police din jan bakinshi yayi shuru..
Su biyun police din suka hada suka arresting,bakaramin baci ran saeed yayi ba sabida shi koh taba bayasha,hasalima baiga amfanin shan abubuwan ba bare kuma har mutum yace zaiyi framing dinshi,,warning ya kashe ma police din akan duk wanda ya sake ya tabashi wlh baza ayi zaman lafiya ba,kuma yasasu dole kiran dad dinshi...
Bai dauki sama da 30 minutes ba Dad dinshi ya iso tare da hajiya,lokacin ana kan bincike...
Wani kallo ya ma police din dake mishi tambayoyi,koh daya bai amsa ba,dai dai shigowar Dad,da sauri Hajiya ta karasa tana fadin"Alhaji garin yaya,nasan sharri aka maka",kawai ta fashe da kuka,kallanta yayi ya murmusa ya girgiza kanshi,danshi baiga abin kuka ba,dakyar dai suka bama dad bail dinshi sannan suka tafi gida dan sun hana bail din abokin nashi....
Gaba daya gidanshi suka wuce,mum na zaune a parlour tana girgiza kafa tana waya,saurin hanging din wayar tayi dan batamaji shigowar motar ba sai sallaman Dad dake gaba,shi kuwa dakinshi direct ya wuce...
Hada rai tayi ganinshi tare da Hajiya,ta kwabe baki tace"sannu ina kwana",hajiya ba tareda ta saurareta ba tace"lafiya",sannan ta samu waje ta zauna,she barely comes to the house she only come for a reason haka zalika itama mum din,she only goes to hajiya's house when her husband force her to,,she seated there patiently waiting for Saeed she want them to leave together moreover Dad ask her to come with them...
Haka mum na zaune ta hada rai koh ruwa bata sa an kawo ma Hajiyar ba,dasauri mum din ta ajiye wayar hannunta when she remembered the reason why they went out together,she calls hajiya's name with a smirk on her face tana adduar tunaninta ya zamo gaske,juyowa hajiya tayi without uttering a word,,"amm dama nace basu bada bail dinshi ba koh daman na sani in sun kama masu kalan halin nan basu bayarwa,Allah dai ya kyauta dan....",maganar bakinta ne ya makale sanadiyyar jin sallamanshi,maybe he intentionally bounce in smilling,"mum sannu da gida",ya fada still smiling sannan ya karasa wajen Hajiya yace"sweetheart lets take our leave",tashi tayi tana fadin"okay,tell him to meet me outside" tana gama fadin haka ta fita...
Mum is shockinly looking at him,she doesn't even understand a single word he said,,kamar makauniya haka ta laluba ta shige dakinta ta kulle...she quickly dial his number knowing no one will hear her..."Yeah am home and fine sofy,you don't have to disturb your self" ya fada yana bude warmern dake gabanshi,,"okay" ya fada keeping the phone beside him...
Ahankali ya bude idanshi,looking at his phone ringing bayasan damuwa yau din nan he need to rest,tsaki yayi ya tashi ya fita dagashi sai three quater da vest,he opens the door,there she is coming,daman kaman ya sani,tsaki ya sakeyi ya juya ciki and left the door open....
The tall,chubby, fair girl quickly go in and engulf him in a hug,and he hugged her back bayanda ya iya,he love her,she mean alot to him,tana bashi care sosai..
Jikinshi ta fara dubawa bayan ta breaking hug din,"are you sure you are not hurt" girgiza kai yayi alamun he isn't,3 seater ya karasa ya zauna,bayanshi tabi ta zauna a cinyarshi,"what do you want to eat,so that i will make it for you",nan ma girgiza kanshi yayi alamun he need nothing
Gab isha suka fito daga part dinshi hannunsu cikin na juna,tana manne a jikinshi tana zuba mishi shagwaba,har bakin motarta ya kaita ya bude mata ta shiga,jin kara kunna mota ya sa hajiya leko window thinking shine zai fita dai dai lokacin kuma sofy ta ajiye jakanta a motar ta fito ta pecking dinshi a kumatu sannan tace mishing goodnight bayan ta hugging dinshi,part din hajiya ya wuce ya sameta tayi tagumi abin duniya ya ishe ta,sai harararrshi takeyi,toilet dinta ya shiga yayi alwala yayi sallahn isha,dan duk irin rashin mutuncin da yakeyi a gari sallah bata wucesa,masallaci ne dai bai cika zuwa ba sabida indai yaje toh bazai rasa wanda zaizo yana mishi magana ba wai waazi,shikuma baya san shishigi a cikin lamarinshi,sallah yazo ya tayar sannan ya dau keyn motarsa dake parlourn tin yamma yabar gida..."Mum,its okay if you don't want to share it with anyone,amma kuma ki dena saka damuwa aranki kinsan condition dinki",hararrta mum tayi tace"inaga dai zahra kece uwar nice yar,tashi kiban waje kan in bigeki" tashi zahra tayi ta ta bar mata dakin,tin da ta taso a lectures bataga mum din ta fito daga dakin ba kuma ta rabka tagumi kaman an mata mutuwa..
Meerah"s Pen🖋
YOU ARE READING
Nemesis of Ayeesherh(on Hold)
General FictionFind out the journey of a young kind hearted lady,who always prays and wishes good for everyone,who thinks she meet the Love Of Her Life along the way but was later snatched by the person she trusted the most....... What will happen when she thinks...