Page 4

10 3 0
                                    

"Waallaikumusallam,zainabu",cewar mama da zata wuce kitchen,shigowa zainab tayi ta gaisheta har kasa sannan mama ta amsa ta kara da fadin"yasu maman naki,yau fa nake cewa zan je amma kuma zan fita anguwa sai dai gobe","Allah ya kaimu mama,aisha fa?"
"Wannan kasar,ba abinda ta tsinanamin a gidan nan yau tana chan tana bacci bata ma tashi ba",murmushi kawai zee tayi ta karasa dakinsu aisha maman ta wuce kitchen har lokacin tana mita,sallamar zee ne ya tasheta a bacci,miqa tayi zee ta wani galla mata harara,murmushi tayi tace"sorry babes,few seconds",da sauri ta wuce toilet..
Zee sat on the bed scanning the room with her eyes,kullum tazo gidan she sees a new thing,duniyar tunani ta fada bata ma ji fitowar aisha daga wanka ba..
She quickly put on the same clothes as zee,which indicates shine ankon,abinci ta fita ta dibo musu,sukaci tass ta tafi mayar da plates din wayanta ya fara ringing,lokacin kuma zee ta shiga alwala dan azahar yayi,tana shigowa ringing din na karewa,wani kiran ya sake shigowa karasawa tayi ta daga wayan,ta picking at the same time tana kokarin shimfida musu praying mat..
Zaro ido tayi jin abinda khadeeja ta fada before saying"ki rufa min asiri,the last time i carried that car inaga samun admission dina ne mama ta dena maganar goge mata motar danayi",,tana warware hijab din dake hannunta daidai fitowar zee a toilet ta  sake fadin"my sister,no means no,ba ruwana dama ya khaleed na gari ne " tana gama fadin haka ta hanging ta saka hijab din ta hau kan praying mat daya tana jin tambayoyin da zee take mata,"wai motar mama zan dauka dan motocin sunyi kadan angwaye basu iso ba sunsamu delay and blah blah blah.." ta juya ta tada sallah...
"Zee why are you in a hurry bayan amaryar ma yanzu ake mata makeup",cewar aisha dake saka wayanta a jaka kafin tabi bayan zee da tuni ta isa parlourn,,"aisha have these,wai motocin are limited there idan kika goge min mota ni dake ne wlh" ta fada tana fita dan jiranta akeyi,,suma fitan sukayi..
Da gudu ta shige dakin mama tana murna,sai da hanif ya tsorata ya tashi zaune daga kwancen da yake,mama kam bata motsa ba tana kan sallaya kuma tasan aikin waye,harara ta daka mata sannan tayi kwafa ta cigaba da azkar dinta..
"Haba ya aisha wlh you scared the hell out of me",,"kai ya khaleed is coming a cikin week din nan",shima murna ya kamayi banda afrah da ta shigo tanajin bad news din dan ita da ya khaleed kamar tom and jerry basa shiri.....

"Yaya zayyad ashe kana garin nan",cewar aisha ganin wanda yayi sallama,,murmushinshi mai kyau yayi sannan ya samu dan nesa da ita ya zauna,zayyad na masifar san aisha tin tana karama,cousin dinta ne mamanshi da mamanta are siblings,kuma bawai ya hakura da santa bane yana nan acikin zuciyarshi kuma gani yake lokaci yayi da zai fara nuna mata,,"prettyn khaleed how are you?",,"am good,ina ammah?","bakisan hanyar gidanta bane" tashi tayi tana dariya..
"Mama look who is here",mama da ta fito a part din baba ta karaso cikin parlourn tana fadin"wato zayyad sai khaleed na gari kake zuwa gidan nan koh",adjusting zamanshi in a respectful manner yayi yana murmushi ya shafa kanshi before saying"a'a mama,ban ma dade da dawowa kasar ba shiyasa",,"Okay ya aikin naku,ina yaya","lafiya alhmdlh,tana lafiya tace agaisheki",,"ina amsawa,khaleed dinma yanzu ya fita","eyy sai da na kusa da na kirashi yace min ya fita amma yanzu zai dawo","okay" ta fada tana tashi tsaye...
"Yaya zayyad ina wuni",cewar afrah bayan ta ajiye mishi tray din hannunta,dan ita jiya ma taje gidansu kuma sun hadu,"lafiya kalau ya school,wait why are you all at home",,juya ido tayi tace"yau easter monday",,"ohh i nearly forgot,ina hanif?"
"Yana parlourn baba"
"Ohh is he home,bari na gaisheshi"ya karasa yana tashi dan zuwa gaida baba,,

Ahankali ta tura kofar bakinta dauke da sallama"Yaya thought yaya zayyad din bai tafi ba ae"
"Yanzu ya wuce wai ana kiranshi,shiyasa kika shigo a nitse?", cewar farin saurayin dake zaune,daga yanda yake zaune zaka gane ba wani tsayi bane dashi kuma ba guntu bane,basa kama da aisha sai dai yana kama da hanif,kuma dukansu biyun da baba suke kama,girgiza kai tayi dan asali maganar da tazo suyi ita ta nitsar da ita,"yaya kanaji",rage volume din tv din yayi sannan yace"am not deaf ae",she kept quite for some seconds thinking of where to start,,"yaya i know you are not in a serious relationship what i mean is that nasan kap cikin yan matanka babu wanda kake da niyyar aure,then why not give her a chance,yaya Dan Allah.." daure fuska yayi tin farkon fara maganar ta har takai yaji zata wuce gona da iri ya tsayar da ita"aisha don't call her name here,get out",,bata daddara ba tasake fadin"yaya what if aurenta is my last wish,yanzu dan wannan bukatar ne bazaka iya biya mun ba",wani irin tsawa ya daka mata sannan yace"i hate her,koh sunanta banasan kina ambata min a kusa dani idan kuma bakiyi wasa ba wlh har kawancen naku zan raba now get out of my sight before i slap you this should be the last da zakizo min da maganar nan" ya karasa yana mata wani kallo,tashi tayi sanin ranshi ya baci zai iya marin nata dagaske,tana tafiya tana tunani,,she knows it since when they were children zainab is in love with her brother,and she promise her self sai ta hadasu aure,sai dai why is her brother not cooperating,ta buga ta buga tin ba yau ba,tin suna secondary school taketa kokarin hadasu  sai dai farko ma yi yake kaman baisan mai takeyi ba da ta matsa ya fara kashe mata warning akan kar ta sake,indai yana kasar koh school zai tafi daukanta indai tare da zainab ne baya zuwa sai dai driver ya daukota koh kuma mama da ta girma kuma sai dai ta hau napep...

Nemesis of Ayeesherh(on Hold)Where stories live. Discover now