Ikon Allah ne kadai yakai Saeed gida dan baimasan hanyar daidai yake binta ba,yana shiga dakinshi ya dinga surutai shi kadai"Ni ba mazinaci bane,ban taba zina ba kuma bazan taba rayuwar aure da mazinaciya ba indai kuma dan zuwa club din danakeyi ake min kallan dan iska ma dena bazan sake ba bazan aureta ba" shi kadai haka ya dinga surutai har zuwa wani lokaci,karamin wayarshi ya sake dauka ya gwada numbern nan luckily ya shiga,tashi yayi ya zauna zuciyarshi nata bugawa,cike da yanga siriryar murya ta dauka da fadin"Hey",batareda yabi takanta ba yace"Who are u?" Murmushi tayi tace"Calm down,kanasan kasan koh ni wacece koh? Then ka fito kofar gidan da ka shiga yanzu" tana gama fadin haka ta kashe wayar,idanshi yakai kan agogo yaga few minutes to 9 tashi yayi ya zura jallabiya akan 3 quatern dayake jikinshi ya fice har ya futa ya dawo ya dau karamar wayar tashi sannan ya futa a kofar gate ya tsaya ya dialing numbern,a chaan neighborhood dinsu ya hangota ita kadai a tsaye sabida hasken security lights din da ya haska layin da farin kwayaye,a hankali ya gangara wajen ta sunkuyar dakanta,yana isa a fusace yace"who are u?" Dago kanta tayi ta zuba mishi idanu,sosai ya firgita abun ya bashi mamaki ganin Zainab a tsaye,yace"Zainab mai kikeyi anan? bakiga wata anan ba?" Murmushi tayi tace"tsayuwarmu anan is risky mu karasa ciki zan maka bayanin komai" tayi gaba shikuma kamar wawa haka yabi bayanta har suka isa kofar gate din,tasa hannu da sauri tayi knocking sai yayi sauri ya bude karamar kofar ya shiga,ahankali mallam mudi mai gadi da ya fito danjin knocking ya futo ganinsun shigo sai ya koma ya ajiye kujera a bakin gate din ya kawar dakanshi yanama Saeed addua a cikin ranshi,har part dinshi ya jagorance ta...
Bayan kamar 1 hour ta fito a firgice tana tafiya tana dingishi hade da dan sauri,ta fice tana waiwayen gidan...
Yana zaune a inda zee ta barshi yayi mutuwar zaune yayi nisa a duniyar tunani wayanshi ya fara ringing ba bata lokaci ya dauka,jin yadda take shashsheka ya dau key din motarshi ya fice da sauri har yana tintube,ganin saurin da ya fito dashi yasa mallam mudi bude mishi gate da sauri sannan ya koma daki....
Har kofar gida ya kaita,calmly ta juyo tace"Thank you" sannan ta sauka gyeda kanshi kawai yayi tana fita ya tada motarshi,tana shiga gida har lokacin bata bar kukan da takeyi ba a tsakar gida ta hadu da baba yana jin radionshi ya daga kai ya kalleta dasauri ta share hawayenta,tace"sannu da gida baba" yace"meyasa kikayi dare a waje yar baba? Hakan sam ba dabiarki bace dan ina dawowa gida nasameki kullum shiyasa yau bazanmiki hukunci ba a kiyaye gaba" kai ta gyeda a hankali sannan ta shige dakinta,tana shiga mama tabi bayanta tace"daga ina kike? Kince min gidan amaryar nan kawai zaki shiga,kuma dazuu ma na aika yaro da magriba yacemin bakya nan" shuru tayi dan batada amsar bama mama,kwafa maman tayi ta fice..
Tindaga ranar kuka ya zama abincin zainab indai tana gida,hakan yasa kullum idanta a kumbure yake dama fuskarta mama ta mata tambaya har ta gaji har yayunta ta taro sukazo suka sakata agaba suna tambayarta shuru tamusu,sabida tsabar starving kanta da takeyi har ramewa tayi sosai ga kuma zazzabi da yake yawan rufeta....
A week later....
Har yau zahrah bata koma gidansu ba tana nan a gidansu mum,yanzu ma zaune take a dakin yar autar su mum din tasu,wacce a kala zata bata shekaru biyu zuwa uku,gaba daya ta rasa meke mata dadi ita gashi ba wani kawance take da kawaye ba bare ace tanada friends masu yawa,gashi har yau ta kasa yima aisha magana domin so take aisha tasan mai takeyi so take aisha ta tashi ta kwatan ma kanta yanci dan koh kaffara bazatayi ba Zee munafuka ce..
Tana kishingide akan gadi tana Game a wayan Aunty Meenah,har anty meenahn tagama saka kaya sannan ta zauna a bakin gadon tace"ban wayata" marairaicewa zahra tayi tace"ayya barin gama wannan",tace "toh kunnamin data dan ni tin jiya ma ban hau online din ba" datan ta kunna sannan ta cigaba da game din messages na shigowa,mistakely hannunta ya shiga kan notification din WhatsApp din,har zata miqa ma anty meenah wayar hankalinta ya sauka akan numbern karshe miqewa tayi zaune ta shiga dp dan ganema idanta,tabbas profile picture din zee ne,hotonta ne akai ga kuma sunan contact din Zee mamah akayi saving,cike da zaro ido tace"anty meenah ina kikasan zee?" Fisge wayarta Meenah tace"wace zee kuma,nikam wasu tarikicen ma bansan inda nasansu ba" takarasa tana kallan hoton zee din,"auu zee mamah wai,kawata ce i knew her couples of months ago,ni banma taba ganinta physically ba infact i met her online" cike da mamaki zahrah ta gyra zama tace"Kawarmu ce tare mukayi part one din nan ma da ita,tell more about her please ni sau daya ma na taba zuwa gidansu kuma muna zargin ta mana laifi" anty meenah tana gyra zamanta a kan gadon tace"Keh da kuka dauki shekara guda da ita bakisan abubuwa akanta ba sai ni da bamu wani jima ba?",ta marairaice tace"bazaki gane bane,wlh anty meenah munafurci ta mana babba,wlh munafuka ce bazaki gane ba kuma keh yanzu baki santa ba zaki fara kawance da ita" rai anty meenah ta hada tace"karki yadda banasan iskanci jiya ma ina ganin kallan da kike ma kawata daga zuwanta,kike wani fice kika barta meye laifinta dan ta saka anklet,tana huji kunne masu yawa?,karkizo nan kinamin waazi malama ki tafi chaan kima wannan dan iskan yayan naki mai yawo da gajeran wando da yanmata ehe" abin yama zahrah zafi amma sabida ta samu cikar burinta tace"kiyahkuri anty meenah nifa ba fita nayi dan wani abuu ba,Saurayina ne yazo kuma baisan gidan nan ba shine naje dan Allah ki fada mai kika sani game da ita" sake fuska anty meenah tayi tace"yanzu naji batuu,ni wlh a wani group na hadu da ita namanta ma wani group ne kinsanni da shige shige,so anan ta dauki number na muke dan gaisawa har tace min itama a jos take amma yanzu haka tana abuja,shikenan abinda nasani nikam" cike da gamsuwa zahrah tace"oh wlh karya takeyi dan nikam tinda nake da ita bantaba jin tayi tafiya bama balle taje Abuja,ba wannan bama kiramana ita Dan Allah" sai da anty meenah tagama hararenta tana cewa kinsakamin kati ne sannan ta kira zee,ta saka a speaker bugu 3 ana 4 zee tayi picking da sauri zahrah ta miqa hannu ta danna recording,meenah tace"Babes ya?" Zee tayi dariya tace"komai normal,ai na fada miki bazai yuwu nazo abuja bai shigo hannu ba nake fada miki yanzu dai zuwa anjima zanje masa da bukatu na na karshe wlh fyade naso yawa shegiya amma sanin zaa iya hadasu aure kuma tsab indai Aisha ce zata yafe mishi sai kawai na chanja plan kedai zan kiraki na baki bayani" da sauri zahrah ta danne speakern taje kunnen meenah tace"ki tambayi sunanshi" sannan ta cire hannun,zee daketa hello hello meenah tace"nikam mai sunan gayen da ya sace miki zuciya ne haka,naga sai wani rawar kafa kikeyi akansa?" Zee tace"Hmm,bazaki gane bane wlh Saeed ya hadu,komai nashi daban ne,ina zuwa ga mayen chaan yusuf yana kirani zamu karasa magana online bye" cike da kaduwa zahrah ta miqe daga gadon ta bude wardrobe din antyn nata ta dauka gyele,ta dau wayarta ta fige 500 akan bedside ta juya zata fita sai kuma ta tuna bata mayi sending recording din ba,riqeta anty meenah tayi tace"wai meyene,kimin bayani please" ta rasa ta ina ma zata fara kuma batawani yadda da anty meenah ba amma kuma tana neman yaddan anty meenahn dan haka cikin dabara tayi summarizing wanda zata iya fada mata ta fada mata,meenah tayi tagumi tace"kinsan mai tacemin? Cemin tayi Ita da aisha duka friends ne da Saeed din,wai da aishan ta gane tanasan Saeed din shima yana kaman crushing dinta sai tayi caraff ta fara soyayya dashi ita kuma shine taje har abujan dan ta kwaceshin,kuma tace ba wannan ne karo na farko da aisha take mata haka ba indai akan soyayya ne tasha kwace mata saurayi shiyasa nayi supporting dinta da na nuna mata meye ne dalilinta da bazata bar kawance da aisha ba tacemin sun sabane amma zatayi kokari tayi baya da ita kinji yanda mukayi" idan zahrah har ya fara zubar da hawaye tace"Ya Saeed slapped me because of her,sabida ita nabar gidan hajiya,nazo nan sabida ita satinmu daya da aisha bama magana amma inaso aisha ta fahimci hakan koh na fada mata wlh ba lallai ta yadda ba dan na rasa wace irin mutum ce" meenah tace"toh meye kuma na kukan? Ni wlh sam wannan Saeed din naku ba birgeni yakeyi ba dan ya mareki sai akayi yaya? Na tabbata anty batasan da maganar nan ba da sai ta mishi double" zahrah ta share hawayenta tace"anty meenah ki taimakamin ya zanyi?" Shuru meenah tayi chaan dai tace"yanzu ba daukar jiki zakiyi ki samu ita aisha take koh who so ever ba,kibi ahankali kiyi komai a sannu ki fara tura mata audio din inta yarda ruwanta in bata yadda bama ruwanta meye zaki takura kanki wlh kikaje yanzu kila ta iya cewa kinasan shiga tsakaninta da kawarta ne tinda keh sama taka kika hadu da ita,ita kuwa suna nan shekaruu aruu aruu ni wlh blocking yarinyar zanyi ma dan ban zaci haka take ba ashe ma yarinya karama ce"
cike da gamsuwa ta tura audion daga wayar anty meenah sannan ta sending ma aisha ta whatsapp,sai ta dago tace"toh zanje gidan hajiya in fadama ya Alhaji"
"Wlh watarana ji nake kamar na kwadeki,shi yafi karfin ki tura masa ta whatsapp din ne?" Shima numbernshi tayi searching sannan ta tura mishi tana farincikin shiryawa da yayanta kwaya daya a duniya,ajiyar zuciya ta sauke tace"Ya rabbi kasa ba wanda zai sake shiga tsakaninsu"
Gefen aisha kuwa,ita gaba daya kullum wuni tunani take gaba daya ta rasa yadda zatayi da ranta,she need a shoulder to cry on amma bata dashi haka kullum take yini a daki gaba daya taji har wayarta ma ta isheta...
Yanzu ma zaune take a daki,gidan shuru dukda weekend ne,daga ita sai afrah a gidan,afrahnma tana chaan tana girki a kitchen data ta kunna tana dan chatting,har taga message daga Zahrah ajiyar zuciya ta sauke tace"bakiyi fushi dani ba" shiga chat din tayi taga audio ne zata kunna kenan sai taji tsayuwar motar mama alamun ta dawo dukda haka sai ta kunna ta tashi da nufin zuwa wajen maman...
Meerah"s pen🖋
Short chapter right? I apologize 🙏 typing is actually not easy...
Pls like,vote and comment...
Follow my page for more interesting free novels,thank u❤
YOU ARE READING
Nemesis of Ayeesherh(on Hold)
General FictionFind out the journey of a young kind hearted lady,who always prays and wishes good for everyone,who thinks she meet the Love Of Her Life along the way but was later snatched by the person she trusted the most....... What will happen when she thinks...