Page 13

5 0 0
                                    

Zaune suke gaba dayansu a parlourn Baba harda hajiya babba da ta hakimce akan 2 seater,suna hira sama sama aisha take jefa musu baki dan hasalima ita hankalinta baa kan hirrar tasu yake ba cike da gadara hajiya babba tace"Na saka ranar tafiya kuma Insha Allahu tare da Aisha zamu tafi" sai da mama ta daga ta kalleta kamar yanda gaba dayansu suka zuba mata idanu,in kacire aisha da ta jima da sanin zance sannan mama ta juya ta kalli aisha da sam hankalinta baya kansu,tayi ajiyar zuciya ita har ranta bataso haka ba amma tayi shuru batace komai ba,Baba yace"wannan ba damuwa Yaya,zaku tafi taje tayi hutunta" ya fadi hakan ne sabida sannin halin yayar tashi....
Jin ana kiran isha yasa ta sulale tabar parlourn kafin ta tada sallah wayanta ya fara ringing,tsurawa numbern ido tayi ganin zai tsinke bata dauka bane yasa tayi ajiyar zuciya ta dauka cikin sanyin murya tayi sallama,shima cikin sanyin murya ya amsa ya rasa ta yanda zai fara kamar yanda ita tayi shuru tana jira taji yanzu kuma da mai yazo,jin shurun yayi yawa ya sa ta sake fadin"Hello!" Ahankali kamar mai rada yace"Ayeesherh" sai da ta lumshe ido sabida yanda taji sunan ya daki kunnanta,she really missed him,she missed his voice she missed everything about him,sun kusa 30 minutes suna waya,cikin wayar da sukayi kuma bayan bata hakuri da yayi na yayanke hukunci cikin fushi kwata kwata bai ce mata ga abinda sofy tace mishi ba kamar yanda bai sake bukatan ta fada mishi mai sofy ta fadamata ba itama kuma bayan nuna mishi tadanyi fushi dashi babu abinda ta buka sani,dakyar dai sukayi sallama domin gabatar da isha....
Ranar kwanan farinciki aisha tayi,batasan meyasa shiryawarta da Saeed ya sakata farinciki ba,dagaske sun shaqu sosai kuma gani take Saeed na daban ne,batayi bacci ba sai da ta kirah zahrah ganin dare yayi yasa tace sai washegari in sunje exams zataje har gida ta nemi zee dan koh ta kirata baya shiga in ya shiga ma toh bata dauka...

Washegari kasancewar exams dinsu ba da sassafe bane har gida Saeed yazo ya dauketa ya kaita har school bai wani bata mata lokaci sannin exams zata shiga ya barta ya wuce office shima kanshi yana jadadda yanda yayi missing dinta a ranshi..
Tindaga nesa zee take hangosu,da lokacin da Aisha ta sauka a motar ta tsaya har tana dariya daga gani abu ya fada mata sannan ya tada motar ya juya,kamar ance ta juya ta hangi zee na tahowa hakan yasa ta tsaya cike da farinciki tana jiranta tana isowa tace"Zee kinsan koh yanda nayi kewarki,inata kiran numbernki bai shiga gashi kuma koh school munkai kwana nawa bamu hadu ba" wayar zee ta dago mata tace"a ruwa yaran anty sadiya ya jefamin wlh,ita kadai take kawo network ta dauke kuma bana ganin missed call nima nayi kewarki sosai" ciki suka karasa Aisha na labarta mata yanda sukayi da Saeed....
Koh da sukagama exams sai da aisha taja zee terminus ta siya mata karamar waya mai 3 sim ta bata,itadai zahrah tace gida zata tafi bata bisu kamar kullum in sun fita tare haka yau ma aka fara sauke zee sannan aka sauke Aisha...
Direct gidan dake jikin gidansu zee ta shiga,da faraa matar da bazata girmeta sosai ba ta amsa mata sallamar tana fadin "sannu da zuwa anty zee tamu" dariya zee tayi tana fadin"nifa nace a dena cemun antyn nan,ina wuni anty amarya" tace"keh ma ki dena cemun anty amarya sai na dena cemiki anty" batareda ta bi takan abun da ta fadaba ta miqa mata wayar da ta ciro a jaka ta cire sim dinta tace"gashi nagode,nan da jibi zan gama exams sai na baki wannan a matsayin tikwicinki" ta karasa tana nuna mata wayar da aisha ta siya mata,godiya anty amarya ta hauyi tin kafin ma abata wayar sannan ta fice ta cigaba da aikinta,ita kuwa sai alokacin ma abin ya sake tabota tayi wani murmushi sannan ta miqe ta fuce a gidan.....
Bayan isha dukansu suna zaune a parlourn kasa,lokaci zuwa lokaci suna kalan haka sabida Dad yaji koh da mai matsala yasa yake yawan zama acikinsu cike da kissa mum tace"Dad dinmu mun kusa samun surika fa" cike da rashin fahimta Dad yace"aina?" Ta sake fadin"Alhaji yanasan aje mishi tambayar aure" daga saeed din har kannenshi mata kallan mum sukeyi musamman Zahrah da bata taba sani da maganar ba,sannan suka dawo da Kallansu kanshi da tuni ya hada rai kamar ba maganarsa akeyi ba,ta sammaceshi beyi zatan zata mishi wannan abun ba Dad yayi hamdala ya kalla Saeed yace"Alhajina,naji dadin wannan maganar sosai ba dan kadan ba dan dama abinda ya kamaceka kenan tinda da karatunka da aikinka da komai wacece ita?" Ya karasa da tambaya,tini zahrah tace"A'ISHA MUHAMMAD JODA" wani irin rikitaccen kallo mum take bin Zahrah dashi,ta kasa cewa komai shima da mamaki yake kallan zahrah,sam beyi tunanin haka ba in ba data fada ba dan da daddy ya tambayeshi rasa ansar da zai bashi yayi,Dad ya jinjina kai yace"Masha Allah,bansanshi ba na taba jin sunanshi a wajen Alhaji Murtala ta dililin matarshi Barrister,zan kira Alhaji murtalan insha Allah" jikinshi a sanyaye ya tashi ya fice a parlourn,itama zahrah tashi tayi tabi bayanshi,sai da ta tabbar ta convincing dinshi kuma lokacin Mum tabar parlourn daki ta wuce direct tayi shirin bacci batareda tabi takan zee baby dake mata tambayoyin rainin hankali ba...
Idanta ta maida kan kofar da aka turo,sannan ta dauke ta maida kan littafi dake gabanta wanda a zahiri zaka dauka shi take karanta amma kuma sam ba haka bane domin tana wata duniyar tunanin daban karasowa afrah tayi ganin aisha ta zuba tagumi ta saka littafi agaba tace"yadai karatun no dey enter ne",kamar jira take afrah ta mata magana ta dago tace"Afrah ina cikin tashin hankali" da sauri afrah tace"menene,Allah yasa lafiya" asanyaye aisha tace"Saeed wai Dad dinshi yace zaizo" cikin rashin fahimta afrah tace"zaizo ina? Yayi mene?" A kufule kamar afrahn ce ta bata mata rai tace"Zasuzo tambaya mana" zaman dirshen afrah tayi akan tiles ta saki wata hamdala tace"Dan Allah ace suzo cikin satin nan,farinciki zai kasheni" tashi tayi ta kama rawa sai da aisha tayi dana sanin fadama afrah maganar nan dai tsokanarta tayitayi data gaji ta dauki wayarta ta kira zee dan tasan zahra tasan da maganar infact kilama tana tunanin ita ta hada komai zee na dagawa ta sanar mata komai,azaune zee take jin abinda aisha tagama fada mata sai da ta miqe tsaye ta cire dankwalinta takama fifita dashi,dakyar ta calming kanta tace"Besty kiyi hakuri abinda nakeso dake shi ne kiyi addua,if possible karki kwanta sai kinyi istikhara sannan ki ajiye maganar nan a gefe kiyi karatunki sai mun hadu gobe,take care" tanagama fada ta hanging wayar tayi cilli da ita.....
Washegari akufule Mum ta tura kofar dakinshi,yana shirin office ya daga kai ya kalleta kana ganinta kasan bata dade da tashi a bacci ba,batareda ta amsa gaisuwar da ya mata ba tace"Saeed haka mukayi dakai? Wacece kuma Aisha? Amanar Safiya zakaci kome,mai kakeso nace ma yarinyar nan da uwarta? Kamar ba dashi take magana ba haka yaba banza ajiyarta,ganin baisan ma tanayi bane tace"kayi iya naka,ka jira kaga nawa style din" sannan ta fice a dakin shi kalan ciwon kannanne yake hanashi zaman gida shi sam baya san hayaniya kayayyakishi ya tatara yaje ya zuba a boot din motarshu sannan ya dawo ya dibi sauran ya kulle kofar ya fice a gidan ranshi a bace....
Dakinsu Zahrah da Zee mum ta wuce,ba kowa a dakin dan dama su Zee baby duk sun tafi school toilet ta duba nan ma ba kowa tayi kwafa ta fice a dakin...
Dad da mum ne zaune da yamma gab da sallahn magriba,tanata kokarin convincing dinshi kan maganar aurenshi da Sofy amma yaki ma bata attention chaan wayarta ya fara ringing,ta miqa hannu tayi picking salati tayi bayan ta gama sauraran mai aka cemata a wayar sannan ta cire wayar a kunne ta riqeta a hannu,sai hawaye,a rikice Dad ya dinga jero mata tambaya"lafiya? Menene ya faru?"
Dakyar tace"Meyesa Saeed zai fada mata,wlh tana asibiti taje tasha pia pia zatayi suicide wannan wani kalan masifa ne tinda dai ya yaudareta meyesa kuma zai fada mata gashi nan a banza taje zata dauki rayuwarta"Dad dinma salati yayi kawai sannan yace"yanzu ya jikin nata? Hope tana cikin koshin lafiya" mikewa tayi tace"ina zan sani,badan nisan kwana ba ai inaga da ta mutu,pia pia wasa ne" tana hawaye haka ta wuce bangarenta bata kara mintuna 30 masu kyau ba ta fice a gidan ta wuce gidan aminiyar tata...
Bayan kwana biyu....
Aisha da dukka sauran friends dinsu na zaune a kasan wata bishiya mai dauke da resting benches,washegari zasu gama exams dinsu hira sukeyi dukkansu banda zee da ta kurawa wayarta kallo cikin sanyi jiki ta dauka hade da sallama,sai suka rage hayaniyar jin tana waya tana gamawa ta zuba tagumi cike da mamaki Aisha tace"menene Zee?" Zee ta dago idanta har ya cicciko tace"Aisha u asked me to give him a chance kuma nabashi har ya cemun zuwa next month iyayenshi zasuzo,aisha na dauka mutumin kirki ne ashe ba haka bane,look!" Ta karasa tana daga masu aisha screen din wayarta,tace"yanzu abokinshi ya kirani,yace bai san har maganata da yusuf takai aure ba da ya dade da bayyana min waye yusuf" zahra da ta danji tausayinta tace"Zainab bazaki yanke hukunci lokaci daya ba,bakida sheda maybe ma abokin nashi sanki yakeyi" ta girgiza kai tace"doguwar magana ma bata hadamu dashi,yana da mata ma",saudat tace"tashi zamuyi muje kofar gate din hotel din mu jira fitowanshi indai shine mu faffasa mishi motar mu musu duka shi da budurwar bashi kenan ba" aisha ta girgiza kai tace"no need meyene na sai an fasa mishi mota? Kawai kisan yanda zakiyi bincike indai hakanne ki fita harkarshi thats all" nan wata baka mara jiki tace"a'a gwara dai aje a tabbatar shidin ne in ba hakaba tana mace ta ina zata fara wani bincike" cike da sanyin zuciya zee tace"Ni banasan muje muna musu hayaniya ne a bakin waje" aisha ta tashi tace"toh muje mu biyu" zee tace"a a,munyi kadan koh zahrah tazo muje mu uku duk masifa babu wanda ya isa mana wani abun" cike da gamsuwa suka tashi dukkansu suka fita bakin gate sannan sauran kowa ya wuce gida sukuma su uku badan ran zahrah yaso ba ta bisu suka kama hanyar Hotel din....
Har harabar hotel din suka shiga babu labarin komai sun dauki awowi shuru,daga baya suka shiga har wajen receptionist din taki basu wani information jikin a sanyeye suka fito domin yamma tayi sosai koh wacce gida ta wuce bayan sun rarrashi zee akan dole zasusan yanda zasuyi kuma sun mata alkwari babu wanda zaiji xancen kamar yadda tasasu...
Meerah"s pen🖋

Nemesis of Ayeesherh(on Hold)Where stories live. Discover now