Da mamaki ya khaleed yake kallanta,yace"gidan ayya kuma? Su afrah dasu maimuna ba gidan mamy suke ba duka?" Trying hard to look normal tace"yaya banasan hayaniya ne,kuma kaga gidan nan ma anata baki ga kuma exams dinmu ma yana approaching inaso koh kadan ne in dan dinga yin karatu" shrugging yayi yace"okay,let me get the keys" daga haka ya juya ya wuce dakinshi ita kuma ta fita tana jiranshi a wajen mootarshi,its almost 3 days now amma abin yaki ya bar ranta,she wants to forget him and everything about him amma takasa everyone is asking her the reason why she is looking dull for the past 2 days,does he even have a place in her heart that way da har yake affecting mood dinta? She keeps on asking herself that question,wannan karan har zainab ta kasa fada mata damuwarta,ta bari a zuciyarta kuma gashi yaki barin zuciyartata,ana bikin da suka jima suna planning kasancewar an dan jima mace batayi aure a cikin familynsu mama ba,sun planning bikin Hafsa kamar mene sai dai bata so ta shiga hayaniya,inta shiga hayaniya jinta take kamar tayita tsala ihuu,few mutanen da suke gidansu yanzu haka sun dameta,batada wajen zuwa da yafi gidan ayya tasan chaan koh zaayi baki sai dai manya wanda sukuma ba hayaniya ce dasu ba,ankon bikin kanshi yana gidansu saudat har lokacin bata samu zuwa ta karbo ba,randa saudat ta kai mata school kuma ta manta bata karba ba har ta tafi gida dan zuwa yanzu ta kasa fuskanta friends dinta tace musu batada damuwa sai dai ta dinga wasan buya dasu,parking ya Khaleed yayi a bakin gate din tana sauke idanta ya sauka akan yaya zayyad dake fitowa daga gidan shima akansu idanshi ya sauka da murmushi ya karaso wajen,sai kuma ya bata rai checking her out yace"mai kika zo yi anan war haka bayan suna chaan suna shirin kamu" ya karasa yana kallan agogon dake hannunshi fitowa ya khaleed yayi a mota yana fadin"inaga mafarkin ayya tayi,tin safe take damuna na kawota nan" tana kokarin kawar da zancen da sukeyi ta ciro dan karamin jakan dake dauke da kayanta da kuma side bag dinta tace"bari na shiga mugaisa da ayya in fara shi kar time ya kure" daga haka ta shige gate din ta barsu a tsaye...
Tanata kallan kiran mama amma taki dagawa daga baya ma kashe wayan tayi dan tasan kwanan zancen wato afrah taje ta fada mata bataje kamu ba kuma kila ta koma gida ma bata sameta ba,dan dama bata fadama mama gidan ayya zata tafi ba duk a zatan mama gidan mami aishan zata koma kuma shuru har yamma tayi bataje ba har maman ta dawo gida kuma bata sameta ba tana kwance a kan sallayan da tayi sallahn laasar ayya ta shigo dakin tana fadin"Aishatu kinyi bakuwa" da mamaki ta tashi zaune tace"Bakuwa kuma Ayya,bawanda ya kirani a waya" sai kuma ta tuna wayan a kashe yake tashi tayi ta wuce parlourn ta samu zee a zaune akan kujeran dake facing tv,murmushi ta kakalo ta karasa ta zauna akusa da ita tace"ya akayi kikasan ina nan?" Da kamar zee baza tace komai ba sai kuma tace"Daga gida nake,nagaji da wasan buyan da kikeyi da ni shi ne na bi ki gida kuma chaan ma bakya chan sai aka cemun kina nan" cike da san fuskewa tace"wasan buya kuma? Ni da wa?" Sai kuma ta miqe tana fadin"bari na kawo miki ruwa" hannunta zee ta kama tace"zauna,banasan pretending tell me your problem" this time she can't hold it,dan she need someone to talk to,dama Kuma zainab din ce wacce take fadama damuwarta,itace kawai take bata shawara nagari cikin kankanin lokaci ta zayyana ma zee abinda ya faru,wanda tin lokacin da abin ya faru har yau Saeed bai kirata ba cike da jimami zee tace"Ki kwantar da hankalinki,insha Allahu karya takeyi,amma maybe he gave her that room,who could she be? but have u talked to zahrah about it? Ina ganin kaman zatafi saurin dai daita wannan al amarin",murmushin takaici aisha tayi tace"i can't confront her da maganar nan,if u can't do anything about it lets forget about it" itama murmushin zee tayi tace"bazai yuwu ba,kina cikin matsala kuma abar maganar, noo its can't be,nasan dole shi ya bata wannan damar idan ba haka ba meye ne alakar rashin kiranki da bayayi kwana kusan 3,indai ba yasan da zancen ba",aisha tace"Nafada miki kawai a rufe shashinshi,in yaga dama ya kira,in baiga dama ba kar ya kira nikuma i will never call him insha Allahu" sake girgiza kanta zee tayi tace"ban numbern i will call him myself inna samu time" tashi aisha tayi ta dauko wayanta ta kunna,ta kalla zee da tintini wayanta ke ringing tace"zee meyesa bazaki dauka ba? Dazu i thought dan muna magana ne" zee ta saka a silent tace"sharesa bazan dauka ba,wlh yusuf ne ya dameni tin last week yake damuna wai sai dai na bashi dama ya turo nikuma sam sam wlh azeem bazan iya aurenshi ba" aisha ta shiga numbern Saeed da tasan yafi waya dashi ta miqa ma zee tana fadin" yanzu zee fisabilillahi meye ne laifin Yusuf?yanada degree dinshi,yana aikinshi,yanada motarshi yanada kyau daidai nashi,toh meye problem din?
Zee tana copying numbern tace"Bazaki gane ba,he is not classy at all he is not even social,dan kauyene na karshe,ni kudinshi da rashinshi bai dameni ba bawani kudi ne dashi bama,ni dai yanzu barin na tafi dan wallahi dakyar mama tabarni na fito kinsan jiya naje birthday din sarah"
"Class kuma,wake duba wannan yanzu? Lemme ask u this,da me ya khaleed ya fishi da kike sanshi shi kuma yusuf baki sanshi?"
Waro ido zee tayi tace"nakesan sa kuma? Yaushe mukayi haka dake? Ae koh wallahi kinsan ya khaleed ya wuce ajin Yusuf sau dubu,he is classy,ga kyau,ga kwarjini keh ni share wani batun yusuf"
"In bakya sanshi what brings about all you say? zee,opportunity comes but ones this is an opportunity for you use it,do it at the right time inma bakiji yusuf ya kwanta miki ba kiyi istikhara and pray for the best Allah yanajinmu,menene wani class kuma?" tashi zee tayi tana fadin"insha Allah zanyi nagode"
Aisha ma ta tashi tace"amma kinsan da wa kike magana?" Dariya zee tayi tace"am trying to be a responsible woman kawata tace nayi aure" batareda aisha ta biye mata ba ta warware veil din kanta ta rakata har bakin titi ta samu napep sannan ta dawo gida,a parlourn ayya inda tabar wayanta anan ta samuu amma 3 missed calls daga ya khaleed,kafin ta kirashi har ya sake kiranta tana dagawa yace"tattaro kayanki ina waje" cike da mamaki tace"kayana kuma yaya,wanne" bai kulata ba yayi hanging wayar sake fita tayi ta sameshi yana kokarin shigowa gidan,yace"ina wasa dake ne? I have other things to do ba kaiki waje da dawo dake bane kawai,kinsaka kawai mama tazo tana min fada ni bada laifi ba,ki wuce kije ki hada kayanki ki fito mutafi",sum sum sum ta koma ciki ta hado kayanta ta shige motar suka wuce gida....
Batasan mama tana gidan ba sai da ta tafi gaida baba bayan magriba,kasancewar gidan shuru ne afrah na chaan gidan biki ya khaleed kuma sun fita tare da hanif..
Wani kallo mama ta bita dashi bayan ta gaisheta tace"Ni da kika rainamin dangi? Zakuma ki gaisar dani,yar yayata fa guda daya tak ita take aure amma kika wanke kafarki kika tafi gidan ayya,toh danma ayya ita ta haifi ni duk dai dangin nawa kikaje amma meye hanaki zuwa Aisha? Everyone was asking me ina kike,wasu ma zasuyi zatan na hanaki zuwa ne for what reason? Kifita dama ki tattara yanzu yanzun nan ki wuce gidan mamy kinaji na ai" batada yadda zatayi illa ta amsa ma mama da toh,haka bayan tayi sallahn isha ta tattara yanata yanata ta tafi gidan bikin dan hankalinta ya dan kwanta da ta fadama zee damuwarta,atleast tasan zata sasanta komai"
Washegari friday haka ta tattara ta tafi lectures din event din sai da yamma kuma akwai assignment din da zatayi submitting...
Haka aka gama biki aka watse takai amarya har gidanta ta kwana sannan washegari ta koma gida,ba laifi ta dan sake dukda har yau zee batazo ta ce mata gashi ba haka kuma itama batace ma zee komai dangane da maganar ba itama kuma bata kira zee ta tambayeta komai akai ba..Gefen Saeed kuwa,cire Aisha a cikin rayuwarshi is not something small,gaba dayashin yanajinshi wani iri kana ganinshi kasan he is not his self,koh da Dad ya kirashi ya mishi magana sai kawai yace mishi yanaso ya fara aiki,sosai hajiya taji dadin wannan maganar hakan yasa cikin kankanin lokaci Dad ya nema mishi aiki a NNPC,in yanada lectures yana zuwa Uj yana gama lectures din kuma yake fita,he just don't want to see her,monday to friday by 9 ya tafi office baya dawowa sai 4 koh abokananshi basa gane kanshi,ita kanta Sofyn da ta zama sanadiyyar shiganshi halin da yake ciki ta fara da nasani dan kuwa yanzu ne ma yafi distancing kanshi da ita cikin kankanin lokaci Saeed changes himself to someone u cant define....
Basu da yawa students din cikin hall din,daga gani an dade da gama exams a hall din..
Zahrah ta rufe zip din jakanta tana fadin"This is the last time da zan tambayeki,insha Allah"
Murmushin karfin hali aisha tayi tace"zahrah ba wai ina boye miki abu bane,kawai dai the only thing i know shi yanzu bansan meyasa ba kaman he is trying to distance himself from me bansan koh na mishi wani laifi bane, nafi tunanin maybe koh sabida aikin da ya fara neh bashi da lokaci" ita kanta in ka tambayeta batasan inda ta lalubo wannan karyan ba,dan abakin zahrah ma taji ya fara aiki,infact koh inda yake aikin ma batasani ba batasan ta fadama zahrah halin da ake ciki koh kadan,ta riga tayi deciding zata kira zee taji yanda ake ciki cox ta bata enough time,its couples of weeks now dakyar take surviving,shuru zahrah tayi tana tunani indai Saeed ya fara shareka toh tabbas kamishi laifi koh kuma kafita akanshi,toh amma meye dalilin da ya sa zai fara share aisha,laifin mai ta mishi?tasan aisha would be the last person da zata ma Saeed laifin da har zai sa ya fita a harkarta,"Aisha ni bansan na mishi magana,amma kuma insha Allah na san mai zanyi i promise you that,sabida you two are made for each other" aisha batace komai ba sai ma tashi da tayi tana sake gwada numbern zee,har lokacin kuma yana ringing amma kuma zee bata dauka ba,dan haka sai kawai tace"zahrah mutafi kawai maybe ta tafi gida tin dazu,but isn't
It strange ace yau kusan 3 days bamu hadu da itaba?"fita sukayi daga hall din zahrah na fadin"maybe she is busy"
Agajiye ta koma gida,ganin moto a fillin gidan kuma harma a parking lot shi ya bata tabbacin Hajiya babba ta iso,da sallama ta shige parlourn ta sameta kuwa a zaune akan 1 seater tana kallo tana shan fruits din dake gabanta,murmushi tayi ta karasa kasa gefen hajiya dake ta kare mata kallo tace"sannunku da zuwa Hajiya"
Hajiya da ta dena kasa kallanta tace"Aishatu kece kika girma haka? Kuma kike zaune har yanzu a gida?" Sunkuyar dakanta tayi tana fadin"Ina wuni Hajiya"
"Lafiya klau,ya makarantar?"
"Alhamdulillah muna exams ne ma",hajiya tace"Ahh toh masha Allahu ki ce tare zamu tafi kenan,Ahh toh toh abu yayi kyau,aji nawa kike yanzu?"
Tana kokarin tashi tace"part 2 zan tafi"
Hajiya tace"Toh toh toh,Masha Allah" ita dai batace komai ba ta mike ta shige kitchen danjin motsin mama achaan...Zahrah nata saka da warwara acikin ranta,har hajiya ta fito tace"Ikon Allah,toh baya nan bai dawo ba nima raban da na ganshi tin jiya da daddare,yau da safe bamu hadu ba har ya tafi office" bata rai tayi tace"Toh keh hajiya wayace miki wajenshi nazo,ba dama inzo gidan nan sai kice wajenshi nazo kuma in banzo ba sai kidinga cewa banzo ba,hajiya tace"Toh ni yanzu ae da zagina kikayi da yafi" batace komai ba sai ma tashi da tayi ta wuce kitchen tanema ma kanta abinda zataci sannan to koma parlourn ta zauna dan batasan ta shiga daki kuma ya shigo bata sani ba tinda hajiyar ma tana parlourn,tana gidan har aka kusa magriba,kiran mum tagani,ita tama manta bata fada mata nan zata wuce ba daga school dauka tayi ta sanar mata tana gidan hajiya tana gama wayar yana sallama a parlourn,zaune ta tashi tana kare mishi kallo dan baiyi kama da wanda ya dawo daga office ba tace"ya Alhaji daga ina?" Yana kallanta tsaf yace"Daga inda kika aikeni" tayi murmushi batace komai ba har ya zauna suna gaisawa da hajiya da ita take zaunen,sai da ya gama cin abincin da ta kawo mishi taga kamar fita zai yi tayi saurin cewa"yaya wajenka nazo fa" komawa yayi ya zauna yace"what is it?" Kusa dashi ta dawo ta zauna dukda ba kowa a parlourn tace"Yaya biki zamuyi,shi ne nakeso ka mana anko da aisha" murmushi mai kama da smirking yayi yace"And who is that?" Da mamaki take kallanshi kafin ta fadi maganar da take da niyyar fada yacigaba"Zahrah why would u let someone like her into my life,why would u let me be obsessed with her bayan kinsan halayenta its hurts me, this is something that will affect me har na mutu" yana gama fadin haka ya fita a parlourn gaba daya jikinta yayi sanyi,bata fahimtar komai kuma babu wanda zai iha fahimtar da ita sai aisha,zama tayi ta fara tunanin ganin bazai kai ta koh ina bane yasa ta tattara ta tafi gida........
Meerah"s Pen🖋
YOU ARE READING
Nemesis of Ayeesherh(on Hold)
General FictionFind out the journey of a young kind hearted lady,who always prays and wishes good for everyone,who thinks she meet the Love Of Her Life along the way but was later snatched by the person she trusted the most....... What will happen when she thinks...