A bakin titi mai napep din ya sauketa sam yaki shiga da ita cikin fillin sukuwa dan yamma tayi kuma tin washegarin randa ta fadama Dad aisha Saeed yakeso tabar gidan ta koma gidan Hajiya dan nanne kawai saukinta har sai mum ta sakko,a fillin gidan ta hangi yaya Saeed kafin ta isa har ya shiga cikin gida da sallama ta shiga,"Daga ina kike?" Waiwayowa tayi a tsorace dan batayi tsammanin yana wajen ba tace"Daga schl" yanda taga ya nufeta cikin yanayin da bata taba ganinshi bane yasa tadanyi baya a tsorace,ya cigaba da takowa har sai da yazo tsakiyar falon yace"Daga nan gidan ubanwa kikaje" gaba daya jikinta kakkarwa yakeyi bai bata damar bashi amsa ba,gashi gaba daya ta tsorata wayarshi ya juyo mata screen din,a firgice take kallan hotonsu ita da Aisha a tsaye a reception din hotel din dasukaje,suna murmushi gaba daya kanta ya cunkushe babu abinda takeyi sai hawaye dakyar tace"Wlh yaya"mari ya sauke mata ya hada mata da wani irin tsawa yace"Tarbiyyarki kenan,kalan tarbiyyyan da Dad ya baki kenan,dan kinje Uj kin samu yarinya kin biye ma tarbiyyarta,nan shekaran jiya kikazo kamar zakiyi kuka kina cemun ita kamila ce" jifa yayi da wayar har sai da ta bige bango ta fadi kasa gaba daya babu abinda takeyi sai kuka,dan ta ma kasa magana shi kuma tsabar takaici ya rasa ma mai zaiyi tana bude bakinta da niyyar bashi hakuri tamishi bayani yace"Keep it to yourself zai miki amfani,amma daga yau karki sake sakawa a ranki kinada yaya infact karki bari fuskata ta sake ganin take bare kuma naji muryarki now get out of this house" ya karasa cike da tsawa yana kuma nuna mata hanyar fitan,jiki na bari ta fita daga gidan tana tafiya tana hawaye haka ta wuce gidansu mum....
Tana fita hajiya dake tsaye a kofar dakinta ta karaso tace"mai ya faru?" Kallanta yayi kanar bazai ce komai ba kuma sai yace"bakomai" ya juya ya fice a parlourn,wayarshi ta karasa ta tattara dan ya riga yayi rugu rugu.....
Aisha ma koh da ta isa gidata samu wai Hajiya Babba ta tafi bauchi kuma tana dawowa zasu tafi,tabe baki tayi batace komai ba sai da taci abinci tayi Sallah sannan ta wuce dakin mama,har lokacin a zuciyarta tana jajen abun da ke faruwa da Zainab,a zaune a bakin gado ta sameta tanaa waya da yayarta,sai da ta gama sannan tace"Mama wai bakyasan nabi Hajiya babba ne?" Batareda mama ta kalleta ba tace"ina ruwana da binta da zakiyi? Nayii magana ace kuna zuwa wajen dangi na wajen dangin babanki ne bakya zuwa? Kawai abinda zan ce miki karki jima achaan koh dan sabida school dinki ma" mama nagama fadin haka ta tashi ta fice dan jin tsayuwar motar baba alamun ya dawo daga aiki tagumi tayi da tunani kala kala a cikin ranta har zata kira Zahra kuma sai ta fasa.....
Washegari da Safe,kusan dukkansu sunyi latti babu wanda ya hadu da wani kafin exams suna gamawa kuma kamar kullum aisha kusan itace karshen fitowa a hall din,sam bataga Zahrah da Zainab ba tana nan zaune dansu saudat sun riga sun tafi sai ga Zahrah ta fito sai da ta tsorata ganin fuskan zahrah yanda ya kumbura suntum da sauri ta tashi tsaye ta isa inda take ganinta yasa zahrah ta rungumeta ta fashe da kuka,komawa wajen da tabar jakanta tayi suka zaune ta rarrasheta har sai da kuka ya tsagaita sannan ta tambayeta mai yafaru idanta itama har ya cicciko,Nan zahrah ta kwashe komai ta fada mata yanda kan Zahrahn ya kulle haka na Aisha ma ya kulle sun kasa fahimtar komai a ciki,ita sam ta san basuyi waya da Saeed ba tin jiya da safe amma bata damu ba sanin yana dan daga mata kafa sabida exams,rarrashinta aisha ta cigaba dayi jiki a mice sunyi shuru kowa na tunanin a ranshi Zainab ta karaso da mamaki take kallansu,tace"kukuma lafiya kamar an muku mutuwa? Yau fa kamata yayi muyi farincikin gama part 1" cike da karfin hali Zahrah tayi saurin cewa "bakomai,zanyi missing aminiyata ne bare kuma tace zatayi tafiya" tabe baki zainab tayi dan ba haka taso ji ba sai kuma ta zauna tayi tagumi tayi shuruuu,cikin sanyi aisha tace"Zee ya maganar Yusuf" rintse ido tayi sai ga hawaye yana zuba,da mamaki suke kallanta yanzu tagama cemusu meye suke kuka ita kuma yanzu ta na kuka,"nifa ba kuka nace kiyiba daga tambayarki,shi kenan abar maganar yaje shi da Allah inma da gaske ne kedai kifita harkarshi" Zee tana share hawaye tace"Da bani da niyyar fadamiki amma kuma ina tsoron kiji a gari kiyi wani zargi daban" a hasale Zahra tace"malama meye?" Harararrta Zainab tayi tace"Bai Shafeki ba" sannan tasa hannu a jaka ta ciro kwalin Iphone 12 pro max,ta ajiye a cinyar aisha ta tashi ta rataya jakarta ta juya tana fashewa da wani irin kuka,atake aisha da Zahra suka miqe aisha ta ruqo hannunta tace"Zee kidena yawan kuka,kuka baya maganin matsala ki mana bayani,menene ya faru? Kuma wayar wayene?" A cikin kukan ta rike hannun Aisha tace"ki gafarceni ni ban taba wani dogon hira da Saeed bama,bani da niyyar tarwatsa miki farincikinki,tin lokacin da kika bani numbern Saeed lokacin da kukayi fada,ina zuwa gida na kirashi abinda ya fadamun ne ya tsoratani ya gigitani yasa na kasa fadamiki yadda mukayi dashi daga bayama nace miki ban kirashi,haka yayita damuna har nayi blocking numbernshi" shesheka tafarayi sannan ta cigaba"jiya bayan na koma gida,da daddare aka aiko ana san ganina,koh da ni fita shi-shi-ne" takarasa a cikin shesheka tana sake fashewa da kuka,aisha ta rasa abunda zatayi,zahrah ce ma mai karfin hali ta dauke wayar da tin tashinsu tsaye ta fadi kasa ta saka a cikin jakar Zee sannan taja
hannun aisha da ta zama kamar hoto,a haka aisha ta juya tana kallan zainab tana kokarin kwace hannunta a hannun zahrah amma ba rikon wasa Zahrah ta mata ba bata saketa ba sai da suka hau napep,har gidan suka shiga bakowa a gidan sai mai aiki k2masancewar koh azahar batayi ba 12 ne da yan mintuna,a dakinsu aisha suka nufa Zahrah bata zauna ba tace"Bazan baki shawarar kiyi fushi da Saeed koh kuma Zainab ba,amma abin da zan fada miki shi ne akwai munafurci a ciki kuma babu wanda nake zargi sa Zainab sabida koh hoton da ya nuna mu biyu ne kadai mai yasa babu ita? Ni nasan yayana na kuma san kalan yanmatan da yake kulawa,i can beat my chest and say karya takeyi,MUNAFUKA CE k" bata karasa maganarta ba aisha ta katseta"Karki sake cemata munfuka,dana sani tin farko na yadda da maganar Sofy da duk haka bata faruba,dan ban sake bashi dama ba sabida haka ni nabar mishi zainab har abada" cike da takaici zahrah take kallanta tace"zakiyi nadama,bazan so haka ba idan kuma na tabbatar da ita ta shiga tsakanina da yayana toh tabbas zan dauka mataki tskaninku kuma yanzu lokaci ne daya kamata ace kin tashi kin kwatar ma kanki yanci.." tana gama fadar haka ta juya ta fice a gidan gaba daya ta koma gidansu mum,ita dama tanada taurin zuciya amma kuma idan damuwa ta mata yawa sai ta zubar da hawaye,a dakin kakarta ta rufe kanta taci kukanta iya san ranta babu mai rarrashinta,a bangaren aisha ma haka takasance kuka tayi mai isartq,kukan da duk wanda ya tambayeta batasan dalili ba sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta hau hada kayayyakinta a akwati mai dan girma,a haka har su afrah suka dawo daga school,bata lura da akwatin ba sai ma fuskar yar uwarta da ta gani yadan kumbura da damuwa afrah tace"Nikam tinda mutumin nan ya shigo rayuwarki kike kunci, yanzu ma koh baki fada ba nasan akanshi ne in ba dole bane ki hakura dashi ya aisha tinda shi ba autar maza bane" tasan ba amsa mata zatayi ba dan haka ta wuce dan cire unfoam dinta a nan idanta ya sauka akan akwatin aishan,tayi murmushin takaici tace"Yanzu akan ya bata miki rai shi ne kika gwammaci kiyi tafiyar? Kin gwammaci barin danginki dukda ba wajen bare zaki tafi ba? Waye bai san halin hajiya babba ba? Jiya da daddare dakanki kikace bazaki bita ba dan mama ranta bayaso yanzu kinfi san kiyi abinda ranta baiso ba sabida wani namiji ya bata miki rai? This is unlike u" tana gama fadin haka tabar dakin.....
Gefen Saeed kuwa gaba daya wani irin daci yakeji a ranshi,bashida sukuni sabida yasan zai sha wahalar rayuwa da rashin Aisha,yana mata wani irin so da bai taba ma kuwa ba kuma gefe daya ga rashin Zahra,wacce itace kawarshi itace abokiyar shawaranshi,ya rasa gane kan al'amarin gashi kuma numbern da aka kirashi dashi har aka turo mishi pics dinsu zahrah baya shiga kwata kwata,ya gwada har ya gaji baya shiga..
Da kafa ya gangara gidansu bayan yayi sallahn isha sabida kiran da Dad ya mishi shi duk a tunaninshi ba Zahra ce takau kararshi koh part din Mum bai kalla ba ya karasa gefen Dad da Sallama ya shiga,dauke kai yayi ganin mum a gefen Dad din tana zaune sai da ya zauna akasa sannan ya gaida Dad dinshi sai chaan ya dago batareda ya kalli mum ba yace"Ina wuni" da murmushi tace"lafiya kalau babana,ya aikin?" Alhmdlh kawai yace ya dauke kai,Dad yayi gyran murya yace"Babana da friday din nan nake saka ran zuwa mu tambayi aurenka amma kuma Alhaji Murtala yace Shi Alhaji Muhammad din baya nan dan haka in yadawo insha Allah zamuji" ajiyar zuciya ya sauke jin Allah ma yanaso ya rabashi da ita sannan cikin karfin hali yace"Dad abarshi kawai sai zuwa wani lokacin" cike da mamaki Dad yace"anama neman aure hakane? Menene dalilinka?" Kafin yayi magana mum ta katseshi da fadin"Karkayi mishi dole,kaga tinda yace abari maybe ma yanada dalilinshi koh yayi wani bincike ne yagano wani abun,kaga sai a chanja mishi gidan nema" hada rai yayi ya dago yana kallanta,dad kuma girgiza kanshi yayi yace"Nasan da ace akwai wata matsala da Murtala bazai boyemin ba sabida aure ba karamin abu bane sabida haka ni na gama maganata insha Allahu zuwa satin sama zaa saka maka ranar aure" tashi yayi cikin wani irin yanayi yace"sai da Safe Allah ya kara girma" sannan ya fice a parlourn mum kama bakin ciki takeji kamar tayi yaya tace"Ni agani na tinda ga chan Safiya da tagama jinya akanshi da daita akayi auren tinda ya nuna bayasan wancan din" tashi tsaye yayi yace"indai har sunasan junansu bayan aurenshi da yar gidan Alhaji Muhammad bazan hanashi ba zai iya kara aurenshi in har zeyi adalci a tsakaninsu,auren kam tsakaninshi da Alhaji Muhammad babu fashi" yana kaiwa nan ya kama hanyar dakinshi mum tana kokarin sake mishi magana yace"Nagama maganata" ya shige dakinshi cike da takaici ta wuce bangarenta,daki Dad ya shiga ya riqe kanshi hawaye na zubo mishi yana sambatu shi kadai"Muhammad ya zaayi namanta dakai? Ya zaayi namanta da hallaccin da kamin? Badan kai ba da babu maganar aure na da Zahra'u,kayimin halacci kuma dole na hada jini dakai da yaddar Allah,bansanka ba amma kuma dukda kafini kusanci daita sai da ka dage ka nuna kai bakasanta ayi auren dani,dana sani ma da na bar maka ita kila kuma da tana raye koh?" haka yayita surutai shi kadai yana hawaye...
Meerah"s pen🖋
YOU ARE READING
Nemesis of Ayeesherh(on Hold)
Aktuelle LiteraturFind out the journey of a young kind hearted lady,who always prays and wishes good for everyone,who thinks she meet the Love Of Her Life along the way but was later snatched by the person she trusted the most....... What will happen when she thinks...