8

571 26 0
                                    

💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫

        ✍🏻M SHAKUR

8️⃣

Ajiyan zuciya Baba yasauke sanan yajuyo da kanshi yazubama Khairy idanunshi da kallo daya tamai kawai tafashe da mugun kuka, duk duniya babu wanda take tsoro kaman mahaifinta, Baba is the best father amman not just her kowa tsoron fushi Baba yake agidan nan sai Mama dan idan Baba ya burkice ko ita bata iya taroshi, tsugunnawa tayi awajen tana kuka sosai tace "Baba dan Allah kayakuri wlh wlh bazan karaba please I am so sorr....." baima jira sauran maganan ta ba yawuce ciki shima fuuuu, cikeda tashin hankali takalli yayanta tace "Ya Manaf na shiga uku daga Baba har Mama fushi suke dani" cikin fushi Mu'az yace "da murna kikeso suyi dake sabida bakida hankali do you know how worried they were, saida akasa direba yakoma gidan bikin nan amman baaa ganki ba wai kintafi, Khairy tunda kike arayuwan ki kintaba tuka mota ne dazaki fara yau inda kinje kin kashe kanki ko kinjima kanki ciwo da yaya kikeso muji eh, kawai gakinan ne girma kawai kike amman bakida hankali ko kwara daya stupid girl" yawuce yajuya yay flat dinsu, hararanta Maheer yayi dudda tabashi tausayi yace "babu abinda ta iya sai rashin kunya da tara kawaye, inda police man dinan bai ceceki ba dakin gane shayi ma ruwane, fitsararra kawai" shima yajuya yatafi, ahankali Ya Manaf yasa hannu yadagota yace "stop crying muje kije change this clothes shower kici abinci and sleep" yay maganan yana sakinta yakoma mota ya tattara kayan jakanta yahada mata ya rike sanan yazo yakama hannunta suka shigo falon, Baba kadaine zaune a falon yana rikeda jarida hakan yasa sukai hanyar stairs, cikin kakkausan murya Baba yace "kawomin wayan ki nan" wani irin fashewa da kuka tasakeyi sosai jikinta har rawa yake ta karbi jakanta daga hannun ya Manaf ba musu hannu tasa taciro wayan sanan ahankali tana sheshekan kuka takaraso wajen Baba tabashi wayan, karba yayi ya ijiye gefenshi, sanan yajuyo yakalleta yace "Ummulkhair" muryanta har shakewa tayi tace "Naam Baba" cikin kakkausan murya yace "I ban you from going outside this house for a whole week" zubewa tayi agabanshi tana girgizamai kai tace "Baba please I am sorry dan Allah" cikeda fada yace "nabata ki dayawa, nabaki freedom dayawa kullum your Mum is complaining yau nagani da idanu na, dan haka bazaki saka kafa kifita daga gidan nan ba dagayau har zuwa kwana bakwai, ba school ba islamiyya, sanan ko friend naki guda daya nazo nagani kokuma aka gayamin tazo saina kulleta, i will even tell the gateman koda wasa yabar kawayenki suka shigo cikin gidan nan abakin aikinshi dan haka duk wacce tazo yacemata ma bakinan kowani abun I don't care" sosai take kuka tana girgizamai kai Baba baitaba mata Wanan kalan punishment dinba tsawa yadaka mata. "tashi daga gabana!" da sauri ta tashi tawuce sama da gudu tana kuka Ya Manaf yabita da kallo yay jim sanan ahankali yadawo falon zama yayi kusada Baba ahankali yace "Baba please kayakuri, punishment dinan yay tsauri dayawa, Khairy batada hankali har yanzu Baba, mudena kallonta kaman wata Babba sabida tana final year a school, Baba she is just 20, yanzu shine lokacin her growth, lokacin datake feeling she's capable itama takai matsayin ahankali zamu nuna mata this and that, but Baba hanata fita, hanata zuwa school, karbe wayanta, dakuma Hana kawayenta zuwa wajenta I feel is too much Baba, she will be depress" wani mugun kallo Baba yamai yace "Manaf koyamin tarbiyan yara kake?" Cikeda girmamawa yace "a'a Baba" cikin kakkausan murya Baba yace "to tashi daga nan wajen" ahankali yatashi zaiyi sama Baba yace "barin flat din nace kayi katafi naku" ganin ran Baba abace yake sosai yasa baiyi gardama ba ya sauko yazo yajuya yafita daga falon.

Waya Baba yadauka yakira wata number, ko 10min baa daukaba wani doctor magidanci haka yazo, tashi Baba yayi sukai sama, afalon sama Baba yanunama Dr kujera ya zauna sanan yawuce dakin Khairy saida yafara knocking sanan yashiga tana zaune kan gado ta chanza doguwan rigan jikinta tasa wata na Atampa simple tasa hula akanta idanunta sunyi jajir sundan kumbura, tana ganin Baba dasauri ta kwanta, ba Yabo ba fallasa yace "fito adubaki" yay maganan ya tsaya yana kallonta tashi tayi ahankali sanan tasaka slippers juyawa Baba yayi tabishi abaya suka taho falon gaida Dr tayi sanan tazauna, dubata yayi yamata yan tattanbaya tana bashi amsa sanan yabata wasu magani guda biyu kafin yakalli Baba yace "shikenan Alhaji" kallonta Baba yayi yace "wuce kitchen kije kici abinci kisha magani" gyadamai kai tayi sanan yajuya shida Dr suka fice, saida sukakai waje wajen motanshi sanan Baba yace "are you sure Dr she's okay?" Dan murmushi yayi yace "eh, ai Asmanta yaragu sosai bakaman da ba datake having constant attack, I am telling u abinda ma yatada nayau was mugun tsoratan datayi saisa numfashinta yafara mata wuyan kamawa, wlh she's very lucky tasami wanda yataimaka mata she would've lost...." Dasauri Baba yace "Alhamdulillah she's fine" gyadamai kai Dr yayi yace "yes, bari idan anything change call me, but for now let her relax and rest system dinta yahuta, magungunan dana bata zaisata bacci sosai" gyadamai kai Baba yayi suka gaisa yashiga motanshi yaja yawuce.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now