22

474 22 0
                                    

2️⃣2️⃣

Free page
Fara ce tass kana ganinta kaga bafulatana dan tanada mark na fulani a gefen fuskanta taci gayu na alfarma tana sanye dawani stone gown na exclusive mai pattern, kunenta zinare wuyanta ma haka yatsun hannunwanta guda biyu ne kawai babu zoben zinare ajiki manyan yatsun hannunta sune babu but sauran 4 4 fingers nata duka da zinare tana zaune akan kujera ta hakimce gawani iPad na Apple agabanta tadaura kan wani very very fine stool tana video call dabata iya ganin kowaye a screen din tunda ita daga waje take, hannunta matan rikeda wani white transparent bowl da ita kanta Khairy basuda irinshi agidansu an yanyanka strawberries da kiwi fruits kanana tanaci da fork, kokai waye kaga matan saika shiga taitayinka like duk rawan kanka irin matan nan ne da they don't even needs to show u su waye kana ganinsu kasan they're no nonsense powerful woman saisa haryau itadai Khairy bazata iya cewa ta tsani matan bane but kawai bata sonta, hasalima ita tsoronta ma takeji ko haukanta take agidan dazaran Ammi tazo wajen natsuwa take kaman ba itaba kodako da Baffa take magana, kuma agaban kowa ko agaban Baffa ne Ammi zata iya rufe kowa da fada baruwanta saidai in bakayi ba daidai ba.

Kallo daya tama Khairy ta dauke kai, ahankali Khairy tajawo kofan falon ta maida tarufe sanan takaraso cikin falon ta nemi waje ahankali akasa tazauna kanta akasa tana sauraron maganan datakeji na namiji daga iPad din ashagwabe data rasa na waye dan tasan muryan duka yaran gidan nan banda Babban yayansu da akace yana UK.

Ashagwabe yace "Ammi please niki kyaleni I will get the food nafita jibi fa yanda kitchen dina yadawo" hararanshi Ammi tayi tana kallon screen din tace "My friend dauki egg din break it ingani" cikeda gajiya kaman zai fashe da kuka yace "I don't even know why I called u ki koyamin yanda ake soya egg ma" dan dariya Ammi tayi da saida Khairy dake zaune tadan saci kallonta dan bata taba ganin Ammi ko taji Ammi tai dariya haka ba lallai waye wanan itakuwa.
"Good boy Zayn, tom add a pinch of salt" Zayn! Zayn Zayn! Itako a inama ta tabajin sunan nan Ohhkay kaman shine sunan yayan nasu dake kasan waje ko yayan su Hafiz, tatabaji Baba da Baffa suna maganan.
Maganan Ammi ne yadawo da ita daga tunanin datake tace "bagashi nan ba kagama soya egg din amman da u are being lazy" dariya yayi sosai yace "Ammi nataba gayamiki u are the world best Mommy? No not just best you are the bestest Mom in this world Ammi na" dan murmushi Khairy tayi dan maganan yasa ta tuna da Mama haka take cema Mama world best, kiss taji yasakin ma Ammi ta wayan yace "love you Ammi bye" murmushi sosai Ammi tayi tace "I love you too Son, speak later, make sure u put on jacket kafin kafita dan u are having cold" "who am I to say no to this fine woman, Ammi this egg taste delicious bye" dasauri Ammi tace "kaci ahankali karka kwar....." kafin takarasa maganan ya katse wayan murmushi tayi sosai kafin takalli bowl don fruits din hannunta ganin tacinye yasa ta kwalama mai aikinta kira. "Karima" da gudu mai aikin tafito daga kitchen jikinta har yana bari dan inhar Ammi takiraka sau biyu to kora ne, cikeda girmamawa tace "Hajiya gani" bowl din Ammi tamika mata tsugunnawa tayi sanan ta karba tace "akawo miki wani abune Hajiya"? Girgiza mata kai tayi tamata alamu da hannu ta tafi, wucewa tayi tawuce kitchen falon yarage daga Khairy dake zaune akasa ta takure waje daya saikuma Ammi data dauki wayanta Z-flip tana daddannawa kaman batasan da mutum awajen ba.

Ahankali kaman ba Khairy ba tsabagen yanda ta natsu tace "Ammi ina yini" batare da Ammi takalleta ba kota daina abinda takeyi da wayaba tace "yanzu kikaga daman shigowa gaida ni Ummulkhairy" girgiza mata kai dasauri Khairy tayi gabanta nafaduwa da kyar tace "Ammi kiyakuri bansan kin....." "stand up and get out of this room!" Ammi tadaka mata tsawa dan she finds it insultive ace itace Babba agidan nan ko kare yashigo gidan nan yasan itane Babba an dole ne abata wanan girman balle Wanan Yar karaman yarinyan nan da aka haifa agabanta tashigo gidan nan saita fara zuwa ta gaida kishiyanta sanan zatazo nan, itafa Ammi is like that bata daukan raini kona waye gatada fada, komin girmanka zata iya daga hannu ta kwasama mari.

Tashi tayi jikinta har rawa yake itafa adai rayuwanta yanzu this woman is the only woman datake shakka aduniyan nan, duk iskancin ka baka iya kallon fuskan Ammi kace zaka mata rashin kunya kozaka maida mata da magana wlh bazaka iyaba Allah yariga yabata Wanan haiba da kwarjinin nanne, gabanta nafaduwa sosai idanunta sunyi ja tace "Ammi I am so......" "out!" Ammi tai maganan tana nuna mata kofa dasauri tai kofa zata bude aka turo kofan hakan yasa kofan yabuge mata hannu, baya tayi tana yarfe hannun dasauri idanunta sunyi ja Hafiz ne yana sanye da jeans da riga ganin Khairy yasa yace "Khairy kene agidan" hannunta yabi da kallo yace "ohh no sorry nabuge miki hannu ne" murmushi takakalo tana maida hannun baya tace "Ya Hafiz welcome ina yini" sanan tabi tagefenshi tafice dasauri yabita da kallo kafin ya kalli Ammi dake danna wayanta abinta, maida kofan yayi yarufe yazo kusa da Ammi ya zaune yace "Ammi yaushe Khairy tazo" batare data kalleshi ba tace "maiya hanaka tambayanta kake tambayana" shiru yayi baice komi ba, saida tagama abinda zatayi sanan ta ijiye wayan takalleshi tace "how's my granddaughter"? Murmushi yayi yace "she's fine" "tafara shan nonon"? Gyadamata kai yayi yace "tafara Ammi, bata barin mu bacci, koda yaushe shan Nono take bata barin Moon tahuta"  dan dariya Ammi tayi taharareshi tace "idan naga granddaughter na tarame dagakai har matarka will have to answer me I am very very serious Hafiz, anyway anjima idan yan suna sun watse akwai kayan dazaka tafi musu dashi" Gyadamata kai yayi yace "Ammi kinsan irin uban kudi da Ya Zayn yaturomin wai nabama Moon da Little niko sule biyar bai baniba bayan ni namafi mai jegon wahala" dariya Ammi tadanyi saikuma tai shiru kaman mai tunani ahankali tace "I can't wait to see yaran Zayn shima" dasauri Hafiz yace "Ammi ai nagayamiki Zayn nadawowa kurikeshi kumai aure dan wlh  Ammi Ya Zayn bai shirya yayi aure ba" shiru Ammi tayi batace komi ba, kallon fuskanta Hafiz yayi ganin tai nisa a tunani yace "Ammi kema u believe what I am saying ko" "stop talking about ur brother Hafiz" shiru yayi saikuma chan yatashi yace "ina zuwa Ammi" baijira amsanta ba yawuce yatafi, awaje yaga Khairy gaban tap na wajen flower tana wanke fuskan ta da ruwa, bamata lurada shi ba yana zuwa ya tsaya agefenta yace "after all this years haryau baki gane halin Ammi ba kullum kikazo sai kinyi kuka common my friend, je daki ki dauko gyalenki keda Batool na kaiku gidan suna kowa nachan banda ku" murmushi tayi tajuya da dan gudunta tashiga dakin Mum, basu wani jimaba itada Batool suka fito datai wanka taci gayu motanshi suka shiga sai gidaUnshi.

ALKAWARIN ZUCIYA (PROMISE OF THE HEART)Where stories live. Discover now